A wannan makon a Madubi, malaman poliyo na zagaye don diga ma yara rigakafin poliyo. Malam Tukur ya rantse baza a diga ma yaransa rigakafin poliyo ba, shi kuma makwabcin sa Muttaka yace hakan zai shafi yaransa. Ko Liman zai daidai ta tsakanin su? Har yanzu dai ana fama da rashin ruwa kuma an cigaba da samun matsala wajen mutan gari game da rigakafin poliyo. Hudu dai ya dawo gida amma ya rasa wajen kwana, ko me yasa? Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.