Fitilar mu ta shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon zata haska Chairman Ghali ne … sai a biyo mu don a sha labari.
A cikin wannan zango na shirin Gatanan Gatanan Ku , Godiya tayi Magana ne kan rayuwan ta, aiki, iyali da kuma soyayya. Don jin abun da ta fada, sai a saurari shirin…
A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan karon, Mun yi hira ne da Iya Remi, inda ta bamu labarin soyayyan ta da Ahmadu. Sai a saurari shirin…
Wannan makon muna so ne masu sauraro su sakata su wala… Barka da Sallah daga shirin Gatanan Gatanan Ku
Saurari wannan shafi na shirin Gatanan Gtanan Ku don jin abinda Fadalla ya gabato mana a cikin shirin.
A cikin shirin wannan shiri na Gatanan Gatanan Ku, Godiya ta rubutowa Alidu wasika inda tayi magana kan abubuwa da dama. Don jin abun da ta rubuta, sai a saurari shirin…
A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon, zamu ji irin buge-bugen da Buba yake yi don tanadawa iyalinsa.
A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon zamu tattauna ne da babban bakuwar mu Malama Farida kan cin hanci da rashawa…
Bello ya je karban kudin aiki, toh… Mammaji kuma, lokacin hauhuwa ya kai... duk cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon.
A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon, har yanzu dai batun Talatu da Fadallah ake, Ghali bai amince da alakar da ke tsakanin su ba. Bilkisa ta ba wa Buba mamaki, ko abin alheri ne? sai a biyo mu…
A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon, Bello ya fara barazana da aikin sa… toh Sai kuma mu garzaya teburin Mai Shayi inda Kere da abokinsa suka hada wata muguwar dabara…
A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon, Talatu da Fadallah suna Magana kan zuwa ganin Ghali sai…. Gidan Danfulani kuma, Bingyel ta shirn haihuwa a asibitti ama Goggo tana da nata ra’ayin.
A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon, Bello bai ji dadin wannan sallah ba, amma Dangwari ya bashi wata labara mai dadi … Bilkisa kuma sai muce mata “fadiwa ya zo daidai da zama” … sai a saurari shirin don jin yadda ta kaya
Remi ta kai wa Talatu ziyara don tattaunawa kan wasu matsaloli da ke damun ta, ko zasu sami mafita? Sai kuma labarin Bilkisa inda ta gayawa Buba bukatarta… duk a cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon.
Shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon kuma Danfulani yana kokarin taimakawa matarsa dai aiyukan gida, sai dai…. Layya kuma tana fushi da Ghali, ko meye dalili? Sai a saurari shirin don jin yadda ta kaya.
A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon zamu leka gidan Ghali inda yake shirin tafiya, Layya kuma ta kusan haihuwa. Bello kuma da Farida ma ba a manta da sub a. Sai kuma gidan Buba inda Bilkisa take karban wata shawara daga wurin kawarta Asabe, ko wane irin shawara ne? Sai a biyo shirin.
A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon Iya Remi ta rubutowa Ahmadu wasika, sai a biyo shirin don jin yadda ta kaya...
A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon Ghali ya hada taron Town Hall da kansilolinsa da jama’an Kasuwa Babba. Sai kuma labarin Terwase da budurwarsa ta yanar gizo waton facebook.. za kuma mu ji labarin Ghali da Talatu.
A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon zamu ji yadda Gwamna ya kawo ziyara cikin garin Kasuwa Babba, Bilkisa ta je neman taimako sai kuma labarin producer da shirin yin film.
Bilkisa ta rubutowa Buba wasika inda tayi masa bayani kan abubuwan da ya zarge ta da shi. Ta kuma gaya masa irin halin da ta tsince kan ta a ciki.sai a saurari shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon.
Alidu ya samu hanyar tallafawa yayan sa, Iya Remi taje ta karbi kudinta da ke hanun Halidu shi kuma producer ko yaya yake tafe da aikinsa? a cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon.
Cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon:
Ghali da kansilolin Kasuwa Babba suna yarjejeniya kan cigaba
Bello da Farida sun dan samu wata yar matsala
Talatu da Ghali suna kokarin sasantawa
A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon zamu ji yadda Gwamna ya kawo ziyara cikin garin Kasuwa Babba, Bilkisa ta je neman taimako sai kuma labarin producer da shirin yin film.
A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon zamu ji yadda al’amura ke tafe da Alidu da yaransa, sai kuma labarin Bello da amaryarsa Farida.
A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon Talatu ta rubuto wa maigidan ta Chairman Ghali wasika sai a biyo shirin don jin abunda wasikar ta kunshi.
Shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon zai ka’tar da mai sauraro saboda za a ji yadda Tabizaro yake kokarin kara girman jarinsa, sai kuma halin da Showboy ya tsinci kansa, a karshe kuma zamu ji labarin producer.
Ghali ya dauki matakai don inganta rayuwan jama’an Kasuwa Babba; Iya Remi ta samu gayyata zuwa wata buki; Balkisa da yaranta sun shiga wata hali; Shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon
Shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon zai kai’tar da mai sauraro saboda za a ji yadda Tabizaro yake kokarin kara girman jarinsa, sai kuma halin da showboy ya sami kansa a karshe kuma zamu ji labarin producer.
Wannan makon Tabizaro ya tattauna da Siyama kan wasu abubuwa masu mahimmanci, Alidu kuma ya je ganin malama Talatu ko don abin alheri ne oho, duk a cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon.
A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon zamu sha labari ne kan wani mahauci mai suna Bello.. sai kuma labarin wata mata mai suna Bilkisa..
Filin Mu Tattauna na wannan mako zai ka’itar da ku. A kasance tare da mu don jin yadda shirin zai kaya.
A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon Bilkisa ta kawo yarinyan ta asibitti, wacece kuma zata gani?.. sai a biyo mu
Wani gudu ba hanzari ba, filin Mu Tattauna zai ja ku wani bangare ne da zaku so ayi da ku... A kasance tare da mu.
A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon, Talatu ta ba wa Alidu shawara ko na menene.. sai a biyo mu
Kamar yadda aka saba, filin Mu Tattauna na wannan mako zai ka’itar da ku. A kasance tare da mu.
Chairman Ghali ya sami kan shi a cikin wani hali, sai koma gidan Buba inda ya siyo wa Bilkisa da Limou tsaraba ko yaya aka raba… a biyo mu a cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon. Filin Mu tattauna na wannan makon zai raja’a ne kan irin haddirran da ke tattare da hako ma’adanan kasa a arewacin Najeriya. Mai sauraro, a biyo mu a cikin shirin.
A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon, zamu leka cikin gidan Buba in da Limou ta yi masa kyauta to ko me ta bashi? Sai a biyo mu …
Filin Mu tattauna na wannan makon ya karkata akalarsa ne kan irin matsalolin da ma’aikata ke fuskanta a arewacin Najeriya da tasirin da hakan ke yi a rayuwarsu. A Mai sauraro, a biyo mu dan jin yadda tattaunawar ta kansance.
A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan makon, Karamar Hukumar Kasuwa Babba ta hana hawar babur a cikin garin, ko me wannan zata haifar?
Daga bisani kuma, zauren Mu tattauna zai zanta ne kan batun almajiranci, idan shirin ya ziyarci wata tsangaya a jihar Kebbi. Ko shin yaya karatun ke sauyawa, kuma ta yaya za’a iya inganta shi. A kasance tare da mu.
A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan mako, Ghali ya kai wa Hajiya Sabuwa ziyara.. Sai a biyo mu don jin yadda ta kaya.
Satar shanu ya taazara a arewacin Najeriya. Shin wa ne tasiri hakan ke yi ga tattalin arziki da kuma alummar wannan yanki? A kasance da mu a filin Mu Tattauna na wannan mako.
A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan mako, Dalla Dalla ya je hira a gidan su Bara’atu.. sai a biyo mu don jin abinda ya faru.
Tun tale tale, manoma da makiyaya tamkar yan uwan juna suke. Amma rashin jituwa ya shiga tsakaninsu a yan shekarun baya. Ko shin me ya haddasa wannan takaddama? Kuma ina mafita? Batun da zauren Mu Tattauna na wannan mako zai zanta akai kenan.
A cikin shirin namu na wannan makon, Buba ya tattauna da Hakimi don fara wata sana’a...
Mai sauraro a kuma biyo mu don sauraron wani kayattaccan shirin Mu Tattauna na wannan mako.
A cikin shirin mu na wannan makon, Remi ta shigo Kasuwa Babba… sai mu biyo mu ji abin da ya kawo ta. Bayan haka za a saurari shirin Mu Tattauna.
A cikin shirin mu na wannan makon,Tabizaro ya hada wani gangami… A biyo mu a sha labari.
Daga bisani kuma zauren Mu tuttauna zai yi bibiyar alkauran da gwamnatocin jihohin arewa maso gabas suka yi wa alummominsu a yayin yakin neman zabe. Shin a ina a ka kwana?
A cikin shirin namu na yau, zamu yi waiwaye ne kan wasu labaru a cikin kayattaccen wasan kwakwayyon namu. Daga bisani kuma, za ku saurari matakan da hukumomin ke dauka wajen yaki da sha da fatauchin miyagun kwayoyi a cikin filin Mu Tuattauna
Mai sauraro a biyo mu a cikin shirin ...
A cikin shirin namu na yau, Bilkisa bata gane wa Falmata ba… me Falmata ta yi?
Dukushi ya hadu da Alidu a shagon Godiya…
Mai sauraro a kuma biyo mu cikin zauren Mu Tattauna don jin sabuwar shirin da zamu kawo...
A cikin shirin namu na yau, Alidu yana shagon Godiya inda yake gyaran suman Nana… wani yayi sallama, wanene?
Mai sauraro a biyo mu a cikin shirin don jin yadda zata kaya...
Shin dan canje-canjen da rigakafi kan haifar zai iya sa ka ki kai yaronka asibiti domin karasa shan maganin?
Ga labarin wani magidanci da ya yi namijin kokari yayin da iyalinsa ta tsinci kanta a cikin wani mawuyacin hali! Shin za ka iya/ ka taba yin hakan? Ba mu naka labarin.
A cikin shirin namu na yau, Saminu ya kai wa Hajiya Sabuwa ziyara. Shin ko mai ya kais hi? Kuma shin ko wacce harkace ta hada Bilkisa da S.A Salah wannan karan? A biyo mu a cikin shirin don jin cikakken labarin...
A cikin shirin namu na yau, Saminu ya kai wa Hajiya Sabuwa ziyara kan taron jam’iya. Buba ya nada wani a matsayin mataimakin sa.. shin ko wanene? Daga bisani kuma a zauren Mu tattauna, za’a saurari tattaunawa kan yawaitar saki a arewacin najeriya… Mai sauraro a biyo mu a cikin shirin...
A cikin wannan shirin, Limou ta rubuto wa Buba wasika daga Niamey.. Ko me ta rubuto masa?
Shin wacce rawa lauyoyi da yan jarida masu gudanar da bincike ke takawa wajen yaki da almundahana a najeriya? Batun da filin Mu tattauna zai zanta a kai kenan.
Mai sauraro, a biyomu a cikin shirin na wannan makon.…
A cikin shirin mu na wannan mako, Talatu ta gabatar da babban bako wato Alidu a second chance. A sashen masu gyaran takalmi kuma, me ke faruwa da buba?
A cikin shirin Gatanan Gatanan Ku na wannan mako, Talatu da ma'aikatan Skill Acquisition Center na shirin karbar wani babban bako, kuma Saminu ya dawo garin kasuwa babba...
A wannan makon, zaku waiwayi labaran yan wasan namu, kamar yadda suka faru a makonnin da suka gabata.….Wai aka ce WAIWAYE ADON TAFIYA…
A wannan makon, zaku waiwayi labaran yan wasan namu, kamar yadda suka faru a makonnin da suka gabata.….Wai aka ce WAIWAYE ADON TAFIYA…
A wannan makon, zaku waiwayi labaran yan wasan namu, kamar yadda suka faru a makonnin da suka gabata.….Wai aka ce WAIWAYE ADON TAFIYA…
A cikin shirin namu na yau, Allah yayi, Ahmadu ya amshi shagon shi. Yau ake yinta, an rutsa Godiya a shagon ta. Buba ya zama shugaban masu shoe shiner…
Don jin yadda aka kaya, a biyo mu a cikin shirin wasan kwaikwayon mu na Gatanan Gatanan ku, da kuma shirin Mu Tattauna.
A cikin shirin namu na yau, mutanen gari sun fara zargin Talatu da koya wa matan aure abubuwan da suka saba wa al’ada. Limou ta sake zuwa neman bashi… Hajiya Sabuwa zata je biybiyan ayyukan da karamar hukuma ke yi a yankuna. Don jin yadda aka kaya, a biyo mu a cikin shirin wasan kwaikwayon mu na Gatanan Gatanan ku, da kuma shirin Mu Tattauna.
A cikin shirin namu na yau, Ahmadu ya rantse sai inda karfinsa yare kan shagon sa.. Jama’a sun fara rigista ta yanar gizo, amma da wata manufa suke yi.
Balkisa zata je taron kara ma juna sani a birni…kada dai ayi katobara dai… Don jin yadda aka kaya, a biyo mu a cikin shirin wasan kwaikwayon mu na Gatanan Gatanan ku, da kuma shirin Mu Tattauna.
A cikin shirin namu na yau, Ghali ya bude sashe a yanar gizon karamar hukuma don jama’a su shigar da bayanai kan abinda zasu iya yi. Maitama ya sa Balarabe ya bude masa shafin Facebook.
Limou ta koma gun Boka…Ko wani salon za’a sake… Don jin yadda aka kaya, a biyo mu a cikin shirin wasan kwaikwayon mu na Gatanan Gatanan ku, da kuma shirin Mu Tattauna.
A cikin shirin namu na yau, Ahmadu ya shawarci Maitama da ya daidaita tsakaninsa da jama’a, musammam ma mata... Balkisa da Limou sun kaure da dambe cikin gida.....wa zai raba?
Don jin yadda aka kaya, a biyo mu a cikin shirin wasan kwaikwayon mu na Gatanan Gatanan ku, da kuma shirin Mu Tattauna.
A cikin shirin namu na yau, Malam Bello ya fara amfani da wajen saida namansa yana bata gwamnatin chiyaman Ghali...... Ghali yana cikin tsaka mai wuya. Jama’an gari sun hura wuta a saya masu motan kasha gobara.... Buba yana aikin shoe shiner.....za’a kare lafiya kuwa? Don jin yadda aka kaya, a biyo mu a cikin shirin wasan kwaikwayon mu na Gatanan Gatanan ku, da kuma shirin Mu Tattauna.
A cikin shirin namu na yau, An rutsa Iya Remi kan kudin da jama’a suka biya na tallafi...
Mallam Bello ya kai wa Maitama ziyara, ko me za’a kulla? Ghali ya barwa Layya daki, ya dawo palour....yau ake yenta....... Don jin yadda aka kaya, a biyo mu a cikin shirin wasan kwaikwayon mu na Gatanan Gatanan ku, da kuma shirin Mu Tattauna.
A cikin shirin namu na yau, Buba ya gwada wa wani halin mahaukata a gidan burodi... Limou tayi kutun kutun kan sai ta tattara hankalin Buba.
Dalla Dalla ya kira taron wasu yan gari don tattauna batu da ta shafe garinsu... Don jin yadda aka kaya, a biyo mu a cikin shirin wasan kwaikwayon mu na Gatanan Gatanan ku, da kuma shirin Mu Tattauna.
A cikin shirin namu na yau, Chiyaman Ghali ya bawa Hajiya Sabuwa jagorancin committee a gwamnatin sa... Balkisa tayi fata fata da Ghali a shirin Garba Garba...
Ana zargin Dalla Dalla da yin munafurci a wajen Chiyaman Ghali. Don jin yadda aka kaya, a biyo mu a cikin shirin wasan kwaikwayon mu na Gatanan Gatanan ku, da kuma shirin Mu Tattauna.
Idan ba ka saurari shirin Gatanan gatanan ku makon da ya wuce ba, toh ga dama ta samu. #daukarmataki #hadinkai