Hukumar Lafiya ta duniya, WHO, ta ce za ta kafa wani Asusun ko-ta-kwana na dala miliyan dari don yaki da cutar Ebola. Babbar Daraktar Hukumar Margaret Chan, ta bayyana cewa annobar Ebola ta ci karfin Hukumar lokacin da ta barke a shiyyar Afirka ta yamma, kasancewar abin da aka bukata wajen yaki da ita ya ninka sauran bukatu da hukumar ta saba dawainiyarsu sau goma. Dr Nasiru Sani Gwarzo Mamba ne a kwamitin ayyukan gaggawa na yaki da cutar Ebola a Najeriya, ga hirarsu da Ibrahim Isa a kan wannan yunkuri na WHO.