A wanan makon a Madubi, Maigari yaje dubiyar matar Lima da sauran jama’ansa kuma har yanzu ana fama da turjiya akan maganar rigakafi. Liman yaci karo da Faiza da Abare a zaure, ko ya zasu kare? Abare ya fada ma ubansa ya shirya aure, amma kuma kamar akwai matsala. Kadan kenan daga cikin labaran da za ku ji a shirin Madubi.