A wannan makon a shirin Madubi, Baba Delu ta bunkasa sana’ar ta da masa, amma shin za ta more wannan bunkasa kuwa? Iliya da su Rabe sun soki wani da wuka wajen aikin su, ko ya mutu? Uwani ta tunkari Hudu da maganar kudin asibiti, har yanzu dai bai ga amfanin zuwa asibiti. Har yanzu Baita na nan kan bakar sa na yin sabuwar amarya. Kadan daga cikin labaran mu na wannan makon a Madubi.