A wannan makon a Madubi, Maishayi ya fara zagaya jama’an gari don samun shiga wajen siyasa. Kyauta taje neman taimako wajen Zinaru, ko za ta samu? Hon. Uba ya dawo wajen Ladidi, amma haduwar an kare da hushi saboda Khalifa ya bace. Barde ya zo neman Garus domin su shirya yadda za su je wajen Kyuata. Baita ya gaya ma Saudatu zai sake aure, ko ya suka kare? Labaran mu kenan na a wannan mako na Madubi