Health magazine programme that focuses on improving family health through proper care-giving habits. It is produced in Hausa language
Shin wadanne irin abincin gargajiya ne masu amfani za mu iya nemo wa mai shayarwa domin ta samar wa yaro isasshen ruwan mama?
Tanko ya ce idan ba a yanke cibiyar mutum ba a lokacin da aka haife shi zai iya samun matsalar kwakwalwa idan ya girma, a cikin wannan wasan kwaikwayo…Me ku ka sani game da al’adar yanke cibiya idan an haihu?
Yaushe ne ya kamata miji ya fara shiri idan mace za ta haihu. Abinda wannan wasan kwaikwayo ya kunsa ke nan. A ra’ayinku yaushe ya kamata a fara shirin zuwan baby?
A cikin wannan wasan kwaikwayo ana gardama kan cewa tunda iyayenmu sun haihu a asibiti, matan yanzu ma ba sai sun je asibiti ba. Ku mene ne naku ra’ayin?
A wannan gajeren wasan kwaikwayo ana gardama kan abinda yake kashe yaran kanin malam Tanko. Rashin kula da lafiya ne ko mayu ne? Mene ne naku ra’ayin?
Do you need advice on maternal and child health? Well this cool & very knowledgeable Grandma gives good tips.
She’s not your usual Grandma Do you like Hip Hop? Because she sure does & she can rap!!! She has lots of helpful advice for new parents & family Coming soon to you radio……..
Ko kasan? Ruwan nonon farko na kunshe da sinsdaran da za su iya kare yaro daga cututtuka da dama.
Wannan shiri labari ne na wata suruka ce wadda mijinta ya rasu, inda ta yi mana bayani kan yadda zamantakewa ta kasance tsakanin ta da uwar mijinta a lokacin da mijinta ke da rai.
Wannan shiri ya duba irin bukatar da ke akwai na gani ana bayar da muhimmanci kan irin abinci da mata masu juna biyu ke ci, a lokacin yin cefane
A cikin zauren magidanta na yau: maza sun bayyana matakin da suka dauka lokacin da aka tsangwami iyalansu a asibiti? Idan kai ne wane mataki za ka dauka?
Yatake Ne Arewa. Ko wace irin gudummowa kake ganin zaka iya bawa matarka mai juna-biyu?
Shin dan canje-canjen da rigakafi kan haifar zai iya sa ka ki kai yaronka asibiti domin karasa shan maganin?
Ga labarin wani magidanci da ya yi namijin kokari yayin da iyalinsa ta tsinci kanta a cikin wani mawuyacin hali! Shin za ka iya/ ka taba yin hakan? Ba mu naka labarin.
A cikin shirin Ya Take Ne Arewa na yau: Mun taka rawar ‘Duba-gari’, inda muka dauki malamar lafiya muka zagaya gidaje domin gane ma idanunmu me ke faruwa …
A cikin shirin Ya Take Ne Arewa na yau: Za a wasa kwakwalwa. Kai ma mai sauraro ka shirya domin amsa tambayoyin da za a yi.
A cikin shirin Ya Take Ne Arewa na yau: Ziyara ce ta musamman muka kai ma Mami. A wannan karo wace shawara za ta ba mu? Ku biyo mu.
Shin ko shan Rubutu kadai ya gamsar ga mace mai juna biyu ko akwai abin da yakamata ayi
A cikin shirin Ya Take Ne Arewa na yau: Wane mataki za ka dauka idan aka ba ka dalili mai kwari wanda zai sanya ka canza ra’ayi a kan wani abu ba ka so? Ku biyo mu.
Shin ka aiko da sako cikin shirin kasa kunne domin wannan makon shirin ya waiwayi sakonnin masu sauraro ne.
A cikin shirin Ya Take Ne Arewa na yau: Mene ne kudurin ‘Dan’auta’ a shekara ta 2016? Kai ma mene ne naka kudurin? Dan’auta ya yi mana nuni a cikin nishadi…
Awannan makon shirin yayi dubane kan tambayoyin masu sauraro kan abunda ya shafi Gudawa, Tazarar haihuwa da kuma zazzabin cizon sauro inda Likita ya amsa musu
Mene ne tsoron da ku ke ji game da tazarar haihuwa? Kila ya yi daidai da wanda aka fada mana a cikin shirin YA TAKE NE AREWA na yau, ku biyo mu.
A cikin shirin Ya Take Ne Arewa na yau: Za mu bi gida-gida, lungu da sako domin jin yadda masu sauraro za su gabatar da shirin Ya take ne Arewa da kansu.
wannan shirin na waiwaye ne inda muka tattauna akan muhimmancin tazarar haihuwa, shayar da yaro zallar ruwan mama da kuma maganar gudawa