A wannan makon a Madubi, Ladidi ta fara daga jijiyoyin wuya a kan Hudu na kokarin saba wa alkawarin da su ka yi kafin auren su, ko wane irin hali Hudu zai shiga. Hon Uba da Khalifa sun je ganin Ladidi amma kaman Hudu bai gamsu da zuwan shi ba. Garus da Barde sun je wajen Kyauta ko wa zata saurara tsakanin su? Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.