Wasu rahotanni sun ce akalla mutune 60 ne suka rasu a wani harin da ake zargin `yan kungiyar Boko Haram da kaiwa a garin Kukuwa a jihar Yobe da ke arewa-maso-gabashin Najeriya.

Wasu da suka fito daga garin sun shaidawa BBC cewa mutanen sun gamu da ajalin su ne sakamakon harbinsu da bindiga, yayin da wasu kuma ruwa ya ci su lokacin da suka fada Rafi a kokarin su na tserewa.

Ku saurari rahoton wikilinmu, Abdullahi Kaura Abubakar domin jin karin bayani.