A wannan makon a Madubi, anyi meeting na shirin rigakafi a Kuka-Jere, an kawo rahoton barkewar cholera a Gangaren Jemagu. Maigari ya yi alkawarin zagaya wa da ma’aikatan polio. Maman Kyauta ta nemi izni Kyauta ta koma talla a Gangaren Jemagu ko baban ya yarda? Garus ya tasa kudi gaba yana ta hidima, amma ko hakan zai taimaka mashi kuwa? Maishayi ya kawo shawarar zuwa wajen Chairman don neman a shawo kan matsalar wajen sana’ar su. Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.