A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon, Karamar Hukumar Kasuwa Babba ta hana hawar babur a cikin garin, ko me wannan zata haifar?

Daga bisani kuma, zauren Mu tattauna zai zanta ne kan batun almajiranci, idan shirin ya ziyarci wata tsangaya a jihar Kebbi. Ko shin yaya karatun ke sauyawa, kuma ta yaya za’a iya inganta shi. A kasance tare da mu.