A wannan makon a Madubi, Kyauta ta dawo gida amma ko me yasa ta gudu, Barde ya zo tadi wajen ta. Uwar Kyauta bata amince da saurayin da ta ke so, ko zata shawo kan uwar? Iliya ya zo neman kudi wajen uwarsa, shin zai samu kuwa? Saudatu ta shiga hali domin mijin ta yayi sabuwar amarya, rigima dai ta cigaba a gidan su, ko Baita zai shawo kan matan shi? Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.