A wannan makon a Madubi, Maigari ya yi wa mutan gari akan maganar diya na filayansu, Maishayi da sauran abokan sana’ar sa basu dai gamsu ba. Rabe ya samu anyi belin shi, amma ko ya zasu kare da wansa Maishayi? Mijin Zinaru ya fara damuwa da zirga zirganta akan maganar kungiya, zasu daidaita kuwa? Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.