Hausa radio drama reflecting the lives Northern Nigerians and their attitudes towards Polio and Routine Immunisation
Wannan makon a cikin shirin Madubi, Hudu na garin Kingari a matsayin researcher. Ko yaya rayuwa ta kasanche a garin Kingari bayan tashin hankalin da aka samu a garin? Ku kasance da mu ku ji yadda ta kaya.
A cikin shirin Madubi na wannan makon, ana tashin hankali a gidan Malam Hudu. Shi kuma Baita, da aka cinye gidan shi garin chacha, ko yaya zai yi da iyalin sa? Ku kasance da mu ku ji yadda ta kaya.
A wanan makon a Madubi, Ladidi dai ta cika ladar ta, ta kai ‘yar ta Arfah asibiti yin rigakafi ta wata tara. Sai kuma Baita ya dauke takardun gidan sa daga hannun uwar gidan sa Saudatu. Tsuntsu da Abare sun shirya su je su saci rago daga gidan Mal. Sabo don basu yi yankan Sallah ba… Kadan kenan daga cikin labaran da za ku ji a shirin Madubi.
A cikin shirin Madubi na wannan makon, Masu rigakafin poliyo sun je ruga kuma kowa ya bada hadin kai, Laraba bata san batun rigakafin da ake yi a asibiti ba…. Hudu kuma ya samo labarin cewa a can yankin da ake fama da tashe tashen hankula, ana kasuwanci sosai, meye matakin da zai dauka? Ku kasance da mu cikin shirin Madubi ku ji yadda ta kaya.
A wanan makon a Madubi, Maigari da masu rigakafin poliyo sun je ruga amma da kyar Maigari ya samu shawo kan wasu! Bilkisu da Hadiza matan Maigari sun je asibiti rigakafi amma Bilkisu na nema ta ja matsala. Ja’e ya amsa kiran Maigari inda yayi masa gargadi akan abin da ya faru a ruga. Maigari yaje zagayen masu turjiyan rigakafi amma da alama an sami mishkila. Kadan kenan daga cikin labaran da za ku ji a shirin Madubi.
A wanan makon a Madubi, karya ta kare ma Bilkisu matar Maigari, ‘yan poliyo sun zo, asirinta ya tonu. Masu rigakafi sun je ruga yin rigakafin poliyo, amma da alama ba su ci nasara ba. Supervisor ya kai kara wajen Maigari akan bore da aka yi ma’aikatansa a ruga. Kadan kenan daga cikin labaran da za ku ji a shirin Madubi.
A wanan makon a Madubi, Maigari yaje dubiyar matar Lima da sauran jama’ansa kuma har yanzu ana fama da turjiya akan maganar rigakafi. Liman yaci karo da Faiza da Abare a zaure, ko ya zasu kare? Abare ya fada ma ubansa ya shirya aure, amma kuma kamar akwai matsala. Kadan kenan daga cikin labaran da za ku ji a shirin Madubi.
A wanan makon a Madubi, Iliya da Abare sun fada kwata, gari yayi zafi, amma kamar akwai wata dabara da suke son hadawa. Zinaru tayi yaji, ko ya zasu kare a gidansu? Kadan kenan daga cikin labaran da za ku ji a shirin Madubi.
A wanan makon a Madubi, da alama Maigari har yanzu na fama da matsalar rigakafi a gidansa. Kyauta ta shiga halin ka-ka ni kayi, ko me ya janyo hakan? Iya Sabuwa da kannen Hudu sun zo karbar kudin gadonsu, shin Hudu zai basu kuwa? Kadan kenan daga cikin labaran da za ku ji a shirin Madubi.
A wanan makon a Madubi, Zinaru fa ta hura ma Sale wuta akan sabon aure da yake son yi. Malam Tsalha ya zo karban bashin kudin sa wajen Hudu, ko zai same shi gida kuwa. Karatun Kyauta ya sami cikas saboda rashin lafiyar mahaifinta. Kawun Kyauta ya ce sai dai ai mata aure, ko ya za ta yi. Kadan kenan daga cikin labaran da za ku ji a shirin Madubi.
A wanan makon a Madubi, Yauta ya kai jami’an rigakafin poliyo ruga, bayan mutanen sun ce basu son rigakafin, ko ya zasu kare. Abare fa yace in ba Faiza ba sai rijiya, ga Liman yaki yadda ayi auren. Shin Faiza zata iya shawo kan Liman? Kadan kenan daga cikin labaran da za ku ji a shirin Madubi.
A wanan makon a Madubi, Maigari ya tura matar sa Bilkisu asibiti wajen rigakafi, ko zata je? Zinaru ta daura dammarar rigima da sale akan maganar auren sa, ko wa zai yi nasara? Kadan kenan daga cikin labaran da za ku ji a shirin Madubi.
A wanan makon a Madubi, Hudu ya ba matansa kudi ajiya ko ya za su kare? ya na kuma shirin bude babbar gona, ko ina ya sami kudi gonar? Kyauta ta shiga wani halin kaka ni kayi akan rashin lafiyar mahaifinta. Da alama kamar Hudu na kan bakarsa na kin poliyo, kadan kenan daga cikin labaran da za ku ji a shirin Madubi.
A cikin wannan makon na Madubi, muna garin Katsina in da muka yi shirin Madubi a gaban ‘yan kallo kuma muka sami tattaunawa da su!
A cikin wannan makon na Madubi, muna garin Katsina in da muka yi shirin Madubi a gaban ‘yan kallo kuma muka sami tattaunawa da su!
A cikin wannan makon na Madubi, muna garin Kano in da muka yi shirin Madubi a gaban ‘yan kallo kuma muka sami tattaunawa da su!
A cikin wannan makon na Madubi, Maigari ya tara mutanen kuka jere ko me ya sa? Hon Uba ya yanke zumuncin da ke tsakanin su da Ladidi, Ladidi ta kala wa Hajjaju laifin, shin ya abokantar Ladidi da Hajjaju zata kasance? Yauta da Ja’e za su yi gasa akan Iggy, shin cikin sun wa zai ci wannan gasar auren Iggy? Ko biyo mu ku sha Labari a cikin wannan shirin na mu na Madubi Hoton kuwa.
A cikin wannan makon na Madubi. Me ya samu Ladidi da ta ke ta saka ihu haka, Hudu zai taimaka mata kowa? Asabe ta nace da neman namban wayar supervisor, sanshi ta ke yi ne ko ko ya ya? Baba Delu ta je yiwa Ladidi fada Hudu ne ya kaita kara? Ko biyo mu ku sha Labari a cikin wannan shirin na mu na Madubi Hoton kuwa.
A wannan makon a cikin shirin Madubi. Hudu ya fara aiki da jami’an poliyo ne? Maigari ya sa a kira DPO saboda abinda Hudu, wacce irin laifi Hudu aikita? Zinaru ta samu sakon mijinta Sale zai kara auren, za ta yadda da wannan sabon salon? Maigari, DPO, Liman da supervisor sun sa Hudu ya fadi inda ya samo maganin rigakafin da ya diga wa yaransa. Za’a tafi da Hudu ko dai za’a ya fe masa wannan karon. Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.
A wannan makon cikin shirin Madubi; Maigari na samun matsala da matarsa Bilkisu ko me matsalar ta? Asabe na son ta fara aiki jami’an poliyo, me ya sa ta yin hakan? Iliya ya je zance wurin Zubaida, za su sa santa kuwa? Ziza ta tsare Baita ko me yayi mata? kadan daga labaran mu kenan a wannan mako na Madubi a yi sauraro lafiya.
A wannan makon a Madubi, Hudu ya ga uwar bari, Uwani ta nace zata koma tsohuwar gidan ta wurin sauran matan, ko me ye dalilin ta? sun yi fada da Hudu ne ko Ladidi? Iliya da abokansa sun sha bulala a padar Maigari ko me ya janyo hakan kuma me su ka yi? Labaran mu kenan a wannan mako a Madubi.
A wannan makon a cikin shirin Madubi, Liman ya je wurin Isiyaku Kafinta Neman shawara a kan Iliya, wacce irin shawara Isiyaku Kafinta zai ba shi? Ana wata ga wata, yau kuma Baita an tuno da tsohuwar soyayya ne ko dai da biyu ya je gurin Saudatu? Labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.
A cikin wannan makon na Madubi, muna garin Kano in da muka yi shirin Madubi a gaban ‘yan kallo kuma muka sami tattaunawa da su!
Wannan makon a cikin shirin Madubi, Ladidi ta shiga cikin tsaka mai wuya gashi ta na da ciki, ga Hudu ya ki bata takardar saki, ko wace irin shawara Hajjaju za ta bata wannan karon? Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.
A cikin shirin mu na wannan mako a Madubi, shin wane cecekuce ne ya faruwa tsakanin Rabe, Iliya da Tsuntsu? Maman Ummi ta zo tafiya da Ummi yaya Zinaru za ta yi kenan? Yan banga sun kama Rabe, Iliya da kusa ko wace irin tsiya ne su aikata wannan karon kuma ya za ayi da su? Labaran mu kenan na a wannan mako na Madubi.
A wannan makon a Madubi, Hudu na nan kan bakar sa na kin sakin Ladidi, shin Ladidi za ta hakura? Garus ya samu daman yin waka akan lokutan rigakafin yara, toh ko yaya wakar za ta kasance? Labaran mu kenan na a wannan mako na Madubi.
A wannan makon a Madubi, Hudu ya samu babbar bakowa, ko da me ta zo kuma wacece ita? Hudu ya je Neman aron kudi cikin gaggawa wurin Isiyaku kafinta, ko zai samu? Kuma yaya za su kare da Aminu agent batun kudin sa? Labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.
A wannan makon a Madubi, an jefo Garus daga tankar ruwa, ko me yasa haka? Baba Delu ta zo yi ma Hudu karin bayani akan amfanin rigakafin poliyo, Hudu ya kuma gaya mata matsalar sa da Ladidi. Garus ya yanke shawarar sa kayan sautin shi akan babur din sa. Hon. Uba ya sami Hudu don ya san matsayin sa akan maganar sakin Ladidi. Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.
A wannan makon a Madubi, Kyauta ta dawo gida amma ko me yasa ta gudu, Barde ya zo tadi wajen ta. Uwar Kyauta bata amince da saurayin da ta ke so, ko zata shawo kan uwar? Iliya ya zo neman kudi wajen uwarsa, shin zai samu kuwa? Saudatu ta shiga hali domin mijin ta yayi sabuwar amarya, rigima dai ta cigaba a gidan su, ko Baita zai shawo kan matan shi? Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.
A wannan makon a Madubi, malaman poliyo na zagaye don diga ma yara rigakafin poliyo. Malam Tukur ya rantse baza a diga ma yaransa rigakafin poliyo ba, shi kuma makwabcin sa Muttaka yace hakan zai shafi yaransa. Ko Liman zai daidai ta tsakanin su? Har yanzu dai ana fama da rashin ruwa kuma an cigaba da samun matsala wajen mutan gari game da rigakafin poliyo. Hudu dai ya dawo gida amma ya rasa wajen kwana, ko me yasa? Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.
A wannan makon a Madubi, kamfanin aikin gada ya kira jama’a don daukan su aikin lebura, Garus da Baita suna cikin wadanda suka je, ko ya aka kare da su? Liman ya kai Iliya kara wajen Maigari, ko zai sha bulala? An ba su Rabe izinin kafa teburin shayi wajen aikin gada, ko sun gaya ma Maishayi? Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.
A wannan makon a Madubi, an gurfanar da Barde da Garus wajen Maigari akan zargin sun sace Kyauta. Tura ta kai bango, Ladidi ta kira Baba Delu neman shawara akan Hudu, ko ya suka kare? Malam Nazifi ya je neman Kyauta wajen kakar ta, ko zai ganta? Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.
A cikin wannan makon na Madubi, Daga dukkan alamu bakin alkalami ya bushe, yau ga rusau a cikin Hauren Rafi, ko me suka zo yi? Mal Isiyaku kafinta ya turo gidan su Kyauta. Kyauta ta gudu daga gida ko ina taje? Uwani ta dawo zama a gidan Ladidi, ko Hudu zai yadda? Ko biyo mu ku sha Labari a cikin wannan shirin na mu na Madubi Hoton kuwa.
A cikin wannan makon na Madubi, Ladidi ta kosa Hudu ya sawwake ma ta dan ta kuma gidan Hon Uba ko za ta yi dace wannan karon? Iliya ya gudu daga gida, toh ku wane ne ya kwance shi? Ladidi ta je gidan Hudu ganin Uwani, Altine da Maimuna ku me dalilin zuwanta? Ko biyo mu ku sha Labari a cikin wannan shirin na mu na Madubi Hoton kuwa.
A wannan makon a Madubi, Ladidi ta fara daga jijiyoyin wuya a kan Hudu na kokarin saba wa alkawarin da su ka yi kafin auren su, ko wane irin hali Hudu zai shiga. Hon Uba da Khalifa sun je ganin Ladidi amma kaman Hudu bai gamsu da zuwan shi ba. Garus da Barde sun je wajen Kyauta ko wa zata saurara tsakanin su? Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.
A cikin wannan makon na Madubi, Daga dukkan alamu bakin alkalami ya bushe, yau ga rusau a cikin Hauren Rafi, ko me suka zo yi? Mal Isiyaku kafinta ya turo gidan su Kyauta. Kyauta ta gudu daga gida ko ina taje? Uwani ta dawo zama a gidan Ladidi, ko Hudu zai yadda? Ko biyo mu ku sha Labari a cikin wannan shirin na mu na Madubi Hoton kuwa.
Shin dan canje-canjen da rigakafi kan haifar zai iya sa ka ki kai yaronka asibiti domin karasa shan maganin?
Ga labarin wani magidanci da ya yi namijin kokari yayin da iyalinsa ta tsinci kanta a cikin wani mawuyacin hali! Shin za ka iya/ ka taba yin hakan? Ba mu naka labarin.
A wannan makon cikin shirin Madubi; Zinaru ta ka ra kiran yan kungiyan ta meeting, ko ya zu su kare. Liman dai na kan batun shi na saka ma Iliya mari, ya Gwaggo za ta yi? Maishayi da Garus sun shiga hannun yan sanda, ko me su ka yi? Kadan daga labaran mu kenan a wannan mako na Madubi a yi sauraro lafiya.
A wannan makon cikin shirin Madubi; Barde ya garzaya ya je gurin inna Hansai kakar Kyauta da ke gangaren jemagu neman auren Kyauta, ko zata yadda? ya ya tsakanin mallam Isiyaku kafinta da Kyauta ya kare bayan ya je ganin ta? Iliya ya dawo gida a cikin maye ya Liman zai da shi? Kadan daga labaran mu kenan a wannan mako na Madubi a yi sauraro lafiya.
A wannan makon cikin shirin Madubi; Saudatu ta je wurin Mal Sabo yayan Baita kai kara akan batun makarantar ta, shin Mal Sabo zai goya mata baya? Garus ya je ganin Barde akan ya bar ma sa Kyauta, ko ya ya za su kare? Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.
A wannan makon a Madubi, kungiyar su Zinaru na shirye-shiryen hada taron lafiya amma an samu matsala wajen sha’anin kudi. An samu an sasanta tsakanin Maishayi da Rabe, ko ya suka kare? Ana ta tsegumin cewa Liman ya karbi kudi don yada amfanin rigakafi, ko hakan gaskiya ne? Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.
A wannan makon a Madubi, Maigari ya fito yawon rigakafi da ’yan polio. Ganin haka, Hudu ya yarda anyi ma yaran shi rigakafi. Har yanzu dai Baita ya ki ya amince ma Saudatu tarewa a makaranta. Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.
A wannan makon a Madubi, Maigari ya shirya aikin gangi don kariya daga kamuwa da ciwon cholera. Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.
A wannan makon a Madubi, mutanen Hauren Rafi sun je wajen Chairman don neman a tsaida korar su daga wajen sana’ar su, ko sun yi dace? Hudu ya kai Ladidi duba gida, amma kudin gida sun canza, ko za ta sayi gidan? Hudu na shirin bude gidan gona. Amarya ta tare a gidan Baita amma har yanzu dai ya kasa shawo kansu. Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.
A wannan makon a Madubi, anyi meeting na shirin rigakafi a Kuka-Jere, an kawo rahoton barkewar cholera a Gangaren Jemagu. Maigari ya yi alkawarin zagaya wa da ma’aikatan polio. Maman Kyauta ta nemi izni Kyauta ta koma talla a Gangaren Jemagu ko baban ya yarda? Garus ya tasa kudi gaba yana ta hidima, amma ko hakan zai taimaka mashi kuwa? Maishayi ya kawo shawarar zuwa wajen Chairman don neman a shawo kan matsalar wajen sana’ar su. Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.
A wannan makon a Madubi, Maigari ya yi wa mutan gari akan maganar diya na filayansu, Maishayi da sauran abokan sana’ar sa basu dai gamsu ba. Rabe ya samu anyi belin shi, amma ko ya zasu kare da wansa Maishayi? Mijin Zinaru ya fara damuwa da zirga zirganta akan maganar kungiya, zasu daidaita kuwa? Kadan daga labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.
Ku saurari labarin da wata mata ta bayar game da abinda ta fuskanta a dakin haihuwa a shirinmu na Ya Take Ne Arewa.
A wannan makon a shirin Madubi, an daura auren Baita da Ziza. ‘Yan uwan Barde za su je neman aure gidan su Kyuata, ko ya zasu kare? Garus yaga uwar bari, ya na so ya nuna ma Kyauta ya na son ta, amma za ko ta saurare shi? Hudu ya ba Maishayi shawara ya rubuta jarabawar WAEC, ta ina zai fara? Kadan daga cikin labaran mu kenan a wannan makon na Madubi.
A wannan makon a shirin Madubi, Baba Delu ta bunkasa sana’ar ta da masa, amma shin za ta more wannan bunkasa kuwa? Iliya da su Rabe sun soki wani da wuka wajen aikin su, ko ya mutu? Uwani ta tunkari Hudu da maganar kudin asibiti, har yanzu dai bai ga amfanin zuwa asibiti. Har yanzu Baita na nan kan bakar sa na yin sabuwar amarya. Kadan daga cikin labaran mu na wannan makon a Madubi.
A cikin wannan makon na shirin Madubi, Maganar ciki ba magana ba ce Ladidi na boye wa Baba Delu zancen auren ta. A na wata ga wata, Maishayi dai ya nace sai ya zama counsellor a garin kuka-jere amma da sharruda, ance sai ya kawo takaddun makaranta, shin ya na da su? Barde ya je ganin Kyauta amma mahaifiyar ta ce ta fito, ko ya suka kare? Ko biyo mu ku sha Labari a Madubi.
A wannan makon a cikin shirin Madubi, Jamilu ya koma makaranta ko waye ya dauki nauyin biyan kudin? Hudu ya je neman taimako wajen Liman, ko me ya kai shi? Anyi ma Kyauta miji, ko zata yarda? Labaran mu kenan na wannan mako a Madubi ayi sauraro lafiya.
A wannan makon a cikin shirin Madubi, Jamilu ya koma makaranta ko waye ya dauki nauyin biyan kudin? Hudu ya je neman taimako wajen Liman, ko me ya kai shi? Anyi ma Kyauta miji, ko zata yarda? Labaran mu kenan na wannan mako a Madubi ayi sauraro lafiya.
A wannan makon a cikin shirin Madubi, Zinaru ta je asibiti ganin likita ko me ke damunta? Yau kuma ga wani sabon zance Ladidi ta na son ta koma gidan mijinta gashi babu aure a tsakanin su ya ya kenan? Toh Baita da Saudatu kuma ya za su kare akan batun barin dakin ta ma sabuwar amarya? Ku biyo mu ku sha labari a wannan mako na Madubi.
A wannan makon a Madubi, Maishayi ya fara zagaya jama’an gari don samun shiga wajen siyasa. Kyauta taje neman taimako wajen Zinaru, ko za ta samu? Hon. Uba ya dawo wajen Ladidi, amma haduwar an kare da hushi saboda Khalifa ya bace. Barde ya zo neman Garus domin su shirya yadda za su je wajen Kyuata. Baita ya gaya ma Saudatu zai sake aure, ko ya suka kare? Labaran mu kenan na a wannan mako na Madubi
A wannan makon a Madubi, Hudu na nan kan bakar sa, har yanzu ya ki yarda Uwani ta kai Abba asibiti, shin Uwani za ta hakuri ta koma gidan sa? Barde ya sami labarin auren Kyauta, shin Garus ya isar da sakon sa ga Kyauta? Garus ya cinye ma Kyauta kudi, ga Iliya can kuma gidan Liman ya sace waya . Labaran mu kenan na a wannan mako na Madubi.
Kaka-sara-kaka! Delu tsohuwa mai ra'ayi rikau! Yaya tsakaninsu zai kasance da liman? In ka ki ji! Ba ka ki gani ba. Jiki dai ance magayi ne. Ko hudu zai ladabta da wannan sakamako.
A wannan makon a Madubi, Yagana ta samu izinin kai yara asibiti don rigakafi. Garus ya shiga gasar wakoki amma baya da kudin zuwa, ko zai iya samun rance? Baita ya sha mari, ko wa ya mare shi da laifin sa? An gano Khalifa a tashar jirgin sama a Ethiopia. Labaran mu kenan na a wannan mako na Madubi.
A wannan makon a Madubi, Garin Kuka – jere zata jagoranci Garin Gabas a kwallon kafa da zaa yi nan gaba. Yau Ladidi tayi bako, ko wanene shi? Malamar Kyauta zata je gidansu Kyauta don ganin mahaifinta, ko meyasa? Labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.
A wannan makon a Madubi, Barde ya nemi shawaran Maginet da Zico don ayi amfani da kudin asusun dambe a biya wa Jamilu kudin asibiti. Baba Delu na shawaran barin garin Kuka – jere ta koma garinsu. Mijin Uwani ya hana a yiwa yayansa rigakafi. Labaran mu kenan na wannan mako a Madubi.
Dan Hudu bashi da lafiya, kuma likita na tunanin ya kamu da ciwon polio. An kawo karar Iliya da Rabe wajen Maigari, ko menene laifinsu? Ladidi ta saida gwal dinta don ta biya kudin tikitin Khalifa. Labaran mu kenan a wannan makon a Madubi.
Hudu ya fara kmmala shirin tafiya Saudi Arabia, shin zai iya cika kudin tafiyar? An sace ma Saudatu kudin adashe, ko barawon gida ne? Maigari ya kaddamar da rigakafin polio, da iyalan sa. Kadan daga cikin labaran mu na wannan mako kenan ashirin Madubi.
Sannun Ku. If you missed Madubi on your radio, catch up now at your leisure. Enjoy this fun 15 minute Hausa drama!
Sannun ku. Have you missed Madubi on your radio? Then listen NOW. Catch up on Series 1 and enjoy all the fun and drama!
Sannu. The Madubi Team are busy recording Series 2 for you! But in the meantime, catch up on Series 1. Enjoy all the fun and drama!
Sannu, the Madubi Team are busy recording Series 2 for you! Coming soon…… But in the meantime, if you haven’t heard Madubi on your local radio station then have a listen to Season 1 Episode 1. Enjoy!