A cikin shirin namu na yau, mutanen gari sun fara zargin Talatu da koya wa matan aure abubuwan da suka saba wa al’ada. Limou ta sake zuwa neman bashi… Hajiya Sabuwa zata je biybiyan ayyukan da karamar hukuma ke yi a yankuna. Don jin yadda aka kaya, a biyo mu a cikin shirin wasan kwaikwayon mu na Gatanan Gatanan ku, da kuma shirin Mu Tattauna.