Hukumar HISBAH ta dakume wani matashi sakamakon hada hoton tsohuwar budurwarsa da yayi dana tsiraici ya kuma wallafa a shafin Facebook da sunan Itace
A yayinda hukumar Hisbar ke cewa ta baza idanuwanta a kowane ANGEL don cafke ‘yan daudu ta inda basa tsammani tuni wasu matasa sukayi amfani da shafin Facebook tun daga garin Kaduna, suka kulla alaka zuwa Kano domin aikata dabi’ar mutanen Annabi Ludu akan kudi N6,000 kacal.
Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma wato CITAD ta bada horo ga wasu matasa kan yaki da kalaman batanci a Internet.
Muna tafe da jerin rahotonninmu na wannan makon, dama cigaban tattaunawarmu da matashin nan da ya kirkiri babbar kasuwarnan ta Internet wato GetkKano.