Acikin shirin na yau zakuji cewa Wani masanin Computer a nan Kano ya bayyana yawaitar manyan wayoyin hannu a wurin jama’a matsayin daya daga cikin dalilan da suka ta’azzara satar asusun Facebook.
Sake dawowar manhajar hangen tsufa ta FaceApp a wannan lokacin ta haifar da cece kuce a tsakanin al’umma a shafukan sadarwa, sai dai tuni masana suka baje kolin bayanai masu cin karo da juna kan halarci ko rashinsa wajen amfani da manhajar a Kimiyyance.
Hukumar shirya jarrabawar kamala makarantar sakandire ta WAEC ta saki sakamakon jarrabawar ta wannan shekara,
Muna tafe da tattaunawa da wani matashi mai sana’ar Blogging a nan Kano.