A wannan makon a Madubi, Hudu ya ga uwar bari, Uwani ta nace zata koma tsohuwar gidan ta wurin sauran matan, ko me ye dalilin ta? sun yi fada da Hudu ne ko Ladidi? Iliya da abokansa sun sha bulala a padar Maigari ko me ya janyo hakan kuma me su ka yi? Labaran mu kenan a wannan mako a Madubi.