A wannan makon a Madubi, mutanen Hauren Rafi sun je wajen Chairman don neman a tsaida korar su daga wajen sana’ar su, ko sun yi dace? Hudu ya kai Ladidi duba gida, amma kudin gida sun canza, ko za ta sayi gidan? Hudu na shirin bude gidan gona. Amarya ta tare a gidan Baita amma har yanzu dai ya kasa shawo kansu. Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.