A wannan makon a Madubi, an jefo Garus daga tankar ruwa, ko me yasa haka? Baba Delu ta zo yi ma Hudu karin bayani akan amfanin rigakafin poliyo, Hudu ya kuma gaya mata matsalar sa da Ladidi. Garus ya yanke shawarar sa kayan sautin shi akan babur din sa. Hon. Uba ya sami Hudu don ya san matsayin sa akan maganar sakin Ladidi. Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.