A wannan makon a shirin Madubi, an daura auren Baita da Ziza. ‘Yan uwan Barde za su je neman aure gidan su Kyuata, ko ya zasu kare? Garus yaga uwar bari, ya na so ya nuna ma Kyauta ya na son ta, amma za ko ta saurare shi? Hudu ya ba Maishayi shawara ya rubuta jarabawar WAEC, ta ina zai fara? Kadan daga cikin labaran mu kenan a wannan makon na Madubi.