A wanan makon a Madubi, Zinaru fa ta hura ma Sale wuta akan sabon aure da yake son yi. Malam Tsalha ya zo karban bashin kudin sa wajen Hudu, ko zai same shi gida kuwa. Karatun Kyauta ya sami cikas saboda rashin lafiyar mahaifinta. Kawun Kyauta ya ce sai dai ai mata aure, ko ya za ta yi. Kadan kenan daga cikin labaran da za ku ji a shirin Madubi.