A wannan makon a Madubi, kungiyar su Zinaru na shirye-shiryen hada taron lafiya amma an samu matsala wajen sha’anin kudi. An samu an sasanta tsakanin Maishayi da Rabe, ko ya suka kare? Ana ta tsegumin cewa Liman ya karbi kudi don yada amfanin rigakafi, ko hakan gaskiya ne? Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.