A wanan makon a Madubi, Maigari da masu rigakafin poliyo sun je ruga amma da kyar Maigari ya samu shawo kan wasu! Bilkisu da Hadiza matan Maigari sun je asibiti rigakafi amma Bilkisu na nema ta ja matsala. Ja’e ya amsa kiran Maigari inda yayi masa gargadi akan abin da ya faru a ruga. Maigari yaje zagayen masu turjiyan rigakafi amma da alama an sami mishkila. Kadan kenan daga cikin labaran da za ku ji a shirin Madubi.