A wannan makon a Madubi, kamfanin aikin gada ya kira jama’a don daukan su aikin lebura, Garus da Baita suna cikin wadanda suka je, ko ya aka kare da su? Liman ya kai Iliya kara wajen Maigari, ko zai sha bulala? An ba su Rabe izinin kafa teburin shayi wajen aikin gada, ko sun gaya ma Maishayi? Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.