BBC Hausa: Recent Episodes

BBC Hausa

Wannan shafin na BBC Hausa ne inda za ku dinga sauraron shirye-shiryen da suka shafi rayuwarku. Ku kasance tare da wannan shafin don sannin labarai da dumi-duminsu. Muna da shafi a Twitter da Facebook da kuma Google+.

View Details

Shirin wasan kwaikwayo na Gatanan gatanan ku wanda BBC Media Action ke shiryawa

View Details

Muryar Seini Oumarou, daya daga cikin masu takara don kalubalantar shugaba mai ci, Muhammadou Issoufou, dangane da damuwar da ya nuna kan jinkirin da aka samu na fara zabe a kan lokaci.

View Details

Shugaban jamhuriyar Nijar, Muhamadou Issoufou, ya bayyana cewa zaben kasar da ake gudanarwa a yau zai karfafa tsarin dimokuradiyayya a kasar.

View Details

Ku saurari shirinmu na safiyar yau, wanda Haruna Shehu Marabarjos ya gabatar mana da shi.

View Details

A tattaunawar ta 'Presidential Media Chat' wacce ita ce irinta ta farko da ya yi tunda ya hau mulki, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa nada shirin sasantawa da kungiyar Boko Haram, Abdullahi Kaura Abubakar ya bibiyi tattaunawar, na kuma tambayeshi karin bayani game da irin abubuwan da aka tabo.

View Details

Ku saurari hirar shugaba Buhari da BBC, kan batun inda aka kwana don kawo karshen kungiyar Boko Haram a wannan wata na Disamba.

View Details

Ko yaya jama'a ke kallon afuwar da Shugaba Buhari ya nema wajen 'yan Najeriya? Wakilin mu Yusuf Ibrahim ya tattaro mana ra'ayoyin jama'a daga gidan mai. Ku surara a nan.

View Details

Ku saurari shirinmu na safiyar yau, wanda Haruna Marabarjos ya gabatar mana da shi.

View Details

Ku saurari shirinmu na safiyar yau, wanda Haruna Shehu Marabarjos ya gabatar mana da shi.

View Details

Har yanzu matsalar mai a Nigeria na kara ta'azzara, inda yan kasar ke kwana a gidajen mai, amma ba tare da sun samu man ba a wasu lokuta. Ku saurari rahoton da Yusuf Ibrahim Yakasai ya aiko mana.

View Details

Ku saurari shirinmu na safiyar yau, wanda Ibrahim Isa ya gabatar mana da shi.

View Details

A Nigeria, wasu malaman addinin Musulunci na ci gaba da jaddada muhimmancin samar da ilimi ga 'ya'ya mata don ci gaban al'umma. Ku saurari hirar Sheikh Malam Ibrahim Khaleel, shugaban kungiyar Majalisar Malamai ta jihar Kano da Yusuf Tijjani.

View Details

Ku saurari shirinmu na safiyar yau, wanda Ibrahim Isa ya gabatar mana da shi.

View Details

Shugaban Tanzania John Magufuli ya fito titi yana kwashe shara, shin meye ya sanya shi wannan aiki? Shin wane irin mutum ne John Magufuli? Tambayar ke nan da Muhammad Annur Muhammad ya fara yi wa Dr. Abubakar Kari, masanin kiyiyyar siyasa a jami'ar Abuja. Ku saurari hirarsu.

View Details

Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta ce akwai kananan yara kimanin dubu biyar, wadanda har yanzu ba su san inda iyayensu suke ba. Ku saurari rahoton da Ishaq Khalid ya hada mana.

View Details

Babu fina-finan Hausa a cikin jerin fina-finan da aka gabatar don shiga gasar Kumawood Akoben Film Festival da za a gudanar a Ghana. Ku saurari karin bayanin da Mallam Abdul Salam Magaji daya cikin shugabannin kungiyar masu shirya fina-finan Hausa na Ghana ya yi wa Iddi Ali.

View Details

Ku saurari shirinmu na safiyar yau, wanda Haruna Shehu Marabarjos ya gabatar mana da shi.

View Details

Kafar yada labarai ta BBC ta gano cewa, akwai yiwuwar an kuskure wata dama da aka samu a can baya, ta kama madugun 'yan bindigan da suka kaddamar da hare-hare a cikin watan jiya a Paris. Ku saurari rahoton da Yakubu Liman ya hada mana.

View Details

Sakataren harkokin wajen Birtaniya,Mista Milliband, ya ziyarci 'yan gudun hijirar a arewa maso gabashin Najeriya, kuma ya ce wajibi ne shugabannin duniya su kara himma wajen taimaka musu. Ku saurari rahoton da Ishaq Khalid ya hada mana.

View Details

Makoko na daya daga cikin tsofafin matsugunnan marassa galihu a birnin Lagos, inda hatta makarantu na koyar da yara don ganin sun samu rayuwa ta gari, a kan ruwa suke. Ku saurari fassarar rahoton Martin Patience.

View Details

Sabon ministan yada labarai na Nigeria Lai Muhammad, ya jagoranci wata tawagar 'yan jaridu zuwa garin Bama na jihar Borno, tare da rakiyar sojoji, domin ganin irin barnar da aka yi a garin Bama. Bashir Sa'ad Abdullahi na cikin wannan tawagar, ku saurari rahoto na musamman da ya hada mana.

View Details

Ku saurari shirin mu na safiyar yau, wanda Haruna Shehu Marabarjos ya gabatar mana da shi.

View Details

A Najeriya wasu 'yan kabilar Igbo dake zaune a arewacin kasar sun bayyana rashin jin dadin su dangane da ci gaba da zanga zangar da masu neman kafa kasar Biafra ke yi. Ku saurari hirar Haruna Shehu Tangaza da Elder Steven Akoma, daya daga cikin shugabanin al'ummar Igbo mazauna jihar Sakkwato.

View Details

Bilkisu Sab'iu Bako, wata da ta tsunduma harkar shirya shagulgulan biki da taruka wadda kuma a halin yanzu take da ma'aikata kimanin 200 da ke cin abinci a karkashinta. Ku saurari hirarta da Halima Umar Saleh.

View Details

Rabi Maidunama wata matashiya ce da ta wahala sosai sakamakon fama da take yi da matsananciyar wahalar cutar amosanin jini, don haka ta kafa wata gidauniya don ta tallafa masu irin wannan cuta. Ku saurari hirar ta da Bara'atu Ibrahim a nan,

View Details

Kawancen wasu kungiyoyin kare muhalli ne suka yi wani maci kan sauyin yanayin. Ku saurari rahoton Abdullahi Kaura Abubakar.

View Details

Ku saurari Mohammed Abdu da Labaran Wasanni.

View Details

Hausawa dai na cewa babu nakasasshe sai kasasshe. Yayin da wasu mutane kan buge da yin barace barace idan sun samu wata nakasa, wata matashiya da take da lalurar jin magana, har litatafai take rubutawa. Ku saurari hirara Matashiyar Sumayya Qaribullah Nasuru Kabara da Yusuf Ibrahim Yakasai.

View Details

Ku saurari shirin mu na safiyar yau, wanda Usman Minjibir ya gabatar mana da shi.

View Details

A ci gaba da shirin nan na 'mace 100 na BBC', wakiliyarmu Tchima Illa Issoufou ta tattauna da Hadjia Fatime wata mata a jahar damagaram da ta bude gidan marayu. Ku saurari hirar su a nan,

View Details

Jami'an tsaro sun kama Bello Chindo, a filin jirgin sama na Abuja, inda suka ce yana cikin 'yan Boko Haram su dari, da aka fi nema ruwa-a-jallo, wadanda aka wallafa hotunansu. Iyalan sa dai sun musanta zargin. Ku saurari rahoton da Is'haq Khalid ya hado mana.

View Details

Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF, ya ce nan da kimanin shekaru talatin da biyar, adadin yara mata da akan aurar da su tun ba su kosa ba, a nahiyar Afirka, zai ninka fiye da sau biyu, inda adadin zai kai miliyan 310.

Ku saurari rahoton wakilinmu, Is'haq Khalid, domin jin karin bayani.

View Details

Mun tattauna da Abubakar Adam Ibrahim da Elnathan John, wasu matasan marubuta na arewacin Nigeria kan sabbin littattafan da suka wallafa.

View Details

Fassarar kalaman Yaya Toure , dan wasan kasar Ivory Coast, da kuma kulob din Manchester City a Ingila.

View Details

Ku saurari fassarar kalaman Sadio Mane, dan wasan kasar Senegal.

View Details

Ku saurari shirinmu na safiyar yau, wanda Usman Minjibir ya gabatar mana da shi.

View Details

Rikicin miji da mata ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu 'yan gida, yayin da na biyar din ke kwance rai hannun Allah a asibiti. Ku saurari rahoton wakilinmu Nurah Mohammed Ringim.

View Details

Shin za ka iya zama da matar da bata iya girki ba? Ku saurari hira da Aisha Bappa ta yi da wata amarya da bata taba yin girki ba har ta yi aure.

View Details

Ku saurari shirnmu na safiyar yau, wanda Usman Minjibir ya gabatar mana da shi.

View Details

Ku saurari fassarar kalaman Yacine Brahimi, dan wasan kasar Algeria.

View Details

A Jerin shirye-shirye da hirarrakin da kan tattauna a kan matan da suka yi fice ko suka zama abin koyi a tsakanin al'umma BBC ke kaddamarwa. Ku saurari hirar Tchima Illa Issoufou da Aishatou Joel, mai rike da Sarautar Noma ta Damagaram.

View Details

Faransa da Rasha sun zafafa hare hare ta sama da suke kai wa kungiyar IS a Syria. Ku saurari fasarar rahoton Olivier Webber.

View Details

Ku saurari shirin mu na safiyar yau, wanda Usman Minjibir ya gabatar mana da shi.

View Details

BBC ta yi hira da dukkaninsu, kuma za a rika gutsuro kadan daga ciki. A yau an tuntubi Andre Ayew ne, dan wasan kasar Ghana. Ku saurari Fassarar kalaman.

View Details

A yau ne ake sa ran shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kaddamar da wani gagarumin shirin bayar da bashi ga manoman shinkafa. Ku saurari rahoton da Haruna Shehu Tangaza.

View Details

A kasar Ghana da alamu binciken da dan jaridar nan Anas Armiya'u Anas ya gudanar kan wasu alkalan kasar ya bar baya da kura. Ku saurari rahoton wakilinmu Iddi Ali.

View Details

Ku sauraryi shirin mu na safiyar yau, wanda Usman Minjibir ya gabatar mana da shi.

View Details

BBC ta yi hira da dukkanin gwarzayen 'yan wasan kwallon kafa na Afrika, kuma za a rika gutsuro kadan daga ciki. Ga fassarar kalaman dan wasan nan Emerick Pierre Aubameyang.

View Details

Ko me ya sa fafutukar yunkurin na kafa jamhuriyyar Biafra yake dada kamari a 'yan watannin nan? Ku saurari rahoton wakilinmu AbdusSalam Ibrahim Ahmed.

View Details

Masana tattalin arziki a Najeriya na cewa faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya ya shafi tattalin arziki da kuma darajar kudin kasar. Ku saurari rahoton Umar Shehu Elleman, kan wannan batu.

View Details

Ku saurari shirinmu na safiyar yau, wanda Ibrahim Mijinyawa ya gabatar mana da shi.

View Details

Wasu mata da suka kai ziyara wasu sansanonin 'yan gudun Hijira a jihar Borno sun koka da irin mawuyacin halin da mazauna sansanonin ke ciki. Dr. Rahama Hasan na daya daga matan da suka kai ziyara sansanin Dalori a jihar Borno, ku saurari hirar su da Yusuf Ibrahim Yakasai.

View Details

Ku saurari shirin mu na safiyar yau, wanda Haruna Shehu Marabar Jos, ya gabatar mana da shi.

View Details

Wani sabon bincike ya bayyana cewa alkaluman zubar da ciki a Nigeria sun matukar karuwa daga dubu 61 a 1996 zuwa sama da miliyan daya a shekarar 2012. Ku saurari rahoton Yusuf Ibrahim Yakasai.

View Details

A Najeriya yau ne ake shiga rana ta biyu kuma ta karshe, a taron bitar da ake yi wa sabbin ministocin gwamnatin kasar 36 gabanin rantsar da su. Ku saurari rahoton Haruna Shehu Tangaza.

View Details

Birtaniya za ta soma kwashe dubban 'yan kasarta da suka makale a Masar a yau. Ku saurari rahoton da Ibrahim Mijinyawa ya hada mana kan wannan batu.

View Details

Har yanzu furucin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi cewa cikin ministocin da za a nada za a samu wadanda ba lalle ne a ba su rikon wata ma'aikata ba, na ci gaba da janyo kace nace. Jaafar Jaafar, wani dan jarida kuma mai sharhi akan al'amuran yau da kullum a Nigeria, ya tattauna da Muhammad Annur Muhammad. Ku saurara a nana,

View Details

A Najeriya, wani dattijon dan siyasa Alhaji Tanko Yakasai ya soki yadda shugaban kasar Muhammadu Buhari ke tafiyar da al'amuran kasar. Za ku ji kuma martanin da fadar shugaban kasar ta mayar a hirar da kakakin Shugaba Buharin, Garba Shehu ya yi da Haruna Shehu Tangaza.

View Details

Ku saurari shirin mu na safiyar yau, wanda Ibrahim Mijinyawa ya gabatar mana da shi.

View Details

Esther Kalenzi ita ce ta kafa kungiyar agaji mai suna 40 days 0ver 4 smiles shekaru uku da suka gabata. Ku saurari fasssarar rahoton wakiliyar BBC Catherine BYaruhanga, wacce ta yi kicibis da ita yayin da take wannan aiki da ta kaddamar.

View Details

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yana kan bakarsa na takaita yawan ministocin gwamnatinsa saboda halin da tattalin arzikin kasar ke ciki. Ku saurari rahoton da Haruna Shehu Tangaza ya hada mana.

View Details

Gidauniyar da ke fafutukar kare hakin Zabiyan Najeriya ta koka da yadda babban asibitin kasar da ke Abuja ya dakatar da kula da lafiyar mambobinsu. Ku saurari rahoton da Badriyya Tijjani Kalarawi ta hado mana.

View Details

A Najeriya, ana ci gaba da kace nace tsakanin jam'iyar adawa ta PDP da kuma fadar shugaban kasar dangane da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki. Ku saurari rahoton da Abdou Halilou ya hada mana.

View Details

Gwamnonin jihohin Nijeriya 'yan jam'iyyar APC mai mulki, sun shawarci shugaba Buhari da ya cire tallafin man fetur, domin ci gaban tattalin arzikin kasar. Meye ku ka gani ga wannan batu? Ga dai hirar shugaban kungiyar gwamnonin jihohin, Cif Rochas Okorocha da wakilinmu Ishaq Khalid game da wannan batu.

View Details

Ku saurari shirin mu na safiyar yau, wanda Ibrahim Mijinyawa ya gabatar mana.

View Details

A Nigeria, yau ne wa'adin da babban bankin kasar ya bada na kammala rijistar masu asusun ajiya a bankunan kasar domin samun lambar nan da ake kira BVN ke cika. Ku saurari hirar Malam Ibrahim Mu'azu wanda shi ne daraktan yadda labarai a babban bakin Najeriyar watau CBN, da Abdou Halilou.

View Details

An tashi baram-baram a majalisar dattawan Najeriya kan batun jefa kuria'r amincewa da nadin tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi a zaman minista. Ku saurari rahoton da Haruna Shehu Tangaza ya hada mana.

View Details

Wani bincike da masu kare muhalli a nahiyar Afrika suka gudanar ya nuna cewa akwai wasu nau'ukan tsuntsaye da ke fuskantar barazanar bacewa daga doran kasa. Ku saurari hirar Muhammad Annur Muhammad da Malam Salisu Dahiru, kan wannan batu.

View Details

Rabon mukaman shugabancin kwamitocin majalisar wakillan Najeriya da kakakinta Hon.Yakubu Dogara ya yi, ya raba kawunan 'yan jam'iyya mai mulki ta APC da ke majalisar. Ku saurari rahoton Haruna Shehu Tangaza.

View Details

Ku saurari shirin mu na safiyar yau, wanda Ibrahim Mijinyawa ya gabatar mana da shi.

View Details

Marie Konate, wata mata mai hangen nesa a kasar Ivory Coast, ta fara sana'ar sayar da abincin jarirai shekaru 20 da suka gabata. Wakiliyar BBC Suzanne Vanhooy-missen ta je har birnin Abidjan don neman karin bayani, ku saurari fassarar rahoton ta.

View Details

A yau ne aka shiga rana ta uku ta babban taron da India ke yi da kasashen Afirka a birnin Delhi. Wakilinmu Is'haq Khalid ya duba mana wasu daga cikin abubuwan da kasashen Nijeriya da India ke da su masu kama da juna, ku saurari rahotonsa.

View Details

Wasu 'yan gudun hijira daga jihar Yobe sun koka da cewa su ba su da sansanoni a cikin jahar. Ku saurari rahoton da Abdou Halilou ya hada mana.

View Details

Yau ne ake sa ran Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai tashi zuwa kasar ta India domin halartar wani babban taron kasashen Afirka da Indiyar. Ku saurari rahoton Muhammad Kabir Muhammad, da kuma hirar da Muhammad Annur Muhammad ya yi da mataimaki na musamman ga shugaba Buhari kan harkar yada labarai, Garba Shehu.

View Details

Ku saurari shirin mu na safiyar yau, wanda Ibrahim Mijinyawa ya gabatar mana da shi.

View Details

Masana harkar lafiya a Najeriya sun nuna damuwa game da yawan karuwar larurar yoyon fitsari a tsakanin matan kasar. Ku saurari hirar wakilin mu Yusuf Ibrahim Yakasai inda ya tambayi wani kwararren likitan mata Dr. Habibu Sadauki yadda girman matsalar take.

View Details

Fagen kade-kade na Najeriya ya samar da mashahuran mawaka a 'yan shekarun nan, kuma ra'ayinsu ba wai a nan cikin gida kadai ba, har ma da kasashen waje. Ku saurari fassarar rahoton Will Ross.

View Details

Ku saurari shirin mu na safiyar yau, wanda Usman Minjibir ya gabatar.

View Details

Wane irin nama ne ke janyo ciwon daji? Ku saurari rahoton Badariyya Tijjani Kalarawi.

View Details

An samu wata girgizar kasa mai karfin gaske a arewa maso gabashin Afghanistan har sai da aka ji karar ta a Pakistan da India. Ku saurari rahoton Badariyya Tijjani Kalarawi aka wannan batu.

View Details

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ba wa shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya janye tallafin man fetur tare kuma da rage darajar kudin kasar. Ku saurari karin bayanin da Dr Nazifi Darma, wani masanin tattalin arziki a Najeriya, da ya yiwa Yusuf Tijjani.

View Details

Shugabannin kasashen tsakiyar turai dana yankin balkan sun amince da wani tsarin da zai kawo karshen matsalar 'yan gudun hijra a yankunan. Ku saurari rahoton da Raliya Zubairu ta hada mana.

View Details

Jami'iyyar APC ta bayar da karin haske akan tantance Rotimi Amaechi a matsayin minista. Sanata Abu Ibrahim dan Majalisar dattawa ne daga jam'iyyar APC, ku saurari hirar su da Yusuf Tijjani.

View Details

A ranar Lahadi mai zuwa ne al'ummomin kasar Tanzaniya za su fita domin kada kuri'a a zaben shugaban kasar. Ku saurari fassarar rahoton Sammy Awami.

View Details

Ku saurari labaran wasanni, wanda Muhammad Abdu , Mamman Skipper ya gabatar mana.

View Details

Millen Mage-se wata gwarzuwar mace ce a Afirka da bata damu a rika koda ta ba. Ku saurari Ku saurari fasarar rahoton Leslie Goffe, kan hikimar da wannan gwarzuwa da ta taba lashe gasar sarauniyar kyau a Tanzaniya.

View Details

Majalisar dattawan Najeriya ta dage zamanta na yau Laraba zuwa gobe Alhamis don ci gaba da tantance sunayen ministoci. Ku saurari hirar Sanata Bala Ibn Na'Allah, mataimakin shugaban kwamitin da'a na Majalisar dattawan da Yusuf Tijjani.

View Details

Rahama Sadau, tauraruwar Kannywood, ta bayyana dalilan da suka sa ake yin raye-raye da wake-wake a cikin fina-finan Hausa, da kuma kalubalen da harkar ke fama da shi.

View Details

Ku saurari shirin safe na ranar 20 ga watan Oktoba shekarar 2015.

View Details

Shekara guda cif kenan da hukumar lafiya ta duniya, WHO ta ayyana Nigeria a matsayin kasar da ta kawar da cutar Ebola a cikin kasarta. Dr Faisal Shuaibu shi ne ya jagoranci cibiyar yaki da cutar Ebolan a Nigeria, ku saurari hirarsa da Aliyu Abdullahi Tanko.

View Details

Wasu kungiyoyin mata da na matasa masu fafutuka na korafin cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari ya nuna masu banbanci wajen mika sunayen ministoci. Ku saurari rahoton da Abdou Halilou ya hada mana.

View Details

Jam'iyyar APC tace suka da jam'iyyar PDP ta ke yi , ba zai hana gwanatin tarayyar binciken mutanen da ake zargi da cin hanci ba. Ku saurari rahoton Umar Shehu Elleman.

View Details

Jami'an tsaro a jihar Agadez ta Jamhuriyar Niger na ci gaba da tsare wani dan jarida daga Nigeria da ya je kasar don neman labarai.

Shi dai dan Jaridar mai suna Lawal Adamu da ke aiki a kamfanin jaridar DailyTrust a Nigeria ya je Nijar din ne don gudanar da bincike akan matsalar tururuwar matasa yanci rani da ke ratsawa ta Jamhuriyar Nijar daga wa su kasashen Afrika zuwa kasashen turai.

Ga hirar wakilinmu Yusuf Tajjani da Malam Mannir Dan Ali babban jami'i a kamfanin jaridar ta Dailytrust.

View Details

ami'an tsaro a jihar Agadez ta Jamhuriyar Niger na ci gaba da tsare wani dan jarida daga Nigeria da ya je kasar don neman labarai.

Shi dai dan Jaridar mai suna Lawal Adamu da ke aiki a kamfanin jaridar DailyTrust a Nigeria ya je Nijar din ne don gudanar da bincike akan matsalar tururuwar matasa yanci rani da ke ratsawa ta Jamhuriyar Nijar daga wa su kasashen Afrika zuwa kasashen turai.

Ga hirar wakilinmu, Yusuf Tajjani da Malam Mannir Dan Ali babban jami'i a kamfanin jaridar ta Dailytrust.

View Details

A Najeriya, wasu masu hada-hadar kasuwar hannayen jari sun koka game da yadda farashin hannayen jarin ke ci gaba da faduwa.

A yanzu haka dai kasuwar hannayen jarin ta fadi warwas tun farkon shekarar nan da kusan kashi 14 cikin 100.

Domin jin karin bayani ku saurari hirar wakiliyarmu, Halima Umar Saleh da Malam Kasimu Kurfi, wani mai hada-hada a kasuwar hannayen jari ta Najeriya.

View Details

A Najeriya, rahotanni daga Adamawa na cewa wasu mahara da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe mutane 12 a wani hari da suka kai kauyen Dar dake karamar Hukumar Madagali

Rahotannin sun ce maharan wadanda suka hada da mata 'yan kunar bakin wake, sun isa kauyen ne ranar Asabar da misalin karfe takwas da rabi na dare.

Ku saurari hirar wakilinmu, Haruna Shehu Marabar Jos da Mista Maina Ularamu, tsohon shugaban karamar hukumar Madagali domin jin karin bayani.

View Details

Shugabannin tarayyar turai da suke tattaunawa a Brussels sun ce sun cimma matsaya kan shirin da suke yi na neman tallafin kasar Turkiyya da nufin magance matsalar kwararar y'an gudun hijra zuwa turai. Ku saurari rahoton da Raliya Zubairu ta hada mana domin jin karin bayani.

View Details

Majalisar dattawan Najeriya ta bayyana damuwarta dangane da sake bude kan iyakokin kasar domin shigo da shinkafa zuwa Najeriyar. A wani kudiri, majalisar ta ce matakin ka iya sake mayar da hannun agogo baya wajen noman shinkafa a kasar.

Ta kuma kira shugaban hukumar hana-fasaauri ta kasar, Kanar Hamidu Ali mai ritaya da bayyana a gabanta sannan ya yi mata bayanin dalilin da yasa hukumar take barin ake shigo wa da shinkafar.

Domin jin karin bayani, ku saurari hirar wakilinmu Yusuf Tijjani da Sanata Adamu Aleiro.

View Details

Sababbin alkalumma da ke fitowa daga hukumomin jamhuriyar Kamaru na nuna cewa kawo yanzu adadin 'yan kasar da suka rasa rayukansu a turmutsutsun da aka yi a Muna a kasar Saudi Arabia lokacin aikin hajjin bana, ya kai 76 sannan wasu da dama sun jikkata a inda kuma har yanzu ba aji duriyar wasu ba.

Gwamnatin kasar dai ta ayyana yau Juma'a domin ta zamo ranar nuna alhini dangane da rashin da kasar ta yi. Ku saurari Usman Minjibi da wikilinmu Muhammad Babalala domin jin karin bayani.

View Details

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce mutane 30 ne aka kashe yayinda da dama suka ji raunuka a hare haren kunar bakin wake da wasu da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne suka kai a gaban wani masallaci a unguwar Mulai a birnin Maiduguri. Ku saurari rahoton da wakiliyarmu Raliya Zubairu ta hada mana domin jin karin bayani.

View Details

Ku saurari shirin safe na BBC na ranar Jumma'a 16 ga watan Oktoba, 2015.

View Details

Ku saurari shirinmu na safe daga nan Sashen Hausa na BBC.

View Details

Sakamakon wani bincike da aka fitar wannan mako na nuna cewa kasashen da yawansu ya kai 52 ne daga kasashe masu tasowa ke fuskantar matsanaciyar yunwa. Ku saurari hirar Abdullahi Tanko Bala da Muhamman Babalala,

View Details

Majalisar dattawan Najeriya za ta ci gaba da tantance mutanen da shugaban kasar ya mika mata a zaman ministoci a gwamnatin kasar. Ku saurari rahoton da Haruna Shehu Tangaza ya hada mana.

View Details

Yau ne majalisar dattawan Najeriya za ta ci gaba da aikin tantance mutane 37 da shugaban kasar ya aika mata, Ku saurari hirar Haruna Shehu Tangaza, da daya daga cikin 'yan majalisar Senata Tijjani Yahaya Kaura.

View Details

Shin kun taba shiga cikin wani yanayin da ba kwa iya gane mutane, kamar mahaifiya, ko `ya'ya, ko kuma abokai ko makwabta da sauran su? Wakiliyar BBC Yusta Seghete ta duba mana wannan cuta da ba kasafai ake ganin irin ta ba. Ku saurara a nan,

View Details

Akwai wasan kwaikwayo da aka shirya a Najeriya, wanda ke nuna wa mutane irin rashin tabbas da aka shiga a yayin da cutar Ebola ta bulla a kasar, a bara. Ku saurari rahoton da wakilin BBC Will Ross, ya hada mana.

View Details

A yau ne a Netherlands ake sa ran gabatar da rahoton faduwar jirigin saman Malysiayan Airlines mai Lamba MH-17, wanda ake zargin an harbo shi ne a gabashin Ukraine mai fama da yaki a watan Yulin shekarar da ta wuce.

Ana kyautata zaton cewa hukumar kula da lafiyar jiragen sama ta kasar, wacce ta gudanar da bincike kan rikitowar jirgin, ba za ta fadi wanda keda alhakkin harbo jirgin ba.

Ku saurari rahoton da wakilinmu Yakubu Liman ya hada mana domin jin karin bayani.

View Details

A yau ne a Netherlands ake sa ran gabatar da rahoton faduwar jirigin saman Malysiayan Airlines mai Lamba MH-17, wanda ake zargin an harbo shi ne a gabashin Ukraine mai fama da yaki a watan Yulin shekarar da ta wuce.

Ana kyautata zaton cewa hukumar kula da lafiyar jiragen sama ta kasar, wacce ta gudanar da bincike kan rikitowar jirgin, ba za ta fadi wanda keda alhakkin harbo jirgin ba.

Ku saurari rahoton Yakubu Liman domin jin karin bayani.

View Details

A kasar Guinea 'yan takarar shugaban kasa bakwai na bangaren adawa sun ce, ba zasu amince da sakamakon zaben shugaban kasar ba, kuma sun yi kiran ayi sabon zaben.

Sun dai zargi hukumar zaben kasar da hada baki da jam'iyya mai mulki wajen murde zaben da aka yi ranar Lahadi.

Ku saurari fassarar rahoton Abdourahmane Dia daga birnin Dakar, domin jin karin bayani.

View Details

A Najeriya, yau ne 'yan Majalisar dattawan kasar zata fara tantance mutanen da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar musu a matsayin wadanda ya ke son nadawa a matsayin ministoci a gwamnatinsa.

Kazalika a yau din kuma ake saran shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki zai bayyana karin sunayen da shugaban kasar ya mikawa Majalisar a jiya Litinin.

Ku saurari rahoton da wakiliyarmu Bara'atu Ibrahim ta hada mana domin jin karin bayani

View Details

A Najeriya, yau ne 'yan Majalisar dattawan kasar zata fara tantance mutanen da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar musu a matsayin wadanda ya ke son nadawa a matsayin ministoci a gwamnatinsa.

Kazalika a yau din kuma ake saran shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki zai bayyana karin sunayen da shugaban kasar ya mikawa Majalisar a jiya Litinin.

ku saurari rahoton da wakiliyarmu Bara'atu Ibrahim ta hada mana domin jin karin bayani.

View Details

Masu fama da cutar amosanin jini na ci gaba da kokawa kan mawuyacin halin da suka ce suna ciki ta fuskar wahalar jinya. Ku saurari rahoton wakilinmu Is'haq Khalid.

View Details

Rundunar sojin Najeriya ta sake yin gargadi ga mayakan Boko Haram da su gaggauta mika wuya kafin dakarun sojin kasar su murkushe su. Ku saurari Kanar Sani Usman Kuka Sheka, wanda shi ne Kakakin rundunar Sojin kasa ta Najeriya, inda ya yi wa Yusuf Tijjani karin bayani.

View Details

Wasu shugabannin jami'iyyar adawa ta PDP sun ce sakacin da jam'iyyar ta yi wajen tunkarar matsalar Boko Haram a shekaru 16 da ta shafa tana mulkin kasar, ya taimaka wajen kara ta'azzara matsalar.

View Details

Wasu kungiyoyin farar hula a Najeriya sun bukaci 'yan Majalisar dattawan kasar da su sanya Najeriyar akan gaba a lokacin da suke fara tantance sunayen mutanen da shugaban kasar ya gabatar don nada su ministoci. Ku saurari hirar wakilinmu Yusuf Tijjani da Alhaji Abubakar Tsanni, shugaban kungiyar dake rajin tabbatar da kishin kasa ta 'Think Nigeria First' domin jin karin bayani.

View Details

Rahotani sun bayyana cewa an sake samun fargabar bular cutar ebola a garin Calabar da ke jihar Cross Ribas a kudo maso kudancin Najeriya. Hakan ya biyo bayan wani matashi da aka kai asibiti wanda ya nuna alamun yana dauke da cutar ta ebola wanda daga bisani ya rasu. Ku saurari hirar wakilayarmu, Raliya Zubairu da Farfesa Abdulsalam Nasidi, shugaban cibiyar yaki da cututtuka ta Najeriya domin jin karin bayani

View Details

Rahotani sun bayyana cewa an sake samun fargabar bular cutar ebola a garin Calabar da ke jihar Cross Ribas a kudo maso kudancin Najeriya.

View Details

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci Birtaniya da ta kara kokari wajen tallafawa Najeriya ta fuskar tsaro musamman wajen samar da taimakon kayan yaki da kuma hanyoyin tattara bayanai na tsaro.

Ku saurari hirar wakilinmu Isa Sanusi da Malam Garba Shehu, shi ne babban mataimaki na musamman ga shugaba Buhari ta fuskar yada labarai, domin karin bayani.

View Details

Ku saurari shirin mu na Gatanan gatanan ku.

View Details

Ku saurari shirin namu na Mutattauna, inda aka zanta game da gudunmuwar da matasa za su iya bai wa gwamnati, wanda Mohammed Kabir Mohammed ya gabatar mana.

View Details

Hukumar kwallon kafar duniya Fifa ta dakatar da shugaba da Sakatarenta, wato Sepp Blatter, Jerome Valcke da Michel Platini na tsawon watanni uku. Ku saurari rahoton Mohammed Kabir Mohammed.

View Details

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri a daren Laraba da shugabannin Majalisun dokokin kasar a fadarsa da ke Abuja.

View Details

Rundunar sojin Najeriya ta ce mayakan Boko Haram da dama aka kashe kuma ta rasa sojoji 7 a bata kashin da sojoji suka yi da mayakan kungiyar Boko Haram a Goniri da ke jihar Yobe. Ta kuma ce sojojinta sun kwace makamai da dama da kuma abubuwa masu fashewa kamar yadda zaku ji a cikin rahoton da wakiliyarmu Raliya Zubairu ta hada mana.

View Details

Bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da sunayen mutanen da yake son ya yi aiki da su a matsayin ministoci a gaban majalisar dattawa domin neman amincewarsu . A yanzu kallo ya koma ga majalisar domin ganin yadda tantancewar za ta kaya.

Ku saurari hira wakilinmu Umar Shehu Elleman da Barrister Ibrahim Jalo , mataimakin kakakin babbar jam'iyyar adawa ta PDP domin jin karin bayani.

View Details

Majalisar dattawan Najeriya ta ce za ta gudanar da aikin tantance ministocin da shugaban kasar ya gabatar mata ba tare da nuna son rai ba.

Haka kuma Majalisar ta maida martani dangane da sukar da wasu 'yan kasar ke yi akan furucin da shugaban kasar ya yi cewar shi da kansa ne zai ja ragamar ma'aikatar man fetur ta kasar. Ku saurari hirar wakilinmu Usman Minjibir da Sanata Ali Ndume, shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan Najeriya domin jin karin bayani

View Details

Rahama Sadau ta ce dadewar da Hausawa suka yi suna mu'amala da fina-finan Indiya ya yi tasiri sosai a kan fina-finan Hausan, Ku saurari hirarsu da Nasidi Adamu Yahaya.

View Details

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da ajujuwan tafi da gidanka, domin karatun yaran da ke sansanoni 'yan gudun hijira a Maiduguri. Ku saurari rahoton Haruna Shehu Marabar Jos.

View Details

A yau ne majalisar dattawan Najeriya za ta dawo zamanta inda ake sa ran shugaban majalisar zai bayyana sunayen wadan da ake son nadawa ministoci. Ku saurari hirar Haruna Shehu Tangaza da Senata Aliyu Magatakarda Wamakko kan wannan batu.

View Details

Wasu gidajen rediyo sun yi nasara wajen kirkiro da shirye-shiryen karanta litattafan Hausa, da ke matukar jan ra'ayin masu sauraro. Ku saurari karin bayani wurin Halima Umar Saleh.

View Details

Saudiyya ta sha alwashin hukunta duk wanda aka samu da laifi a turmutsustun da ya faru a Mina ranar Sallah. Ku saurari rahoton da wakilin mu Yusuf Ibrahim Yakasai ya aiko mana.

View Details

Mayakan Boko Haram 80 sun mika wuya ga sojojin Najeriya a garin Bama da ke jihar Borno, cikin su har da kwamandojin kungiyar. Ku saurari karin bayani a hirar da Ibrahim Mijin yawa ya yi da Kanal Sani Usman Kukasheka, mai magana da yawun rundunar sojin kasar.

View Details

Hankulan 'yan Najeriya da dama sun karkata ne kan yadda Majalisar dattawan kasar zata gudanar da tantance ministocin da shugaban kasar ya gabatar. Ku saurari hirar Mohammad Annur Mohammad da Dr Abubakar Kari, malami a jami'ar Abuja kuma mai sharhi kan harkokin siyasa.

View Details

Karin kudin lantarki na tayar wa da talakawan Najeriya hankali. Ku saurari rahoton da wakilinmu Is'haq Khalid ya aiko mana.

View Details

Ana ci gaba da bayyana fargaba dangane da barakar da majalisar dattawan Najeriya take fama da ita. Ku saurari hirar Sanata Habu Ibrahim, daya daga cikin 'yan majalisar dattawan da Usman Minjibir kan wannan batu.

View Details

Hukumar alhazan Najeriya ta ce ya zuwa yanzu mahajjatan kasar 64 ne suka rasa rayukan su, yayin da 71 suka samu raunuka Ku saurari karin bayanin da Alhaji Uba Mana, jami'in yada labarai na hukumar alhazai ta Najeriya ya yi wa Abdullahi Bala Tanko.

View Details

Ku saurari shirin mu na gatanan - gatanan ku, wanda ya tabo kadan daga cikin matsalar ambaliyar ruwa.

View Details

Ku biyo mu ku saurari Muhammad Abba wanda ke gabatar da filin namu na Mutattauna, inda aka zanta kan cin zarafin da ake yi wa yara kanana.

View Details

Magidanta a Zimbabwe, sun samo wata hanya na rataya wa dabbobi wani abu mai kyalli a jelarsu da kuma wuyansu, domin magance matsalar haddura. Ku saurari fassarar rahoton Richard Hamilton.

View Details

Yau ne 'yan majalisar dattawan Nigeria za su koma aiki bayan hutun da suka yi na makonni shida. Ku saurari hirar Yusuf Tijjani da Sanata Shehu Sani dan Majalisar dattawa.

View Details

Bayanai daga Saudiyya na nuna akwai yiwuwar alkaluman yawan mutanen da suka rasa rayukansu su haura wanda aka fitar zuwa yanzu. Ku saurari rahoton Yusuf Ibrahim Yakasai.

View Details

A yau ne tawagar karshe ta ma'aikatan lafiya na Najeriya da suka je kasar Saliyo domin taimaka mata yaki da cutar Ebola suka dawo gida. Ku saurari rahoton Halima Umar Saleh.

View Details

Shugaban Nijar Alhaji Muhamadou Issoufu ya tsige gwamnan jihar Diffa Malam Yakubu Sumana Gawo daga kan mukaminsa. Ku saurari rahoton BARO ARZIKA.

View Details

Fadar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta tabbatar da cewar alkawarin Shugaban Kasar na nan daram na bayyana sunayen ministocinsa a wannan makon. Ku saurari rahoton da Ibrahim Mijinyawa ya hada mana.

View Details

Masana a jami'ar 'Max Planck Institute for Chemistry' sun gano gurbatr yanayi yana sandin mutuwar mutane miliyan daya da dubu dari a kowane shekara a China, wannan gurbatar yanayi kuma ta hada da Najeriya. Ku saurari karin bayanin da Dr. Auwal Umar Gajida, kwararran Likita ne a bangaren kula da lafiyar al'umma a asibitin Malam Aminu Kano dake Kano, ya yi wa Ibrahim Mijinyawa.

View Details

Babbar jam'iyyar adawa ta Nijeriya wato PDP, ta ce akwai yiwuwar ta sauya sunanta. Ku saurari bayanin da Barista Abdullahi Jalo, mataimakin sakataren watsa labarai na jam'iyyar ta PDP na kasa, ya yi wa Is'haq Khalid.

View Details

Rundunar sojin Nigeria ta sake jaddada matsayinta na cewa abinda ta sa a gaba yanzu shi ne murkushe kungiyar Boko Haram baki daya. Kanar Rabe Abubakar shi ne daraktan watsa labarai a rudunar Tsaron Najeriyar, ku saurari hirarsu da Muhammad Annur Muhammad

View Details

Bankin Musulunci ya ce zai kashe kusan dala miliyan 100, watau sama da naira biliyan 19, wajen shigar da darussan karatun zamani a makarantun allo, da isalmiya. Mai martaba sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, ya yi wa Yusuf Yakasai karin bayani, ku saurara.

View Details

Rahotanni daga garin Mungono na Jihar Borno na cewar wani harin kunar bakin wake da wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai ya halaka mutane 32, kuma mutane 29 sun samu rauni. Ku saurari hirar da BBC ta yi da Dan Civilian JTF ko kato da gora na Garin Mungono.

View Details

Dubun dubatar mahajjanta bana daga dukkan sassan duniya sun soma aikin Hajji a yau. Ku saurari hirar Ahmad Abba Abdullahi da editan mu na Abuja Bashir Sa'ad Abdullahi, wanda yanzu haka ke Mina.

View Details

Yanzu haka dai maniya aikin hajjin bana suna cigaba da shiga Mina domin shirye shiryen hawan Arfa. Ku saurari karin bayanin Abdullahi Muktar Mohammed, Shugaban Hukumar alhazan Nigeria.

View Details

Abubakar Shekau, ya fitar da wani sakon murya inda yake yi wa sojojin Nigeriar raddi, toh shin sabbin hare-haren nan na da alaka da furucin nasa? Ku saurari rahoton Muhammad Anur Muhammad.

View Details

A wani hali kasar Burkina Faso ta ke ciki yanzu? Ku saurari hirar Abdulkareem Dayyabu, wani Dan Nijar masanin kimiyyar siyasa kuma malamin jami'a a kasar ta Bourkina Faso, da Usman Minjibir.

View Details

UNICEF ta ce tarzomar Boko Haram cikin watanni biyar da suka gabata, ta raba kananan yara kimanin dubu dari biyar da muhallansu. Ku saurari rahoton da wakilinmu Is'haq Khalid ya aiko mana.

View Details

Jami'an sojin da suka jagoranci juyin mulki a kasar Burkina Faso sun ce sun sako shugaban gwamnatin rikon kwarya, Michel Kafando. Ku saurari rahoton da Mohammed Kabir Mohammed ya hada mana.

View Details

Babbar kotun tarayya a Abuja ta dakatar da yunkurin hukumar kula da da'ar ma'aikata ta Najeriya na gurfanar da shugaban majalisar dattijai, Dr. Bukola Saraki. Ku saurari rahoton da Yakubu Liman ya hada mana.

View Details

Majalisar Koli ta Tattalin Arzikin kasa a Nijeriya ta bayyana cewa kawo yanzu jihohi goma sha takwas ne a kasar suka samu tallafin kudi daga gwamnatin tarayya da nufin warware matsalar basussukan albashin da ya yi masu katutu. Wakilinmu Is'haq Khalid ya duba mana tasirin tallafin gwamnatin tarayyar ga jihohi masu katutun bashi da kuma irin matakan da ya kamata jihohin su dauka domin kada a koma gidan jiya. Ku saurarin rahotansa domin jin karin bayani.

View Details

Hukumar NDLEA mai hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta chafke wasu mutane shidda da su ka kware wajen hadiyar dalar Amirka a cikinsu , a shirin fasa kwarinta zuwa kasashen ketare. Wannan dai shine karon farko da hukumar ta kama wasu da sabon salon fataucin haramtattun kudade inda su ka bullo dashi. Ku saurari rahoton wakilinmu, Umar Shehu Elleman domin jin karin bayani

View Details

Gwamnatin Najeriya ta bayyana sakamakon binciken da ya nuna cewa yara 6 daga cikin kowadanne yara 10 a kasar sun taba fuskantar azabtarwa ko cin zarafi. Ku saurari rahoton da Haruna Shehu Tangaza ya hada mana.

View Details

Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa ta kama mutane 33 da suke samarwa da mayakan Boko Haram kayan abinci. Ku saurari rahoton Ibrahim Mijinyawa.

View Details

Sarkin Makkah ya yi alkawarin biyan diyyar mutanen da suka hada da dangin wadanda suka rasu, da kuma wadanda suka samu raunuka. Alhaji Abdullahi Mukhtari Muhammed shi ne shugaban hukumar aikin Hajjin Najeriya, ku saurari tattaunawar su da Isa Sanusi.

View Details

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty international tana zargin jami'an sojin kasar Kamaru da kuma mayakan Boko Haram da tafka ta'asa kan jama'a fararen hula a kasar. Ku saurari rahoton da Muhammad Babalala ya hado mana.

View Details

Farfesa Attahiru Jega ya ce a shirye yake ya amsa kiran sake yi wa kasarsa aiki idan dai aka bukace shi da yin hakan. Ku saurari hirar Haruna Shehu Tangaza da tsohon shugaban hukumar zaben na Najeriya.

View Details

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kammala ziyarar kwanaki uku da ya kai a kasar Faransa. Malam Garba Shehu, kakakin shugaba Buharin ya yi mana bayanin abubuwan da shugaban zai yi a rana ta karshe ta ziyarar tasa?

View Details

Gwamnatin Najeriya ta fara wani yunkuri na sauya tunanin mayakan kungiyar Boko Haram da ake tsare a gidajen yari daban daban, a matsayin wata hanyar yakar ta'addanci da tsattsauran ra'ayi ta ruwan sanyi.

View Details

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaida wa BBC cewa sun yi wa mutanen da aka bai wa kwangilar samar da wutar lantarki barazana cewa idan suka ci gaba da kin samar da wutar, to lalle za a bankado cuwa-cuwar da suka yi domin gudanar da bincike, shi ya sa yanzu ake samun wutar sosai.

View Details

Hukumar sojin Najeriya ta bayyana maida sojoji fiye da dubu 3 da aka sallama daga aikin sakamakon zargin aikata laifuka daban daban da suka shafi yakin da rundunar ke yi da kungiyar Boko Haram. Ku saurari bayanin Malam Hussaini Mungono, masanin harkokin tsaro ne a Najeriya a kan wanna batu.

View Details

Wata kungiya mai suna CEDRA ta gudanar da taron maneman labarai domin duba salon mulkin gwamnatin jihar karkashin jagorancin Mal Nasiru El Rufai. Ku saurari rahoton wakilin mu Nurah Mohammed Ringim.

View Details

Rahotanni a hukuman ce na nuna cewa an samun ingantuwar wutan lantarki daga megawati 2,500 zuwa megawati dubu 5,000, cikin watanni uku. Ku saurari rahoton wakilinmu Umar Shehu Elleman.

View Details

Rundunar sojojin Najeriya ta sake jaddada cewar dakarun ta za su murkushe mayakan Boko Haram cikin watanni uku. Ku saurari hirar da Babban Hafsan Sojin Kasa na Nigeria Manjo-Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi da BBC.

View Details

Rundunar sojojin Najeriya ta sake jaddada cewar dakarun ta za su murkushe mayakan Boko Haram cikin watanni uku, kamar yadda Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya ba su umarni. Ku saurari hirar da Babban Hafsan Sojin Kasa na Nigeria Manjo-Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi da BBC.

View Details

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da kuma mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo sun bayyana kadarorin da suka mallaka. Ku saurari rahoton Yakubu Liman kan wannan batu.

View Details

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC a Najeriya, ta soma bincike a kan wasu tsoffin gwamnonin jihohin kasar su hudu, wadanda ake zarginsu da almundahana da dukiyar gwamnati. Ku saurari rahoton da Ummulkhair Ibrahim ta hado mana.

View Details

Cibiyar McArthur Foundation a Nigeria ta ce wani bincike da ta gudanar ya nuna cewa, ana samun karuwar mutanen da ke amfani da kalaman nuna kiyayya ko na batanci a shafukan sada zumunta na zamani. Ku saurari rahoton da Halima Umar Saleh ta hado mana.

View Details

Jam'iyyar APC mai mulki ta ce an samu ci gaba ta fuskar magance wasu daga cikin matsalolin kasar da ta yi alkawarin shawo kan su da zarar ta karbi ragamar shugabancin kasar. Ku saurari hirar Senata Lawal Shu'aibu, mataimakin shugaban jam'iyar ta kasa mai kula da yankin arewacin Najeriya, da Abdou Halilou.

View Details

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kwace iko da yankin Gambourou-Ngala daga hannun `yan Kungiyar Boko-Haram a jiya Talata. Ku saurari bayanin Kanar Sani Usman Kuka-Sheka shi ne Kakakin rundunar da kuma ra'ayoyin wasu 'yan asalin garin Gamborou Ngala da rikicin Boko Haram ya tilastawa kaura.

View Details

Tsohon dan wasan tawagar Nigeria, Segun Odegbami ya bayyana aniyarsa ta son zamowa shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya. Ku saurari filin wasanni da Muhammada Abdu Mamman Skipper.

View Details

Mu tattauna, shiri ne da ke bincikowa da kuma bayyana gaskiyar al'amari. Ku saurari shirin namu wanda Muhammad Kabir Muhammad ya gabatar, inda aka tabo batun illar tallace-tallacen 'yan mata a al'umma. Menene ra'ayin ku ga wannan batu?

View Details

Ku saurari shirin mu na gata-nan gata-nan ku, inda ya tabo batun Illar tallace-tallacen 'yan mata a tsakanin al'umma.

View Details

An rantsar da Dr Akinwumi Adesina,a matsayin shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika - AFDB, na 8 a Abidjan na kasar Ivory Coast. Ku saurari tattaunawar da aka yi da Farfesa Dan-Bala Danju, shugaban Bankin raya aikin Noma na Najeriya, yana kuma daya daga cikin mutanen da suka shedi rantsar da sabon Shugaban Bankin raya kasashen Afrikan.

View Details

An sanya hannu kan wata yarjejeniya tsakanin kungiyar masu rini a Kano, da cibiyar ciniki da masana'antu ta kasar China. Ku saurari rahoton Yusuf Ibrahim Yakasai.

View Details

A makon nan ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke cika kwanaki 100 kan kujerar shugabancin kasar. Ko yaya kamun ludayin wanna sabon gwamnatin? Ku saurari rahoton Haruna Shehu Tangaza da kuma tattaunawar Nasidi Adamu Yahaya da Dr Bello Mohammed Halliru shugaban kwamitin amintattu na jam'iyar adawa ta PDP.

View Details

Batun cin hanci da rashawa ne dai ake ganin ya dade yana yi wa Najeriya illa. Ku saurari tattaunawar da shugaban hukumar ta EFCC Ibrahim Lamorde, ya yi da Abdullahi Kaura Abubakar.

View Details

A ci gaba da kawo maku rahotanni na musamman kan cikar shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari kwanaki dari a kan karagar mulki, wakilinmu Is'haq Khalid ya duba mana yadda sabuwar gwamnatin ke tunkarar yaki da Boko Haram kawo yanzu. Ku saurari rahoton sa.

View Details

Mahaifiyar daya daga cikin dalibai 'yan Najeriya da aka kama a Indiya bisa zargin cewa za su shiga kungiyar nan mai da'awar kafa daular musulunci ISIS ta musunta cewa danta yana da niyyar shiga kungiyar, tana mai cewa danta mutumin kirki ne. Ku saurari abin da ta shaida wa wakilinmu na Kano, Yusuf Ibrahim Yakasai:

View Details

Ana samun karuwar masu harbuwa da cutar MERS mai alaka da numfashi a kasar Saudiyya. Abdullahi Tanko Bala ya tuntubi Alhaji Uba Mana, kakakin hukumar Alhazzai ta Najeriya a kan yadda suka ji da yaduwar wannan cuta. Ku saurari hirar su a nan.

View Details

Mutane 500 sun kife a tekun Libya a kusa da birnin Zuwara. Ku saurari rahoton da Bashir Sa'ad Abdullahi ya hada mana.

View Details

Jama'ar shiyyar kudu maso gabashin Najeriya ta al'ummar Ibo na ci gaba da bayyana fargaba tare da damuwa, cewa da alamu za a mayar da shiyyarsu saniyar ware a nade-naden mukaman da shugaban kasar, Muhammadu Buhari yake yi a gwamnatinsa. Ku saurari bayanin da Mista Kalu Eziyi, wani dan asalin jihar Abiya mai sharhi kan al'amura, ya yi wa wakilinmu AbdusSalam Ibrahim Ahmed.

View Details

A Nigeria bisa ga dukkan alamu allura na neman tono galma a binciken da wani kwamitin Majalisar dattawa ya fara akan hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC. Ku saurari hirar Mansur Liman da tsohon Sanata, Alhaji Abubakar Sodangi game da wannan batu.

View Details

Hukumar nan ta kayyade albashin ma'aikatan gwamnati RMAC ta ce ta soma aikin zaftare yawan kudaden da ake biyan Shugaban Kasa da Sanatoci da 'yan majalisar wakilai da Gwamnoni da kuma sauran jami'an gwamnati. Ku saurari hirar Aliyu Abdullahi Tanko ya da Hon.Jagaba Adams Jagaba, kan wanna batun.

View Details

Wasu dakarun sojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram, sun bayyana cewa, sauyin da aka samu a yanayin makaman da suke aiki da su bai taka kara ya karya ba, tun lokacin da suka yi korafi ga gwamnatin da ta gabata. Dangane da wannan batu, ku saurari martanin da mai magana da yawun sojin kasa na Najeriya Kanal Sani Usman Kuka sheka, ya mayar.

View Details

Shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa EFCC, Ibrahim Lamorde ya musanta zargin da 'yan majalisar dattawan kasar ke yi masa. Ku saurari rahoton Haruna Shehu Tangaza wanda ya halarci zaman majalisar da kuma ku ji ta bakin Shugaban EFCC Ibrahim Lamurde.

View Details

Wakilinmu Umar Shehu Elleman ya tambayi Alhaji Aliko Dangote, hamshakin attajirin nan a Africa a wajen sa hannu a kan wata yarjejeniya tare da kasashen Afrika 9, kan kafa kamfanonin siminti, ko yaya faduwar hannayen jari a China ta shafi harkokin kasuwancinsa ? Ku saurara a nan,

View Details

Batun kiwon lafiya shi ne ya fi jan hankalin jihohi da kananan hukumomin Najeriya a shekarun da aka kwashe ana aiwata shirin muradun karni na kawo ci gaba wato MDG. Dr. Abdullahi Umar Ganduje shi ne gwamnan jihar kano wadda tafi yawan jama'a a kasar, kuma a lokacin ziyarar da babban sakataren Majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon a Nigeria, sun yi hirar da Haruna Shehu Tangaza.

View Details

A Najeriya, wa su gwamnoni a yankin arewa maso yammacin kasar sun sha alwashin ci gaba da hada kai a tsakanin su don ganin an magance matsalar sace sacen shanu a jihohin su. Ku saurari hirar Nurah Mohammed Ringim da gwamnan jihar Katsina Alh Aminu Bello Masari.

View Details

Shugaban Faransa Fracois Hollande, ya yi tayin shirya wani taro na kasashen duniya domin tattaunawa kan yadda za a yaki kungiyar Boko Haram a Nigeria. Ku saurari rahoton Nasidi Adamu Yahya, kan wanna batu.

View Details

Masu mu'amala da shafin sada zumunta na Twitter sun yi tsokaci sosai a kan wata sabuwar wakar da jarumin fina finan Hausa, Sani Danja ke shirin kaddamarwa. Mun dan gutsuro muku wakar tasa, sannan ku saurari hirarsa da abokiyar aikin mu Badariyya Tijjani Kalarawi.

View Details

A Nigeria, hukumar tsaro ta farin kaya, DSS ta ce ta gurfanar da tsohon mai ba da shawara ta fuskar tsaron kasa, Kanar Sambo Dasuki mai ritaya a gaban kotu, bisa zargin sa da mallakar bindigogi ba bisa ka'ida ba. Ku saurari rahoton da Ibrahim Mijinyawa ya hada mana.

View Details

Shirin Gatanan-Gatananku wanda ya tabo matsalolin da mazauna gidajen haya ke fuskanta. Wadanne irin matsaloli ke tattare da zaman gidan haya? Yaya kuke ganin za a inganta batun zaman gidan haya?

View Details

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja. Ku saurari rahoton da Haruna Shehu Tangaza ya aiko mana.

View Details

A China, masu hada-hadar hannun-jari sun wayi gari da mummunar asarar da ba su taba yin irin ta ba cikin shekaru takwas din da suka wuce. Ku saurari fassarar rahoton Celia Hatton.

View Details

Rahotanni daga arewa maso gabashin Nigeria na cewa, direbobin manyan motoci sun tsare babban haryar da ta hada jihohin Adamawa da Taraba domin nuna fushinsu game da kisan da aka yi wa wani direba dan uwansu. Ku saurari rahoton da Badariyya Tijjani Kalarawi, a kan wannan batu.

View Details

Rahotani daga Syria sun ce mayakan kungiyar IS dake ikirarin jihadi sun lalata wani wurin ibada mai dimbin tarihi a garin Palmyra. Ku saurari rahoton da Raliya Zubairu ta hada mana.

View Details

Masu bincike a jami'ar London sun ce aiki na tsawon sa'oi ga alamu na da alaka da karuwar hatsarin kamuwa da cutar nan ta shanyewar bangaren jiki wato stroke a Turance. Dangane da wannan bincike ne Ibrahim Mijinyawa ya tuntubi Dr. Bashir Mijinyawa, wani Likita da ke Abuja domin jin yadda suke kallon binciken.

View Details

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon zai gana da shugaba Muhammadu Buhari a ranar Litinin. Ku saurari hirar Haruna Shehu Tangaza da gwamnan jihar Bauchi Barista Mohammad Abubakar kan wannan batu.

View Details

Ma'aikatar harkokin waje ta Najeriya ta ce ta nemi gwamnatin kasar India akan ta ba su damar ganawa da wasu matasa biyu da aka kama wadanda rahotani ke cewa 'yan Najeriya ne . Rahotanin sun ce jamian tsaro na India sun kama matasan ne wadanda dalibai ne da ke karatu a kasar lokacin da ake zargi suna kokarin tsalkawa kasar Pakistan domin shiga cikin kungiyar IS . Ku saurari rahoton wakiliyarmu, Raliya Zubairu domin jin karin bayani.

View Details

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya yi gargadin cewar ba zai yarda da karbar kudi daga hannun marasa aikin yi ba yayin daukar 'yan sanda aiki.

Shugaban ya yi wannan furuci ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Mr Femi Adesina.

Sanarwar ta ce Shugaban Najeriyar ya bayyana haka ne a wajen wata ganawa da ya yi jiya tare da jami'an ma'aikatar kula da harkokin 'yan sandan kasar da kuma hukumar 'yan sandan a Abuja.

Ku saurari rahotan da wakilinmu Ibrahim Mijinyawa ya hada mana domin karin bayani.

View Details

A jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya, an samu wasu matasa hudu sun yi wata yarinya'yar shekaru 14 fyade bayan sun bata wani abu mai gusar da hankali a unguwar Gwiwa Lowcost da ke babban birnin jihar. Ku saurari hirar Haruna Shehu Tangaza da shugaban hukumar kare hakkin bil adama ta jihar Sakkwato Alhaji Kabiru Umar Dodo.

View Details

Shin fina-finan Hausa suna karawa masu kallo ilimi, ko kuwa maimakon gyara tarbiyya da aikewa da sakonni na gari, masu yin fina-finan na taka rawa wajen bata al'adun bahaushe ne? Ku saurari hirar Nasidi Adamu Yahaya da wani tauraron fina-inan Hausa watau Alhaji Abba Almustapha, wanda aka fi sani da Abba Ruda.

View Details

Hukumomin Lebanon ne dai suka kama Ahmed Al'asir a filin tashin jirgin saman Bierut lokacin da yake shirin zuwa Najeriya da Fasfon Falasdinu na Jabu. Ku saurari bayanin da Babban Sakatare a ma'aikatar harkokin wajen Najeriyar Mr. Bulus Lolo ya yi wa BBC da kuma tsokaci da Husseini Munguno ya yi akan batun.

View Details

A Najeriya ana ci gaba da tsokaci akan sauye-sauyen da ake yi wa kamfanin mai na kasar wato NNPC.

Shi dai sabon shugaban kamfanin mai na NNPC Emmanuel Ibe Ikachukwu ya yi wasu sauye sauye ciki har da wasu sabbin nade naden a wani mataki na maido da martabar kamfanin.

Sai dai masana da kuma wasu maaikatan kamfanin sun bayana ra'ayoyi mababanta akan sauye-sauyen kamar yadda zaku ji a cikin rahoton da Raliya Zubairu ta hada mana.

View Details

Wasu rahotanni sun ce akalla mutune 60 ne suka rasu a wani harin da ake zargin `yan kungiyar Boko Haram da kaiwa a garin Kukuwa a jihar Yobe da ke arewa-maso-gabashin Najeriya.

Wasu da suka fito daga garin sun shaidawa BBC cewa mutanen sun gamu da ajalin su ne sakamakon harbinsu da bindiga, yayin da wasu kuma ruwa ya ci su lokacin da suka fada Rafi a kokarin su na tserewa.

Ku saurari rahoton wakilinmu, Abdullahi Kaura Abubakar domin jin karin bayani.

View Details

Wasu rahotanni sun ce akalla mutune 60 ne suka rasu a wani harin da ake zargin `yan kungiyar Boko Haram da kaiwa a garin Kukuwa a jihar Yobe da ke arewa-maso-gabashin Najeriya.

Wasu da suka fito daga garin sun shaidawa BBC cewa mutanen sun gamu da ajalin su ne sakamakon harbinsu da bindiga, yayin da wasu kuma ruwa ya ci su lokacin da suka fada Rafi a kokarin su na tserewa.

Ku saurari rahoton wikilinmu, Abdullahi Kaura Abubakar domin jin karin bayani.

View Details

A Nigeria, wasu 'yan Majalisar wakilan kasar sun musanta rahotannin dake cewa daukacin 'yan Majalisar dattawa data wakilai sun kashe fiye da Naira biliyan goma sha biyu cikin watanni biyu da fara aiki a Majalisar.

Ku saurari hirar wakilinmu, Yusuf Tijjani da Alhassan Ado Doguwa, mai tsawatar wa a Majalisar wakilan Nigeria domin jin karin bayani.

View Details

Ku biyo mu a shirin na mu na 'Mu tattauna', shirin da ke bincikowa da kuma bayyana gaskiyar al'amari na zamantakewar 'yan kasa. Ku saurari Muhammad Abba inda ya ke gabatar muku da shiri a kan matakan da ya kamata a dauka domin kare hakokkin fasinjoji na ababan hawa.

View Details

Ku saurari shirin mu na Gata-nan-gata-nan ku, inda ya maida hankali a kan biyan haraji. Shin jama'a, kuna biyan haraji kuwa?

View Details

Rundunar sojin Nigeria ta ce duk da faifai da ke ikirarin cewa jagoran kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau yana raye bai mutu ba, babban abin da ta sa a gaba shi ne na ganin ta murkushe kungiyar nan da 'yan watanni. Kanar Sani Usman Kukah Sheka, shi ne kakakin rundunar sojin kasa ta Nigeria, ku saurari hirar su da Yusuf Tijjani.

View Details

Kungiyar Boko-Haram ta fitar da wani faifai da ke ikirarin cewa jagoranta Abubakar Shekau yana nan raye bai mutu ba. Badariyya Tijjani Kalarawi ta saurarin faifan, ga kuma rahoton da ta hada mana.

View Details

ahotanni daga jihar Zamfara sun ce akalla mutun daya ya nutse bayan gadar nan da ke kan babban titin Sakkwato zuwa Gusau da ta ruzga a farkon makonnan ta sake ruftawa. Ku saurari karin bayanin da Hon. Abdulmalik Zubairu Bungudu, dan majalisar da ke wakiltar yankin da lamarin ya faru a majalisar dokokin kasar, ya yi wa Haruna Shehu Tangaza.

View Details

An gudanar da jana'izar babban basaraken kabilar Yarabawa, Ooni na Ife da ke Kudu maso yammacin Nigeria. Aliyu Abdullahi Tanko, ya tuntubi Alhaji Abubakar Madagali, Sarkin Hausawan Ile Ife domin jin karin bayani. Ku saurara a nan,

View Details

Wasu 'yan hamayya a jihar Kano sun soki gwamnatin jihar kan matakin da ta dauka na kashe Naira Miliyan 180 dan gyaran gidan mataimakin gwamnan jihar. Ku saurari rahoton da Yusuf Ibrahim Yakasai ya aiko mana.

View Details

Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci manyan hafsoshin dakarun kasar su kawo karshen kungiyar Boko Haram a cikin watanni uku. Ku saurari bayanin da Hussani Munguno, wani mai yin sharhi akan al'amuran da suka shafi Tsaro a Najeriya ya yi wa Nasidi Adamu Yahya.

View Details

Mahukuntan kasar China sun ce za a yi duk abubuwan da suka kamata don taimakawa wadanda mummunar fashewar wani abu da ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 50, a yankunan masana'antu dake tashar jiragen ruwan a birnin Tianjin. Ku saurari rahoton da Bashir Sa'ad Abdullahi ya hada mana.

View Details

Amurka ta yanke wa wani dan Najeriya hukuncin daurin shekaru 22 a gidan yari a bisa laifin goyon bayan kungiyar Al-Qaeda. Ku saurari rahoton da Bahsir Sa'ad Abdullahi ya aiko mana.

View Details

Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci manyan hafsoshin dakarun kasar su kawo karshen kungiyar Boko Haram a cikin watanni uku. Ku saurari rahoton da Ibrahim Mijinyawa ya aiko mana.

View Details

Wata dambarwa ta kunno kai bayan da gwamnan jihar na yanzu, Mista Simon Lalong, ya bai wa tsohon gwamnan jihar, Dokta Jonah Jang, wa'adin makwanni biyu, ya mayar wa gwamnati kudade sama da naira miliyan dubu dari biyu da ashirin da ake zargin an sace a lokacin mulkinsa na shekaru takwas.Ku saurari rahoton da wakilinmu Is'haq Khalid ya aiko mana.

View Details

A Najeriya wasu dalibai na kwalejojin ilimi na cewa ba su amince da soke takardar shaidar ilimi ta NCE a makarantun su ba, duk kuwa da cewa an ayyana mayar da makarantun zuwa jami'o'i. Ku saurari rahoton wakilin mu Nurah Mohammed Ringim.

View Details

Amurka ta yi Alla wadai da harin bam din da aka kai a wata kasuwar sayar da wayoyin hannu dake garin Sabon Gari kusa da Damboa a jihar Borno a jiya. Ku saurari rahoton da Raliya Zubairu ta hado mana.

View Details

Sabon Babban Sakatare Janar na Mujami'ar Anglican ya yi kakkausar suka akan shugabannin addinin Kirista a Nigeria, wadanda ya dorawa alhaki na kasa tattaunawa tare da Musulman kasar akan barazanar da kungiyar Boko Haram ke yiwa kasar. Ku saurari fassarar rahoton John McManus, da kuma martani da Reverend Dr Sunday Ibrahim, sakatare Janar na Kungiyar CAN ta reshen Jihar Kaduna.

View Details

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce nan da wasu 'yan makonni za a soma shari'ar mutanen da suka sace dukiyar kasa. Ku saurari hirar Ibrahim Mijinyawa da Malam Garba Shehu, mataimaki na musammman ga shugaban kasa kan yada labarai.

View Details

Hukumar agajin gaggawa ta kasa a Nigeria NEMA ta ce mutane 28 ne suka mutu wasu arba'in da hudu suka jikkata bayan fashewar wani bam a wata kasuwar sayar da wayoyin hannu dake garin Sabon Gari kusa da Damboa a jihar Borno. Ku saurari tattaunawar da Ahmed Abba Abdullahi ya yi da Alhaji Muhammadu Kanar, shugaban hukumar ta NEMA a shiyyar Arewa maso gabas.

View Details

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin kasar ba zata dauki dawainiyar tura tawagar gwamnatin tarayya ta musamman zuwa aikin Hajjin bana ba. Ku saurari hirar Abdullahi Tanko Bala da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, shugaban hukumar Hizbah na jihar Kano.

View Details

Hukumomin tsaro a birnin Accra a kasar Ghana sun ce sun cafke wani mutun da suke zargi da cunna wutar da ta haddasa gobarar da ta hallaka mutane sama da dari a wata tashan man petro a bala'in ambaliyar ruwa da gobarar da suka abka ma birnin na Accra a ranan 3 ga watan Yunin wannan shekarar. Ku saurari rahoton iddi Ali.

View Details

Ku saurari shirin namu na gata nana-gata nan ku....

View Details

Ku saurari shirin mu na 'Mu tattauna'... Inda Muhammad Abba zai tattauna da Alhaji Imrana Wada Nas, shugaban kungiyar cigaban matasan arewa, da kuma Aisha Larai Musa, shugabar sashen wayer da al'umma da kuma tarbiyyantarwa ta hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati.

View Details

Hukumar shige ta fice ta Najeriya ta ce a cikin watanni 15 da suka wuce, ta hana matasa sama da dubu ashirin da uku barin kasar, bisa fargabar za su iya aikata ta'adanci ko karuwanci da kuma sauran ayyukan ashsha a kasashen waje. Ku saurari rahoton da Raliya Zubairu ta hada mana.

View Details

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada wani kwamitin da zai ba shi shawara kan yadda zai yaki cin hanci da rashawa. Farfesa Sadik Isa Radda shaihin malami a fannin nazarin miyagun laifukka a jami'ar Bayero da ke Kano na daya daga cikin mambobin wannan kwamiti, ku saurari hirarsa da Ibrahim Mijinyawa.

View Details

A Najeriya, masana tattalin arziki na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu a kan umurnin da Shugaban kasar ya bai wa ma'aikatun gwamnatin Tarayya cewa su dinga sanya kudaden shigarsu cikin wani baitulmali na bai-daya.

Ku saurari hirar wakilinmu Ibrahim Isa da Nazifi Darma, masanin tattalin arziki, domin jin karin bayani.

View Details

Dazu a Kano kungiyar ma'aikatan sabuwar jami'ar ilimi ta tarayya dake kano da aka daga darajar ta a farkon bana suka yi wata zanga zangar lumana dan nuna adawa da wani yunkuri da suka ce gwamnatin Nigeria na yi na mayar da jami'o'in tsohon matasayin su na kwalejojin ilimi. Ma'ailkatan da suka hadar da malaman jami'ar da kuma manyan ma'aikatan jami'ar sun ce matakin tamkar maida hannun agogo baya ne a ce an mayar da makarantun matsayin su na da. Ku saurari hirar wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai da Shugaban kungiyar malaman jami'ar Dr Abubabakar Sadik Haruna domin karin bayani.

View Details

Fadar shugaban Nigeria ta tabbatar da cewa wasu tsofaffin shugaban kasar biyu sun kaiwa shugaba Muhammadu Buhari ziyara a fadar gwamnatin kasar.

Rahotanni sun ce a karshen makon daya gabata ne dai tsohon shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari, yayin da shi ma tsohon shugaba Chief Olusegun Obasanjo, rahotanni ya ziyarci shugaba Buharin a ranar juma'ar data gabata.

To shin ko me ne makasudin wannan ziyarar na tsofaffin shugabannin? Ku sauri hirar wakilinmu Yakubu Liman da Malam Garba Shehu mai magana da yawun Shugaban Najeriya domin jin karin bayani.

View Details

Fadar shugaban Nigeria ta tabbatar da cewa wasu tsofaffin shugabannin kasar biyu sun kaiwa shugaba Muhammadu Buhari ziyara a fadar gwamnatin kasar.

Rahotanni sun ce a karshen makon daya gabata ne dai tsohon shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari, yayin da shi ma tsohon shugaba Chief Olusegun Obasanjo, Rhotanni suka ce ya ziyarci shugaba Buharin a ranar juma'ar data gabata.

To shin ko me ne ne makasudin wannan ziyarar na tsofaffin shugabannin? Ku saurari hirar wakilinmu, Yakubu Liman da Malam Garba Shehu mai magana da yawun Shugaban Najeriya domin jin karin bayani.

View Details

Daruruwan matafiya da ababen hawansu sun rasa na yi a kan babban titin da ya hada jihar Zamfara da makwabtan jihohin Sakkwato da Kebbi sakamako ruftawar wata gada a kan wannan titin. Gadar, wadda aka fi sani da gadar Danmarke ta auka ne jiya bayan da aka kwashe wasu sa'o'i ana tafka ruwan sama.

View Details

Rahotanni daga jahar Yobe da ke arewa maso gabshin kasar na cewa wasu mahara akan babura sun kashe mutane tara. Ku saurari rahoton da Abdou Halilou ya aiko mana.

View Details

Gwamnatin shugaban Ghanan Draamani Mahama na fama da yaje-yajen aikin malaman jami'un Ghana, da ke neman a biya musu wasu bukatu. Ku saurari hirar Bilkisu Babangida da Malam Abbas Umar Mohammed, Malami a jami'ar Accra game da yajin aikin.

View Details

A ci gaba da kawo maku rahotanni kan salon suturun Afirka, wakilinmu a Enugu, AbdusSalam Ibrahim Ahmed ya jiwo mana ta bakin wasu 'yan kabilar Ibo na yankin kudu maso gabashin Najeriya, game da yadda kowanne yake kallon abin da salon suturar mutanen nahiyar Afirka yake nufi.

View Details

Wasu alkalumma daga ma'aikatar kula da hakar ma'adinai ta Najeriya sun nuna cewa kusan kashi 90% na aikace-aikace hakar ma'adinai a kasar ana yinsu ne a gargajiyance.Ku saurari rahoton Haruna Shehu Tangaza.

View Details

A Nigeria an yi nunin wani bangare na wani sabon fim din Hausa mai suna Gwaska, wanda shahararren jarumin nan Adam Zango ya jagoranta. Ku saurari rahoton da wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai ya aiko mana.

View Details

Wani dan kunar bakin wake ya tada bam a wani masallaci da ke yankin Aseer na kasar Saudiya. Abdullahi Tanko Bala ya tuntubi Malam Muhammad Kaddam Sidq Isa mai sharhi kan al'amuran yau da kullum wanda ke zaune a Dubai yadda suke fassara wadannan karuwar hare hare na kunar bakin wake a Saudiyya. Ku saurara a nan,

View Details

Masu fafutuka a yankin Ogoni na Naija Delta na Najeriya na ci gaba da mayar da martani game da matakin da Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya dauka, na kafa kwamitoci da za su yi aikin share man da ya malala a yankin na Ogoni. Ku saurari rahoton da Bashir Sa'ad Abdullahi ya hado mana.

View Details

NEMA ta gargadi al'ummomin da ke zaune a kusa da kogin Benue da su tashi domin akwai yiwuwar samun ambaliyar ruwa daga nan zuwa watan Nuwamba. Ku saurai hirar Abdullahi Abubakar Kaura da Alhaji Muhammad Sani Sidi shugaban hukumar agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, da kuma rahotn da wakinlinmu Nura Mohammed Ringim ya hada mana.

View Details

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya wato NEMA, ta gargadi al'ummomin da ke zaune a kusa da kogin Benue da su tashi domin akwai yiwuwar samun ambaliyar ruwa daga nan zuwa watan Nuwamba. kU SAURARI HIRAR aBDULLAHI aBUBAKAR kAURA DA Alhaji Muhammad Sani Sidi shugaban hukumar agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, da kuma rahoton da wakilinmu Nurah Mohammed Ringim ya hada mana.

View Details

Kamar dai yadda kuka ji galibi 'yan gudun hijirar da gwamnatin Kamaru ta dawo dasu Nigeria 'yan asalin jihar Borno ne. Ku saurari hirar halin da wasu 'yan gudun hijirar ke ciki, da kuma tanadin da gwamnatin su ta yi masu.

View Details

Wani dan kwamitin gudanarwar babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ya zargi gwamnatin jam'iyyar APC da hannu a rikicin da jam'iyyar ta samu kanta a ciki tsakaninta da ma'aikatanta. Ku saurari rahoton da Haruna Shehu Tangaza ya hada mana.

View Details

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, ta ce 'yan kasar kusan su 12,000 sun fara isowa gida daga iyakar jamhuriyar Kamaru bayan da aka ba su umurnin su bar kasar. Ku saurari hirar Abdullahi Tanko Bala da Alhaji Muhammad Kanar, Jami'in hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA, mai kula da shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

View Details

Wani bincike da aka yi a kasar China ya nuna cewa cin abinci mai yaji, musamman danyen borkono, zai iya taimakawa mutane su yi tsawon rai. Ku saurari rahoton Raliya Zubairu wacce ta jiyo ra'ayoyin wasu yan Najeriya masu son cin yaji.

View Details

Mutattauna, shiri ne da ke bincikowa da kuma bayyana gaskiyar al'amura akan jagoranci, wakilci, adalci, 'yanci, da kuma hakkokin 'yan kasa da kuma zamantakewa da cigaban al'umma. Ku saurari Muhammad Kabir Muhammad, wanda ya gabatar da filin na mu, inda aka tattauna akan cin hanci tsakanin al'umma.

View Details

Yanzu kuma bari mu gabatar da filin mu na Gatanan gatanan ku.

View Details

Wakilinmu Is'haq Khalid ya duba mana yadda mata masu shayarwa ke hada aiki da rainon jarirai, ku saurari rahoton da ya aiko mana.

View Details

Rashin jituwa a jam'iyyar PDP ya kunno kai sakamakon wani shiri da Shugabanin suka fito da shi na rage ma'aikatan da kashi 50 da kuma zaftare albashinsu. Haruna Shehu Tangaza ya yi mana nazari kan wannan batu, ku saurari rahoton sa

View Details

Gwamnatin Jahar Kaduna ta ce daga yau laraba ne zata fara karbe duk wasu Filaye na makarantu da asibitoci wadanda ta ce an baiwa wasu a jahar ba bisa ka'ida ba. Ku saurari rahoton wakilin mu Nurah Mohammed Ringim.

View Details

Rahotanni daga jihar Yobe a Nigeria na cewa ruwan saman da aka yi mai karfin gaske a daren jiya ya haddasa ambaliya da rushewar gidaje masu dama , da kuma malale shaguna a garin Ganjarma. Ahmad Abba Abdullahi ya tattauna da wani da ya ziyarci garin na Ganjarma, da kuma Alhaji Abdullahi Bego, kakakin gwamna Ibrahim Geidam na jihar Yobe, ku saurari hirarsu a nan,

View Details

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya sanar da nadin Dr Emmanuel Ibe Kachikwu a matsayin sabon shugaban kamfanin mai na kasa NNPC. Ku saurari rahoton Halima Umar Saleh.

View Details

Amurka ta ce za ta sassauta dokar Leahy da ta kakaba wa Najeriya na kin sayar mata da makamai. Raliya Zubairu ta halarci taron, ku saurari rahoton da ta hado mana.

View Details

A ranar Talata ne makon ranar shayar da nonon uwa na duniya yake farawa. Dakta Mariya Muktar Yola, likitar yara ce a babban asibitin kasa da ke Abuja, ta kuma yi karin haske kan alfanun shayar da jarirai nonon uwa.

View Details

Manoma a jihar Kano dake arewacin Nigeria sun koka da rashin samun takin noman zamani dan amfani da shi a gonakin su. Yusuf Ibrahim Yakasai ya aiko mana da karin bayani a cikin wannan rahoto.

View Details

Wakilin BBC Ibrahim Isa, ya tuntubi Malam Hussaini Munguno, mai sharhi a kan harkokin tsaro don jin yadda yake kallon rashin fitowar shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, a bidiyo biyu da kungiyar ta fitar a baya-bayan nan.

View Details

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta koka da matsanancin halin da musulmi ke ciki a wasu sassa na yammacin Jamhuriyar tsakiyar Afrika na rashin samun sukunin gudanar da addininsu yadda ya kamata. Ku saurari rahoton da wakilin mu Mohammed Babalala ya aiko mana.

View Details

Hukumomi a Burundi sun yi kiran kwantar da hankula bayan da wasu yan bindiga sanye da kakin soji suka harbe wani babban janar din soji a jiya Lahadi. Ku saurari rahoton da Badariyya Tijjani Kalarawi ta hada mana.

View Details

Wasu daga cikin sojojin Najeriya da kotun soji ta kora daga aiki saboda samun su da laifin gudu daga fagen daga sun fara mai da martani dangane da matakin da mahukuntan kasar suka dauka na sake nazarin wasu sharaoin da ke gaban kotunan sojin. Ku saurari hirarar da Ibrahim Isa ya yi da wani sojan da aka kora bisa zargin gudu daga fagen daga.

View Details

A cigaba da ganawa da jama'a a matsayin daya daga cikin alkawururrukan da gwamnan jahar Kaduna Mal Nasiru El Rufai ya dauka a lokacin yakin neman zabe, gwamnatin jahar ta gudanar da taron zaure na tattaunawa da jama'a. Ku saurari rahoton wakilin mu Nurah Mohammed Ringim.

View Details

Jami'an tsaro a kasar Kamaru sun ce sun kama wasu mutane uku da ake zargin 'yan Boko Haram ne da wasu ababan fashewa a birnin Maroua. Ku saurari rahoton da Muhamman Babalala ya aiko mana.

View Details

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar tarwatsa sansanoni takwas na 'yan ta'adda a wani farmaki da suka kaddamar ranar Lahadi. Ku saurari karin bayanin da Kanal Usman Sani Kukasheka ya yi wa Ibrahim Mijinyawa.

View Details

A yau ne Manjo-Janar Iliya Abba, ya karbi ragamar jagorancin sabuwar rundunar hadin gwiwa ta kasa-da-kasa mai yaki da kungiyar Boko Haram watau MNJTF a takaice. Ku saurari rahoton da Haruna Shehu Tangaza ya hada mana.

View Details

Gwamatin Chadi ta dawo da dokar hukuncin kisa da ta soke shi watanni shida da suka wuce. Abdullahi Tanko Bala ya tuntubi wani mazaunin Chadin wanda ya bukaci a sakaya sunansa, domin jin yadda jama'a suka karbi wannan sabuwar dokar, ku saurari Hirarsu a nan,

View Details

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na cewa wasu 'yan kunar bakin wake sun hallaka sakamakon wani bam da ya tashi a cikin a daidaita sahu da safiyar yau. Ku saurari karin bayanin da Nasidi Adamu Yahya ya aiko mana.

View Details

An gudanar da jana'izar wani yaro Bapalasdine mai shekara daya da rabi, wanda aka kashe bayan da aka cinna ma gidansu wuta a gabar yammacin kogin Jordan. Ku saurari rahoton da Halima Umar Saleh ta hada mana.

View Details

An kammala wani taro na bunkasa kasuwanci tsakanin 'yan kasuwar Najeriya dana Birtaniya a birnin London. Ku saurari hirara shugaban cibiyar kasuwanci da masana'antu ta jihar Kano a Alhaji Umar Faruk Dansuleka wanda ya jagoranci tawagar da Abdullahi Tanko Bala.

View Details

Rahotanni sun nuna kusan rabin mutane a duniya da ke amfani da shafin sadarwa na facebook, watakila suna yi ne sau daya a cikin kwanaki talatin. Wakilinmu na Lagos Umar Shehu Elleman , ya jiyo ma na ra'ayin wasu masu mu'amala da shafukan facebook, Ku saurari ra'ayoyin su.

View Details

Rahotanni daga kasar Ghana ta nuno matsalar da nakasassu ke ciki, na halin rashin muhalli da tsafe-tsafen da ake sa su ciki. Ku saurari fasarar rahoton da wakiliyar BBC, Sophie Morgan ta hada mana.

View Details

Majalisar dattawan Najeriya ta zartar da wani kudirin doka na tura tawaga ta musamman yankin arewa maso gabashin kasar. Sanata Ali Ndume shi ne shugaban masu rinjaye na Majalisar, ya kuma yi wa Yusuf Tijjani karin bayani kan kudirin da Majalisar ta zartar.

View Details

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta mutunta yarjejeniyar da ta mika tsibirin Bakassi ga Kamaru. Ku saurari rahoton da Mohaman Babalala ya aiko mana.

View Details

Wasu majiyoyi na gwamnatin kasar Afghanistan sun ce shugaban 'yan kungiyar Taliban Mullah Omar, ya mutu. Ku saurari rahoton da Ummul Khair Ibrahim ta hada mana.

View Details

Hukumomi a kasar Masar sun ce wasu 'yan bindiga sun bude wuta a kan jami'an tsaro a wajen ofishin jakadancin Jamhuriyar Nijar da ke kasar. Ku saurari hirar Bilkisu Babangida da Mal Nasiru S Rufa'i Sakkwato wani dan jarida mazaunin birnin Alkahira.

View Details

Kungiyar kare hakkin biladama ta Amnesty International ta ce akwai ''kwakkwarar shaida''cewa Isra'ila ta aikata laifukan yaki yayinda take maida martani kan cafke daya daga cikin jami'anta lokacin wani tashin hankali a Gaza. Ku saurari rahoton da Ummulkhair Ibrahim, ta hada mana.

View Details

A Nigeria, bisa ga dukkan alamu an tasamma kawo karshen takaddamar da ake fuskanta kan batun shugabancin da ya dabaibaye 'yan jam'iyyar APC mai mulki a Majalisar dattawa da kuma Majalisar wakilai. Ku saurari bayanin da Abdullahi Kaura Abubakar ya yi wa Aisha Shariff Bappa.

View Details

Shugaba Obama ya shaida wa shugabannin Afrika cewa ci gaban nahiyar ya ta'allaka ne a kan tsarin dimokradiyya, da ba da 'yancin walwala da kare hakkin bil'adama. Ku saurari rahoton da Ummulkhairi Ibrahim ta hada mana.

View Details

Kusan dakarun tsaro dubu biyu ne Ma'aikatar tsaro ta Kamaru ta ce tana shirin aikawa zuwa wasu sassan lardin arewa mai nisa domin dada karfafa tsaro akan Boko Haram. Ku saurari rahoton da Mohaman Babalala ya aiko mana.

View Details

Wata kotu a Libya ta yanke hukuncin kisa a kan dan gidan marigayi Moammar Gaddafi, Saif al Islam da wasu mutane takwas. Ku saurari rahoton Ummulkhair Ibrahim da kuma ra'ayin wani dan Nijar mazaunin birnin Tripoli na Libya.

View Details

Rikicin na jagoranci yafi kamari a zauren majalisar wakilan Najeriya sakamakon zargin da wasu 'yan majalisar suka yi cewa shugaban majalisar, Yakubu Dogara ya bujurewa umarnin uwar jam'iyyar APC. Honorabul Ibrahim Baba, Danmajlisar wakilai ne, ku saurari hirarsa da Usman Minjibir.

View Details

A Najeriya, yayin da 'yan majalisar dattawan kasar ke komawa bakin aiki ranar Talata, alamu na nuna cewa takaddama ka iya barkewa bisa zargin sauya kundin tsarin tafiyar da majalisar da wasu suka ce an yi. Ku saurari rahoton da Abdou Halilou ya hada mana.

View Details

Kamfani Glaxosmithcline na Biritaniya ya jagoranci kirkiro rigakafin zazzabin cizon sauro na farko, wanda zai taimaka wurin yaki da cutar. Ku saurari bayanin da Dr Hassan Muhammad Garba, kwararren likitan a birnin Bauchi, kuma shugaban hadin gwiwa na Kwamitin Wayar da kan al'umma game da dokar tsarin kiwon lafiya ta kasa a Najeriya.

View Details

A yau ne Najeriya ke cika shekara daya ba tare da samun wani yaro ya sake kamuwa da cutar shan inna ba. Ku saurari hirar da Yusuf Tijjani ya yi Dr Ado Muhammad, shugaban hukumar kula da harkokin lafiya a matakin farko ta tarayya a Nigeria.

View Details

Wadanda hare-haren bama-bamai da aka kai jiya a tashoshin mota a birnin Gombe na Nijeiya suka shafa, suna ci gaba da karbar magani a asibitoci, yayin da adadin wadanda suka rasa rayukansu ya karu zuwa talatin da bakwai. Ku saurari rahoton wakilinmu Is'haq Khalid domin karin bayani.

View Details

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace matakin da Amurka ta dauka na rashin sayarwa da Najeriya makamai bisa zargin keta haddin bil Adama da ake yiwa sojojin Najeriya wanda ba'a tabbatar da shi ba ya kawo nakasu wajen yaki da Boko Haram. Ku saurari hirar wakilinmu Abdullahi Tanko Bala da Dr Aliyu Musa malami a Jami'ar Coventry a Birtaniya domin jin karin bayani.

View Details

Ku saurari yadda wasu masana ke kallon ziyarar da shugaba Muhammadu Buhari ya kai Amurka. Kuma ko za'a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu? Ga hirar Yusuf Tijjani da Dr Abubakar Kyari, wani masanin kimiyyar siyasa a jami'ar Abuja.

View Details

Hukumomin tsaro a Najeriya sun yi karin haske kan cafke wani mai wakiltar mayakan Boko Haram wajen cinikin makamai. Kanar Usman Kukah Sheka, shi ne kakakin rundunar sojin kasa ta Nigeria, ku saurari bayanin da ya yiwa Abdullahi Kaura Abubakar.

View Details

Wani sabon bincike da aka yi ya nuna cewa an gano maganin-gwaji da zai hana ci gaban da cutar mantuwa ke yi. Dr Sanusi Muhammad Bello, kwararren likitan kwakwalwa ne a jami'ar Sarki Faisal dake Saudiyya, ga kuma hirarsu da Ahmad Abba Abdullahi.

View Details

Masu bincike a Jami'ar Birmingham da ke Biritaniya sun ce sun gano wasu daga cikin takardun Al-Kur'anin da mai yiwuwa suka fi tsufa a duniya. Ku saurari hutun Abdullahi Tanko Bala da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa shugaban hukumar Hizbah na Jihar Kano.

View Details

Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-rufai ya ce ba za su huta ba har sai sun magance matsalar barayin shanu wadanda ke gudanar da sace sace ,da hare hare da kuma fashi da makami a dajin Kamuku mai makwabtaka da wasu jihohi kimanin 5 ko 6 na arewacin Najeriya a wani yakin da suka soma da masu fashin dabbobin. Ku saurari hirar wakilinmu, Nurah Muhammad Ringim da gwamnan jihar domin jin karin bayani.

View Details

Jami'an tsaron Najeriya sun kama wani limamin addinin Kirista da ake zargi da safarar kananan yara a jihar Taraba ta arewa-maso-gabashin kasar. An kama mutumin a Karamar Hukumar Ibbi ne ya kwashi kananan yara goma sha bakwai, yana tafiya da su a mota inda yaran ke kukan a kai su wurin iyayensu. Ku saurari rahoton wakilinmu Ishaq Khalid domin jin karin bayani.

View Details

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-rufai ya ce ba za su huta ba har sai sun magance matsalar barayin shanu wadanda ke gudanar da sace sace ,da hare hare da kuma fashi da makami a dajin Kamuku mai makwabtaka da wasu jihohi kimanin 5 ko 6 na arewacin Najeriya a wani yakin da suka soma da masu fashin dabbobin. Ku saurari hirar waklinmu Nurah Muhammad Ringim da gwamnan jihar da kuma rahoton da ya hada domin jin karin bayani.

View Details

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi zargin cewa gazawar da gwamnatin da ta gabace shi ta yi wajen magance matsalar Boko Haram shi ne dalilin da ya sa matsalar kungiyar ke neman zama alakakai. Ya baiyana hakan ne a wata mujalla da ya wallafa a mujallar Washinton Post ta Amurka. Ku saurari hirar wakilinmu, Yusuf Tijjani da Dr Jibrin Ibrahim domin jin karin bayan.

View Details

Amurka ta ce zaben shugaban kasar da ake gudanarwa a Burundi yana da aibi sakamakon ce-ce-ku-cen da ake yi a kansa, kuma zai kuma kara rage wa gwamnatin kasar tagomashi. Shugaba Pieere Nkurunziza dai na neman ta-zarcen waadin mulkin karo na uku, duk kuwa da cewa kundin tsarin mulkin Burundi ya takaita wa shugaban kasar waadin mulki sau biyu rak. Ku saurari rahoton wakiliyarmu Badariyya Tajjani.

View Details

Fursunonin da suka futo dai suna bayyana irin mawuyacin halin da ake gamuwa da shi a gidajen kurkuku, inda suke bayyana cewa fitar da su da ake yi wata gagarumar gudunmuwa ce da za ta sauya rayuwar su. Ku saurari rahoton da wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai ya hada mana.

View Details

Shugaban Amurka Barack Obama da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya sun tattauna ne a kan muhimmancin hada-kai a fannin tsaro. Ku saurari hirar Ahmad Abba Abdullahi da Sanata Hadi Sirika, wani makusanci ga shugaban Najeriyar kuma daya daga cikin wadanda suka rufa masa baya.

View Details

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, yana ganawa da Shugaba Barack Obama a birnin Washington.

Jami'an fadar White House sun ce shugabannin biyu na tattaunawa kan yadda za su hada kai domin yaki da kungiyar Boko Haram. Ku saurari hirar wakilinmu Ahmad Abba Abdullahi da Malam Aminu Gamawa, wani dan Nijeriya mai sharhi kan al'amurran yau da kullum domin jin karin bayani:

View Details

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya isa birnin Washington inda zai gana da Shugaba Barack Obama.

Jami'an fadar White House sun ce shugabannin biyu za su tattauna kan yadda za su hada kai domin yaki da kungiyar Boko Haram. Ku saurari hirar wakilinmu Ahmad Abba Abdullahi da Malam Aminu Gamawa wani dan Nijeriya mai sharhi kan al'amurran yau da kullum,

View Details

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya isa birnin Washington inda zai gana da Shugaba Barack Obama.

Jami'an fadar White House sun ce shugabannin biyu za su tattauna kan yadda za su hada kai domin yaki da kungiyar Boko Haram. Ku saurari hirar wakilinmu Ahmad Abba Abdullahi da Mallam Aminu Gamawa, wani dan Nijeriya mai sharhi kan al'amurran yau da kullum domin jin karin bayani.

View Details

Fadar gwamnatin Amurka ta White House za ta tarbi shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a yau litinin don ganawa da shugaba Obama, a wata ziyarar kwanaki hudu da Buharin ya kai kasar ta Amurka. To ko wane tasiri ziyarar za ta yi?

View Details

Mai alfarma Sarkin Musulmi na 18 a Nigeria, Alhaji Ibrahim Dasuki ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda jami'an tsaro suka shiga gidansa na Sokoto inda suka yi binciken kwakwaf.Alhaji Ibrahim Dasuki ya ce bai kamata jami'an tsaro su shiga gidansa ba tare da neman izininsa ba. Ku saurari hirarsa da abokin aikinmu Aliyu Tanko domin jin karin bayani.

View Details

Yayinda ake ci gaba da shirye shiryen bukukuwan sallah a sassa daban daban na duniya, gwamnatin kasar Ghana ta bada sanarwar hana saye da sayar da kajin har na wani tsawon lokaci a jihar Accra, saboda cutar nan ta murar tsuntsaye da tace ta barke a wasu sassan kasar.

View Details

Kamfanin man fetur na kasar China (CNPC) ya hana fitar da man fetur na kamfanin Soraz daga Nijar zuwa kasashen waje. Ku saurari rahoton da wakilinmu Baro Arzika ya hada mana.

View Details

Masarautar Zazzau a jihar Kaduna ta ce bana ba za ta yi bikin hawan Sallah kamar yadda aka saba yi a duk shekara ba. Ku saurari karin bayanin da Alhaji Ahmed Aliyu Idris, Cika Soron Zazzau kuma dan gidan sauratar Zazzau ya yiwa wakilin mu Nurah Mohammed Ringim.

View Details

Nadin Sunday Olishen a matsayin sabon kocin Najeria ya janyo cece-ku-ce saboda wasu na sa alamar tambaya akan kwarewarsa. Ku saurari hirar Jimeh Saleh da Garba Lawal tsohon dan wasan Super Eagles.

View Details

Shugaba Buhari ya ce za a dauki matakai na binciko tare da hukunta duk wasu dake da hannu a wani haramtaccen gidan radio mai suna Radio Biafra dake watsa shirye shirye a wasu yankuna na kudu maso kudancin kasar. Ku saurari bayanin da Malam Garba Shehu mataimaki na musammman ga shugaban kasa kan yada labarai, ya yi wa Yusuf Tijjani.

View Details

Shugaban Buhari ya umurci hukumomin tsaron kasar su kara matsa-kaimi wajen murkushe masu satar fasaha a harkar fina-finai da rubuce-rubuce a kasar. Ku saurari rahoton Badariyya Tijjani Kalarawi, da kuma hirar BBC da Malam Ado Gidan Dabino, wani marubuci kuma mai hada fina-finan Hausa.

View Details

Rahotanni daga garuruwan Ngamdu da Damasak na jihar Borno na cewar mayakan Boko Haram sun kaddamar da hare-hare. Ku saurari hirar Hon Mohammed Sanda, dan Majalisar tarayya mai wakiltar yankin da wakiliyarmu Bilkisu Babangida.

View Details

Rahotanni na cewa mazauna garin Damasak, sun kwarara zuwa wasu yankuna na jihar Diffa ta Jamhuriyar Nijar. Ku saurari bayanan da Senata Abubakar Kyari, mai wakiltar yankin arewacin Borno ya yiwa Abdou Haliou.

View Details

A jihar Kaduna a yayin da wasu mabarata ke kokawa a bisa matakin hana bara da gwamnatin jihar ta kafa, gwamnan jihar Mal Nasiru El Rufai ya bayyana cewa gwamnatinsa na wasu tanade- tanade ga mabaratan. Ku saurari hirar gwamnan da wakilinmu na BBC Nurah Mohammed Ringim.

View Details

Dr Abubakar Sa'id Kanya, likita ne da yayi aikin yaki da cutar AIDS ko SIDA a wasu kasashen Afrika da dama, wakilinmu Ibrahim Isa ya tattauna da shi kan wannan batu, in da ya fara da jin ra'ayinsa kan wannan rahoto.

View Details

Sakatare Janar na MDD Ban Ki Moon ya yaba da nasarar da aka samu wajen yaki da cutar nan mai karya garkuwar jiki wato HIV AIDS.

Yana magana ne a wani taron kaddamar da wani rahoto na wani shirin hadin guiwa na MDD kan cutar ta HIV/AIDS a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Rahoton ya ce matakan da kasashen duniya suka dauka kan cutar ta HIV sun hana samun sabbin yaduwar kwayar cutar miliyan 30, da kuma mutuwar mutane miliyan 8 tun daga shakera ta 2000.

View Details

Rundunar 'yan sanda a jahar kaduna ta tabbatar da kama wani mutum wanda ake zargi da yi wa wani yaro dan shekara 9 a duniya fyade. Ku saurari rahoton wakilin mu Nurah Mohammed Ringim.

View Details

Sarkin Musulmi Muhammad Saad Abubakar ya ce sabbin manyan hafsoshin tsaron da aka nada sun zo a wani lokaci mai wuya ga sashen tsaron na kasar. Ku saurari rahoton Haruna Shehu Tangaza.

View Details

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci sababbin manyan jami'an tsaro su mayar da kimar kasar a idanun duniya. Ku saurari hirar Yusuf Tijjani da Dr Bawa Abdullahi Wase, wani masani kan sha'anin tsaro a Nigeria.

View Details

Rahotanni daga garin Fotokol na kasar Kamuru da ke kan iyaka da jihar Bornon Najeriya sun ce da safiyar yau ne aka samu gawarwakin wasu mutane 13 cikin ginin wata makarantar Firamare.

Mazauna yankin sun ce mutanen sun rasa rayukan su ne sakamakon wani harin da wasu 'yan kunar bakin wake suka kai. Ku saurari rahoton da wakilinmu Muhammad Babalala ya hada.

View Details

Rahotanni na cewar wani bam ya tashi da wani dan kunar bakin wake a garin Jimtilo da ke kusa da Maiduguri babban birnin jihar .

Lamarin ya faru ne a yau da rana lokacin da wani direban mota ya nemi a bincika mishi wani mutun da ya shiga motarsa a matsayin fasinja. Ku saurari rahoton da wakilinmu Abdu Halilu ya hada mana.

View Details

Cece-ku-ce ya kunno kai a jIhar Katsina da ke arewacin Najeriya bayan sabuwar gwamnatin APC mai mulkin a jihar ta sauke daukacin zababbun shugabanin kananan hukumomin jihar su 34 tare da mashawartan su.

View Details

Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga kungiyar likitocin Nigeria masu neman kwarewa da su janye yajin aikin da suke yi yanzu haka. Ku saurari rahoton Yusuf Ibrahim Yakasai.

View Details

Teloli dai kan taka muhimmiyar rawa wajen inganta suturar da al'umma maza da mata, yara da manya ke sanyawa a ko da yaushe. Amma babbar matsalar da mutane ke kokawa da ita game da telolin ita ce rashin cika alkawari. Ku saurari rahoton da Badariyya Tijjani Kalarawi ta hada mana.

View Details

A Najeriya, Masana sharia sun fara tofa albarkacin bakinsu game da umarnin da wata kotun tarayya ta bayar na cigaba da tsare tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido tare da 'ya'yansa biyu a gidan wakafi har zuwa 28 ga watan Satumba don ci gaba da yi musu sharaa.

View Details

Wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kai hari a daren jiya. Wata majiya ta soji ta tabbatar wa BBC hakan, amma ta ce sojoji sun dakile harin. Ku saurari rahoton wakiliyarmu, Habiba Adamu domin karin bayani

View Details

Rikicin shugabancin da Majalisar wakillan Najeriya ke fama da shi bai kusa ga kawowa karshe, duk da kwamitin da gwamnonin jam'iyya mai mulki ta APC suka kafa domin warware shi. Ku saurari wakilan bangarorin biyu, Hon. Abba Baba Kaita da Hon. Babangida Ibrahim.

View Details

Gwamnatin jahar Kaduna mai kananan hukumomi 23 na cewa a yanzu kowacce karamar hukuma za ta rinka karbar kudaden ta kai tsaye ba tare da gwamnati ta yi mata kwange ba ,domin gudanar da ayyukan raya kasa ga jama'a. Ku saurari rahoton wakilinmu Nurah Mohammed Ringim.

View Details

Masu sharhi a harkokin siyasar Nigeria sun ce hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta'annati ta fara zage-dantse saboda sun san Buhari ba zai yi wasa wajen kawar da matsalar ba. Ku saurari hirar Abdou Halilou da Dr Jibrin Ibrahim na Cibiyar bunkasa Dimokaradiya da cigaba, watau Center For Democracy And Developmment.

View Details

Takaddama ta kaure tsakanin gwamnatin Muhammadu Buhari da kuma babbar jamiyyar adawar kasar, watau PDP bayan wani kudin-shigar da kasar ta samu daga iskar-gas da ya kai sama da Dala biliyan biyu, a cikin wata guda da hawa karagar sabon shugaban kasar. Ga hirar Dr Nazifi Darma, masanin tattalin arziki a Jamiar Abuja da abokin aikinmu Ibrahim Isa.

View Details

Kungiyar Boko Haram ta dauki nauyin hare-haren kunar bakin wake da aka kai a birnin N'Djamena na kasar Chadi. Ku saurari rahoton da Muhamman Babalala ya hada mana.

View Details

Kotu ta yankewa tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido zaman kurkuku har tsawon watanni biyu kafin a sake sha'i'a, bayan hukumar EFCC ta kai wa kotun karar sa. Ku saurari bayanin lauyan EFCC da kuma korafin da lauyan tsohon gwamnan ya gabatar.

View Details

Masana harkokin tsaro a Najeriya sun bayar da shawarwari a kan yadda 'yan Najeriya zasu taimaka wajen dakile hare-haren Boko Haram. Ku saurari hirar wakilin mu, Abdu Halilu da shugaban cibiyar samar da bayanai a kan tash-tashen hankula a Najeriya.

View Details

Rundunar 'yan sanda a Najeriya ta hana talace-talace a jihar Kaduna domin 'yan ta'ada na iya shiga rigar masu tallar domin yin kunar bakin wake. Ku saurari hirar wakilin mu Nura Mohmmad Ringim da kakin rundunar 'yan sanda na jihar kadun domin karin bayani.

View Details

Shin ko kun san ta yaya za ku kare kan ku daga masu hari kunar bakin wake? Ku saurari hirar wakilinmu Abdou Halilou da Air Commando(rtd) Yusuf Anas, shugaban cibiyar bincike kan tashe- tashen hankula a Najeriya.

View Details

Mahaifiyar daya daga cikin 'yan matan Chibok da aka kama, ta yi kira ga shugaba Buhari da ya taimaka ya ceto mata 'yar ta daga hannun kungiyar ta Boko Haram. Ku saurari abinda ta ce.

View Details

Wacce ta lashe lambar yabo ta rubutun adabi na kasashen Afirka wato Caine Prize for African Writing,Namwali Serpell 'yar kasar Zambia, ta ce zata raba kyautar kudin da ta samu tare da wadanda aka tantance su tare. Ku saurari hirar BBC da Elnathan John, dan Najeriya kuma daya daga cikin wadanda aka tantance domin samun lambar yabon.

View Details

Babban mataimaki mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan watsa labarai, Malam Garba Shehu, ya ce alhakin Hafsan Sojin kasar ne ya mayar da shingayen binciken abubuwan hawa a wuraren da ke da matukar hatsari bayan shugaban kasar ya umarce shi ya janye shingayen daga kan titunan kasar. Ku saurari karin bayanin da ya yi wa Haruna Tangaza:

View Details

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido tare da 'ya'yansa guda biyu bisa zargin almundahana da kudaden jihar.

View Details

Akalla mutane 44 ne suka rasa rayukansu sannan wasu 47 suka jikkata bayan tashin tagwayen bama-bami a Jos, babban birnin jihar Plateau da ke tsakiyar arewacin Najeriya a daren Lahadi. Ku saurari hirar da a ka yi da wakilnmu Wakilinmu Isha'q Khalid

View Details

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta sanar da kudaden kujerun aikin hajjin bana. Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a Abuja. Ga hirar Alhaji Uba Mana kakakin hukumar aikin hajjin ta kasa,da abokiyar aikinmu, Ummulkhairi Ibrahim.

View Details

Rahotanni daga jihar Borno a arewacin Najeriya na cewa, alumomin Kukawa suna can suna kokarin janaizar yan uwansu da ake zargin mayakan boko-haram da kashewa. Ku saurari karin bayanin da wani dan garin Kukawa, mazaunin Maiduguri, wanda ke shirin tafiya Kukawa don yin janaiza, ya yi wa Bashir Sa`ad Abdullahi.

View Details

Fadar shugaban Najeriya ta mayar da martani game da zargin da jam'iyyar adawa ta PDP ta yi , cewa shugaba Muhammadu Buhari bai bi ka'ida ba, wajen nada Amina Zakari a matsayin shugabar hukumar Zaben kasar mai rikon kwarya. Ku saurari rahoton da Haruna Shehu Marabar Jos ya hada mana.

View Details

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya shaida wa BBC cewa yana goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari dari bisa dari, yana mai cewa shi cikakken dan jam'iyyar APC ne. Ku saurari hirarsa da Harun Tangaza Tangaza.

View Details

Wasu 'yan jam'iyyar APC a jihar Kaduna da ke Najeriya sun yi zargin cewa gwamna Malam Nasir El-Rufai yana nada bare mukamai. Ku saurari rahoton wakilinmu Nurah Mohammed Ringim.

View Details

Masana sun soma yin tsokaci a kan jan- kafar da gwamnatin Muhammadu Buhari ke yi, wajen kafa kwamitin da zai rika sa ido kan tattalin arzikin kasar. Dr Obadiah Mai lafiya tsohon mataimakin direkta ne a babban bankin Najeriya, kuma mai sharhi a kan tattalin arziki, ga kuma hirarsu da Raliya Zubairu.

View Details

Makonni bakwai bayan an bayyana Liberia a matsayin kasar da ta kawar da cutar Ebola, an bayar da rahoton wani da ya kamu da cutar a kasar. Ku saurari rahoton da Haruna Shehu Marabar Jos, ya hada mana.

View Details

Yau ne dai wa'adin shugaban hukumar zaben Najeriyar Farfesa Attahiru Jega yake karewa. Dr Kole Shettima na kungiyar bunkasa dumokradiyya da ci gaba a Afrika da ke Abuja, ya yi bayanin nasarorin da Jega ya samu.

View Details

Muhammadu Buhari ya kaddamar Majalisar koli kan tattalin arziki, kuma za ta gudanar da bincike kan yadda kamfanin mai na kasar, NNPC ya karkatar da wasu kudade da yawan su zai kai Naira Tiriliyan Uku da rabi. Ga hirar da Haruna Shehu Marabar Jos ya yi da Alhaji Badaru Abubakar, gwamnan jihar Jigawa, kuma mamba a majalisar.

View Details

Kimanin mutane miliyan 60 ne da ke kasashen kudu da Sahara ke cikin barazanar kamuwa da cutar Bacci a Afruka, wanda KUDAN TSANDO ke haddasawa. Ga fasarar rahoton Maryam Arua, da Badariyya Tijjani Kalarawi ta hada mana.

View Details

A yayin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke cika wata guda cif da fara aiki a ranar Litinin, jam'iyyar adawa ta PDP ta soki sabuwar gwamnatin da jan- kafa da kuma rashin sanin alkiblar kasar. Ga hirar Malam Abdullahi Bayero na wata Kungiyar dake fadakar da al'umma, da abokin aikinmu Ibrahim Mijinyawa.

View Details

Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wani otal da 'yan yawon bude ido ke zuwa kasar Tunisia, inda suka hallaka akalla mutane 27. Ku saurari rahoton da Habiba Adamu ta hado mana.

View Details

Najeriya dai na daya daga cikin kasashen da su ka rattaba hannu akan yaki da fataucin miyagun kwayoyi. Ku saurari hirar wakilinmu Umar Shehu Elleman da Alhaji Ahmadu Gyade, shugaban hukumar NDLEA.

View Details

A Najeriya, a jiya Alhamis ne aka samu yamutsi a majalisar wakilan kasar game da maganar zaben shugabanin majalisar. Ku saurari tattaunawar Usman Minjibir ya yi da, Dr. Abubakar Kyari masanin kimiyyar siyasa a Najeriya kuma malami a jami'ar Abuja.

View Details

A jiya ne wata babbar kotun addinin musulunci da ke zama a Kano ta yankewa wasu mutane tara hukuncin kisa a sakamakon samun su da laifin cin zarafin Manzon Allah (saw). Ku saurari hirar Bilkisu Babangida da Malam Aminu Daurawa, shugaban hukumar Hizba na Kano.

View Details

Bincike ya nuna cewa mutane da dama ne ke mutuwa bisa dalilin rashin jini a jika a daidai lokacin da suka fi bukatarsa. Ku saurari rahoton da wakilinmu Yakubu Liman ya hado mana.

View Details

Wasu dattijai a Najeriyar suka fara tofa albarkacin bakinsu kan yadda suke kallon tafiyar gwamnatin shugaban kasar Muhammadu Buhari bayan rantsar da shi. Farfesa Dandatti Abdulkadir, tsohon jami'in diplomasiyya ne, kuma ga hirarsu da wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai.

View Details

A Najeriya, yanzu haka dai a na ci gaba da kai ruwa rana a majalisar dattawan kasar game da maganar shugabanci a majalisar. Ku saurari hirar da Abdou Halilou ya yi da Sanata Suleyman Nazifi Gamawa, mai wakiltar Bauchi.

View Details

A Najeriya, hukomomin lafiya a jihar Kano sun ce matashiyar nan da a makon jiya ta je wani gidan rediyo domin neman mijin aure, yanzu haka tana jinya a asibitin masu tabin hankali. Ga karin bayanin da Malam Isma'ila garba Gwammaja, jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar lafiya ta jihar Kano ya yi wa Nasidi Adamu Yayaya.

View Details

Wasu yan bindiga a kan Dawaki sun kai hari a kauyen Yebbi da ke jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar jiya da daddare, inda suka banka wa gidaje da shaguna wuta tare da hallaka jamaa. Ku saurari hirar da Bilkisu Babangida ta yi da wani daga cikin su.

View Details

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta samu tabbaci daga Amurka da wasu kasashe, domin kwato kudaden da aka sace, aka ajiye a kasashen. Ku saurari hirar mai taimaka wa shugaban kasar a kan harkokin yada labarai, Mallam Garba Shehu, da Ibrahim Isa.

View Details

Shugaban Faransa, Francois Hollande zai tattauna da shugaba Barack Obama a kan wani bayanin da aka kwarmata cewa jami'an Amurka sun leki asirin shugaba Hollande da wasu shugabannin Faransa biyu da suka gabace shi. Ku saurari rahoton Mansur Liman ya hada mana.

View Details

'Yan gudun hijirar dai na kokawa da rashin wadatar abinci da ruwan sha, a cikin wannan lokaci na azumi. Ku saurari abinda abun da daya daga cikinsu ya shaidawa abokin aikin mu, Abdou Halilou.

View Details

Ana bukatar mawadata su yi kokarin yin alherin ciyarwa a lokacin azimin watan Ramadan, musamman wa mabarata da ke yawo kwararo kwararo suna neman taimako. Ku saurari rahoton da rahoton wakilinmu Nurah Mohammed Ringim, ya aiko mana a kan wannan batu.

View Details

Shafin Wikileaks mai kwarmata bayanan sirri ya wallafa wasu bayanai da suke nuna cewa hukumar leken asiri ta Amurka ta leko asirin shugaban Faransa Francois Hollande. Ku saurari rahoton da Haruna Shehu Marabar Jos ya hada mana.

View Details

Gwamnatin Kasar Rwanda ta mayar da martani da kakkausan lafazi akan kame shugaban hukumar leken asirin kasar da aka yi a birnin London, bisa umarnin wani alkalin kasar Spaniya. Ku saurari rahoton da Mansur Liman ya hado mana.

View Details

Kasar Rwanda ta bayyana tsarewar da aka yi wa shugaban hukumar leken asirinta, Karenzi Karake a London da cewar abin takaici ne matuka. Ga tattaunawar Ahmad Abba Abdullahi da Barrister Aminu Gamawa, lauya mai bincike a jami'ar Harvard ta Amurka, ya kuma dade yana zuwa Rwanda.

View Details

Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnonin jihohi sun ce za su duba matsalolin da suka janyo tabarbarewar tattalin arziki, lamarin da ya sa wasu jihohi suka gaza biyan albashi na watanni da dama. Ga hirar Nasidi Adamu Yahaya da gwamnan jihar Kano, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje a kan wannan batu.

View Details

A yau Litinin ne majalisar dokokin kasar Najeriya ke komawa hutun da 'yan majalisar suka tafi, tun bayan kaddamar da majalisar a farkon wannan watan. Ku saurari tattaunawar Nasidi Adamu Yahaya da Honourable Mohammed Tahir Monguno.

View Details

Wasu gwamnonin Najeriya musamman na arewa na kukan karancin kudi, har ma ta kai ga wasunsu na ragewa kansu albashi da kuma duba yiwuwar rage ma'aikata ko albashin ma'aikatan. Ku saurari hirar Sanata Shehu Sani, da wakilinmu Nura Muhammad Ringim, a kan wannan batu.

View Details

An shawarci sabon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya soke tsarin bayar da tallafin mai a kasar. Ku saurari bayanin Chief Audu Ogbeh, wani jigo a jam'iyar APC mai mulkin Najeriyar, kuma memba a kwamitin da ya bada shawarwarin.

View Details

Wasu jerin hare-haren gurneti a wasu sassan kasar Burundi sun hallaka mutane hudu tare da jikkata 30. Ku saurari rahoton da Jimeh Saleh ya hada mana.

View Details

'Yan sanda a Accra na kasar Ghana sun fesa barkonon-tsohuwa a kan dubban mutanen da ke yin zanga-zanga saboda za a rushe unguwar matalauta mafi girma a birnin. Ku saurari abunda daya daga cikin mazauna unguwar ke cewa.

View Details

A yau Litinin ne tashar watsa labarai ta BBC a yankin Afrika take fara kawo muku jerin rahotanni na tsawon mako guda da suka shafi cututtukan da nahiyar ke fama da su wadanda mutane basa iya yada su ga wasu ta hanyar mu'amala. Wakiliyarmu Tchima Illa Issoufou ta duba mana matsalar Hawan jini a jihar Tahoua ta jamhuriyar Nijar, ku saurari rahoton da ta hada mana

View Details

Yayin da ake ci gaba da azumin watan Ramadan a fadin duniya, wasu daga cikin musulmai sukan hada azumin ne da aikin karfi cikin zafin rana saboda irin sana'ar da suke yi. Ga rahoton da wakilinmu Is'haq Khalid ya hado mana.

View Details

Wasu 'yan majalisar dattawan Najeriya a karkashin jam'iyyar APC sun ce za su bijirewa duk wani yunkuri da za ta yi domin tursasa musu zabar sauran shugabannin majaliasar. Sanata Danjuma Goje na cikinsu, kuma ga abin da ya sahaida wa BBC.

View Details

Mutane akalla 23 aka bayyana sun hallaka a garin Monguno da ke jihar Borno, arewa maso gabashin kasar. Ku saurari hirar Honorabul Tahir Monguno da Bashir Sa'ad Abdullahi a kan wannan batu.

View Details

Shugaban rukunin masa'antun Dangote yace zai kafa masana'antu biyu na sarrafa shinkafa da sikari a jihar Jigawa dake arewa maso yammacin Najeriya. Ku saurari rahoton da wakilin mu Yusuf Ibrahim Yakasai.

View Details

Yayin da ake kokawa da matsalar cunkoso a gidajen yarin Najeriya, wasu bayanai sun nuna cewa fursunoni suna cikin mawuyacin hali, kuma abin tausayi a galibin gidajen yarin. Ku saurari rahoton da wakilinmu AbdusSalam Ibrahim Ahmed ya aiko mana.

View Details

'Yan Nigeria sun yi amfani da shafukan zumunta na intanet inda suka caccaki 'yan majalisar dokokin kasar a kan batun kudaden alawus da za su karba da suka kai naira biliyan tara. Ku saurari bayanin Malam Ibrahim Muhammad wanda shi ne kakakin hukumar da ke kayyade albashi da alawus alawus na masu rike da mukaman siyasa.

View Details

A yau ne ake sa ran shugabannin wata babbar hukumar da ke yaki da almundahana ta fuskar ma'adinan da ake hakowa daga kasa mai suna NEITI za su gana da shugaba Muhammadu Buhari ko mataimakinsa. Ku saurari tattaunawar Hajiya Zainab Ahmed, sakatariyar zartarwar hukumar da ke yaki da almundahana ta fuskar ma'adinai a Najeriya, NEITI, da Haruna Tangaza.

View Details

Gwamnatocin wasu jihohin Nijeriya sun himmatu domin bincike da kuma kwato kadarori da kudade na gwamnati daga tsofofin gwamnoni da sauran jama'a da ake zargin sun kwashe. Ku saurari rahoton da wakilinmu Is'haq Khalid ya aiko mana.

View Details

A Najeriya hukumomi a matatar man NNPC ta Kaduna na musanta zargin samun matsalar haihuwa a tsakankanin jama'a dake makwabtaka da matatar man. Ku saurari rahoton da wakilinmu Nurah Mohammed Ringim ya hada mana.

View Details

Kwamitin da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya kafa domin tallafa wa mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu, watau Victims Support Fund, ya ce har yanzu bai kai ga fara aiki ba duk kuwa da tsananin bukatar tallafin da mutanen ke yi. Malam Alkasim Abdulkadir shi ne kakakin kwamitin, ga kuma hirarsu da Nasidi Adamu Yahaya.

View Details

Shugabannin kasashen yankin tafkin Chadi da Benin sun ce dakarun rundunar hadin-gwiwarsu za su fara aikin fatattakar Boko Haram a karshen watan Yuli. Ku saurari bayanin Dr Muhammad Kabir Isa malami a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya kuma mai sharhi a kan al'amuran tsaro.

View Details

Gwamnatin Jihar Niger ta bukaci manyan jami'an tsohuwar gwamnatin da ta sauka su hanzarta mayar da kusan naira biliyan 3 da suka ranta kwana guda kafin karewar wa'adin mulkinsu. Kakakin gwamnan Niger, Ibrahim Dooba ya ce ba za a bar dukiyar al'umma ta salwanta ba. A yayinda kakakin tsohon gwamna Mu'azu Aliyu wato Israel Ebije ya ce babu ko asi da gwamnatinsa ta kwashe. Ku saurari tattaunawar da aka yi da su a nan,

View Details

Shugabannin kasashen da ke makwabtaka da Tafkin Chadi da kuma Jamhuriyar Benin, za su gana a Abuja da nufin daukar muhimman matakai na kafa rundunar hadin gwiwar da za ta yaki kungiyar Boko Haram. Ku saurari karin bayanin da Injiniya Sanusi Imran Abdullahi shugaban Hukumar Raya Tafkin Chadi, ya yi wa Raliya Zubairu.

View Details

Daga yanzu masu amfani da wayar salula a Nijeriya za su iya sauraron shirye-shiryen BBC na Hausa da kuma harshen Ingishi ta hanyar kiran lambar 01-440522. Ku saurari tattaunawar da Ahmed Abba Abdullahi ya yi da abokin aikinmu Aliyu Abdullahi Tanko, wanda ke lura da shafinmu na inatanet da kuma salula.

View Details

Wata mata `yar kasar Belgium ta kasance ta farko a duniya da ta haihu ta hanyar sake dasa mata jakar kwan-mahaifa, wadda aka cire mata tun tana karama aka kuma adana ta hanyar ajiye kwan a Firji. Ku saurari rahoton da Bilkisu Babangida ta hada mana.

View Details

Wani rahoton da Kungiyar kare hakkin biladama ta fitar ya yi zargin cewa manyan kamfanonin sarrafa Gwal na ci da gumun kananan yara a kasar Ghana, a wajen hakar maadinan da ake yi ba bisa ka`ida ba. Ku saurari rahoton da Badariyya Tijjani Kalarawi ta hada mana.

View Details

An tashi baran-baran a zauren majalisar dattawan Najeriya tsakanin 'yan majalisar nan 53 da aka yi zaben shugabannin majalisar basa nan, da kuma sauran 'yan majalisar masu biyayya ga jagorancin shugaban majalisar Sanata Bukola Saraki. Ku saurari rahoton da Haruna Shehu Tangaza ya aiko mana.

View Details

Hukumar kula da safarar jiragen sama ta Najeriya ta ce ta sake bude filin jiragen saman Maiduguri, babban birnin jihar Borno. Ku saurari karin bayanin da Kakakin hukumar, Mr Yakubu Dati ya yi wa Nasidi Adamu Yahaya.

View Details

Wani masanin kimiyyar siyasa a Najeriya, Dr. Kabir Mato wanda malami ne a sashen koyar da kimiyyar siyasa a jami'ar Abuja, ya ce zaben da aka yi a majalisar dokoki da ta wakilai bai saba kundin mulkin kasa ba. Ku saurari sharhin da ya yi mana.

View Details

Shugaba Muhammadu Buhari ya mai da martani ga yadda zaben shugaban majalisar dattawan kasar ya gudana, yana mai cewa ba haka aka so ba. Sai dai jam'iyyar ta APC ta ce sam ba za ta sabu ba. Ku saurari rahoton da Muhammad Kabir Muhammad ya hada mana.

View Details

Barrsiter Muhammad Shu'aibu lauya ne mai zaman kansa a Abuja, ya kuma yi wa Yakubu Liman karin bayani a kan matsayin zaben shugabannin majalisar dokokin Najeriya a ma'aunin dokar majalisa.

View Details

An zabi tsohon gwamnan jihar Kwara, Sanata Abubakar Bukola Saraki a matsayin sabon shugaban majalisar dattawan Nigeria, zubi na takwas. Sai dai wasu masana sharaa a nasu bangaren na ganin cewa an yi wannan zaben ba bisa kaida ba, ku saurari bayanin Furofesa Awwalu Yadudu na jami`ar Bayero ta kano.

View Details

Sanata Ali Ndume, dan majalisar dattawa mai wakiltar jihar Borno, yana daga cikin masu ganin cewa zabin da uwar jam'iyyar tayi tamkar yi wa tsarin dimokradiyya karan tsaye ne. Ku saurari ra'ayin sa.

View Details

A ranar Litnin ne rundunar sojin Nigeria za ta mayar da cibiyar da ke jagorantar kai hare-hare zuwa Maiduguri, babban birnin jihar Borno. Ku saurari hirar Abdullahi Tanko Bala da Malam Hussaini Mungono, mai sharhi kan al'amuran tsaro a Najeriya.

View Details

Wasu ma'aikatan kananan hukumomi a jihar Yobe dake arewa maso gabashin Nigeria sun yi zargin cewa an hana su albashi tsawon wata biyu, sabo da wasu dalilai na siyasa. Ku saurari karin bayanin da wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai, ya aiko mana.

View Details

A Najeriya, alkaluman da kungiyoyi masu kare muhalli suka bayar , sun yi nuni da cewa mutane akalla 95000 ne ke mutuwa duk shekara sakamakon shakar hayakin girkin itace. Ku saurari rahoton da Yakubu Liman ya hada mana.

View Details

A Najeriya zaben share fagen da jam'iyyar APC ta gudanar gabanin zaben shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai na barazanar kawo baraka a jam'iyyar. Ga hirar Malam Muhammad Sani Zorro, zababben dan- majalisar wakilai daga jihar Jigawa, da Abdou Halilou.

View Details

Shugabannin kasashen na G7 sun gayyaci shugaban na Najeriya Muhammadu Buhari da ya halarci taron nasu, kuma sun nemi ya tafi da bukatun kasarsa, don su duba yiwuwar biya masa. Babban maitaimaki na musamman ga shugaban Najeriya a kan al'amuran yada labarai, Malam Garba Shehu, ya yi wa Muhammad Kabir Muhammad karin bayani. Ku saurara a nan,

View Details

Yau ne kungiyar kwadago ta duniya ILO ke gudanar da wani taro a birnin Geneva, don tattanawa da kuma rattaba hannu kan dokar kawar da bauta a kasashen duniya. Ga hirar Bilkisu Babangida da Alhaji Mustapha Khadi wanda shine shugaban kungiyar RDM mai yaki da bauta a Jamhuriyar Nijar.

View Details

Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya ta ce mutane akalla 31 ne suka mutu yayinda 40 suka jikkatta a wani harin kunar bakin wake ya kai wa wata kasuwa a garin Jimeta a jiya a jihar Adamawa.

View Details

Majalisar dokokin kasar Najeriya ta yi zamanta na ban kwana jiya Alhamis gabanin kaddamar da sabuwar majalisa. Haruna Shehu Tangaza ya nemi jin ra'ayoyin wasu daga cikin 'yan majalisar dattawa masu barin gado, ku saurara a nan,

View Details

Gwamnatoci da dama wadanda suka gabata dai sun sha yin alkawarin farfado da matatun man Najeriya, amma kawo yanzu lamarin ya faskara. Shin ina matsalar ta ke? Wakilinmu Is'haq Khalid ya duba mana lamarin, ku saurari rahotonsa.

View Details

Gwmnati kasar Ghana ta ayyana kwanaki uku na zaman makoki dangane da asarar rayukan da aka samu a birnin Accra, sakamakon ambaliyar ruwa da kuma gobarar da suka abka wa babban birnin kasar.

View Details

Rahotanni daga Borno da Adamawa a Najeriya sun ce an kai harin kunar bakin waken da ya kashe wasu kuma ya jikkata mutane. Ku saurari rahoton da wakilinmu Haruna Shehu Marabar Jos, ya hada mana.

View Details

Jama'a da dama na cikin halin kaka-ni-kayi a Accra, babban birnin kasar Ghana, sakamakon ambaliyar ruwa da aka yi. Ku saurari abinda Kamar Irbard Ibrahim, wani mazaunin birnin ya shaidawa Jimeh Saleh.

View Details

Shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama ya ziyarci gidan man da aka yi gobarar da ta hallaka jama'a. Ga kuma abunda ya ce,

View Details

Ana cigaba da shirye shiryen gudanar da zaben badi a jamhuriyar Nijar. Hukumomi kuma sun kaddamar da aikin rajistar masu kada kuri'u. Ku saurari rahoton da wakilinmu Baro Arzika ya aiko mana.

View Details

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari,ya kammala ziyarar aikin da ya kai a kasar inda ya tattauna da hukumomin kasar a kan maganar yaki da kungiyar Boko Haram. Ku saurari rahoton da wakilinmu Baro Arzika ya aiko.

View Details

Ma'aikatar lafiyar Najeriya sun musanta cewa wasu ma'aikatan lafya da suka je inda cutar Ebola tafi kamari watau Liberia da Saliyo, sun shiga wani hali sakamakon kullesu da aka yi cikin wani Otal din da suka sauka a Abuja. Ku saurari hirarar da Badriyya Tijjani Kalarawi ta yi da Farfesa AbdusSalam Nasidi, jagoran hukumar hana yaduwar cututtuka a Nigeria.

View Details

Kasar Kamaru ba ta cikin jerin kasashen da Shugaba Muhammadu Buhari zai ziyarta fitarsa ta farko zuwa kasashen dake makwabtaka da Nigeria wadanda ke fama da hare-haren Boko Haram. Yusuf Tijjani ya yi wa Ambassada Sulaiman Dahiru, wani masanin harkokin diplomasiyya a Nigeria, tambaya akan meye dalilin rashin kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashen biyu?

View Details

Tsohon jami'in Fifa Chuck Blazer, ya fayyace yadda suka dinga karbar cin hanci da rashawa tun daga shekarar 2013 a lokacin sauraren kara a New York. Ku saurari rahoton da Usman Minjibir ya hada mana.

View Details

Wakilinmu Yakubu Liman ya tattauna da wani dan asalin yankin arewa maso gabashin Najeriya, wanda ya bayyana masa yadda sojojin da aka tura yaki da 'yan Boko Haram suka rika cin zarafinsu. Ku saurari hirarsu a nan.

View Details

Shugaba Muhammadu Buhari yayi alkawarin bincikar zargin cin zarafin da Kungiyar kare hakkin bil adama, Amnesty International tayi wa sojojin Najriya. Ga hirar Ahmad Abba Abdullahi da wani tsohon sojan da yayi yaki a yankin na Arewa maso gabas, wanda ke musanta zargin da ake yi ma sojojin na aikata ta'asa.

View Details

Kungiyar Amnesty International ta ce ya kamata a tuhumi wasu manyan sojojin Nigeria da laifin cin zarafin bil'adama da kuma laifukan yaki. Ku saurari rahoton da Haruna Shehu Tangaza, ya hado mana.

View Details

Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara jamhuriyar Nijar domin tattauna yadda za a yaki kungiyar Boko Haram. Ku saurari rahoton Baro Arzika.

View Details

'Yan sandan Ghana sun yi wa al'ummar kasar kashedi cewa su yi hankali da pastocin zamani dake shugabancin majami'u saboda halayensu na yaudara da damfarar mutane. Ku saurari fassarar rahoton da wakilin BBC Sammy Darko ya hado.

View Details

Wasu magoya bayan tsohon gwamnan jihar Jigawa sun maida martani dangane da ikirarin cewa ya bar wa jihar basussukan fiye da Naira biliyan 100. Ga hirar da Sanata Abdulmuminu Muhammad Hassan, daya daga cikin makusanta ga tsohon gwamnan ya yi da Yusuf Tijjani.

View Details

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika takarda zuwa majalisar dattijai domin neman amincewarta ya nada mukaman mataimaka na musamman 15 a gwamnatinsa. Ku saurari tattaunawar da wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai ya yi da Farfesa Umar Pate na sashen nazarin aikin jarida a jami'ar Bayero da ke Kano.

View Details

Jami'an kasar Amurka sun fara bincikar tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Sepp Blatter, jim kadan bayan ya yi murabus. A hirar Ibrahim Isa da Alhaji Ibrahim Galadima tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Nigeria, ya yi karin bayani a kan lamarin. Ku saurara.

View Details

Masu aikin ceto a China na can suna kokarin neman sama da mutane 400 da wani jirgin ruwa da ya kife da su a kogin Yangtze. Ku saurari rahoton da Badariyya Tijjani Kalarawi ta hada mana.

View Details

Masana a harkar muhalli da kuma kwararru kan tsara birane na ci gaba da tsokaci dangane da yawan gidajen da ke cikin Abuja, ana kuma fama da matsalar rayuwa a wasu unguwannin na maras sa galihu. Ga rahoton da Yakubu Liman ya hada mana.

View Details

Kafofin sadarwa na zamani a tsakanin al'umma na karuwa sosai, musamman sakamakon karuwar da wayoyin salula ke yi. Aisha Shariff Baffa ta yi nazari akan wannan batu ga kuma rahoton da ta hada mana.

View Details

Tsohon gwamnan jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya, Rear Admiral Murtala Nyako mai ritaya, ya ce bai mallaki ko da dala daya ba a kasashen duniya. Ga hirarsu da Yusuf Tijjani .

View Details

Direbobin motocin haya suna yajin aiki a Accra, babban birnin Ghana a wani zanga-zanga domin nuna adawa ga sabobbin dokokin da aka bullo da su. Iddi Ali ya aiko mana karin bayani, ku saurara.

View Details

A shekarar nan an samu gagarumar asarar rayukan 'yan ci-rani a tekun bahar Rum, kuma yawancin masu kasadan dai suna tasowa ne daga gabar tekun Libya, 'yan gudun hijira dai manema arziki ne. Ku saurari fassarar rahoton Rana Jawad.

View Details

Hukumomi a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nigeria sun ce mutane 69 sun mutu lokacin da wata tankar mai ta kife a wata tashar mota da ke birnin Onitsha. Ku saurari rahoton da wakilinmu AbdusSalam Ibrahim Ahmed ya hado mana.

View Details

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nigeria, EFCC, za ta gurfanar da wasu manyan jami'an babban bankin kasar gaban kuliya bisa zargin zamba. Ku saurari rahoton abokin aikin mu Abdou Halilou.

View Details

To shin mene ne mata ke fatan samu daga sabuwar gwamnatin? Wakilinmu Is'haq Khalid ya ji ta bakin wata mai fafutikar kare hakkin mata da kyautata rayuwarsu a Nijeriya, Mrs Hannatu Ibrahim. Ku saurari hirarsu a nan.

View Details

Masana tsara-tsaren birane sun yi kira ga sabuwar gwamnati ta Muhammadu Buhari da ta gudanar sauye sauye kan tsarin sayan filaye da kuma mallakar gidaje a birnin Abuja. Malam Umar Shu'aibu masanin tsara birane ne a Abuja, ku saurari hirarsu da Raliya Zubairu.

View Details

Wasu tsofaffin mata a kasar Uganda sun gudanar da zanga-zanga tsirara a gaban ministocin kasar game da mallakar filaye. Ku saurari fassarar wakiliyar BBC Catherine Byaruhanga.

View Details

Wasu al'ummar arewa mazauna birninn Lagos, sun gudanar da addu'oi na musammman ga sabuwar gwamnatin kasar tare kuma da add'u'ar samun ci gaba mai dorewa. Ku saurari rahoton da wakilinmu na Lagos Umar Shehu Elleman ya aiko mana.

View Details

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari zai kai ziyara Jamhuriyar Nijar ranar Laraba, a wani mataki na kawo karshen hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram. Malam Garba Shehu, shi ne babban mataimaki na musammman kan harkokin watsa labarai, ga kuma bayanin da ya yiwa Yusuf Tijjani.

View Details

Ku saurari bikin rantsar da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai ya dauko mana.

View Details

To shin ko menene tarihin zababben mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo. Umar Shehu Elleman ya duba ma na tarihin sa, ga kuma rahoton daya aiko mana.

View Details

Honorable Lawal Garba tsohon dan Majalisar wakilai ne a Nigeria, kuma daya daga cikin wadanda keda kyakkawar dangantaka da shugaba Muhammadu Buhari, a tsawon shekarun daya shafe yana neman mukamin shugaban kasar. Ga hirar sa da Ibrahim Isa.

View Details

To shin wanene Muhammadu Buhari, sabon zababben shugaban Najeriya? Badariyya Tijjani Kalarawi ta yi waiwaye akan rayuwar sa, ku saurari rahotonta.

View Details

Shugaban Hukumar Kwallon kafa na duniya, Sepp Blatter ya ce ba zai yi murabus daga mukaminsa ba, kuma ba zai fasa takarar da yake yi ta shugabancin hukumar ba. Ku saurari rahoton da Badariyya Tijjani Kalarawi ta hada mana.

View Details

Mazauna jihohin dake samun wuta daga kamfanin rarraba wutar lantarki dake Kano na fuskantar karancin wutar lantarki mafi tsanani a shekaru da dama. Ku saurari rahoton da wakilin mu Yusuf Ibrahim Yakasai ya aiko mana.

View Details

Majalisar zartarwar Najeriya ta yi zamanta na karshe jiya a karkashin Jagorancin shugaban kasa mai-barin-gado Goodluck Ebele Jonathan. Haruna Shehu Tangaza ya nemi jin ta bakin wasu daga cikin ministocin masu-barin-gado, ku saurari hirarsu a nan.

View Details

Mamayewa da man fetur ya yi a Najeriya tana kassara tattalin arzikin kasar ta hanyar hana habbakar sauran harkokin kasuwanci. Wakilinmu AbdusSalam Ibrahim Ahmed ya duba mana abinda ya kamata a yi don gyara wannan bangare na man fetur yadda al'amura za su kyautata a Najeriyar, ku saurari rahotonsa.

View Details

Binciken cin hanci da rashawa da ake gudanarwa a hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA na ci gaba da fadada. Amurka ta zargi tsohon mataimakin shugaban hukumar, Mista Jack Warner da hannu a badakalar cin hancin. Ku saurari rahoton da Haruna Shehu Marabar Jos ya hada mana.

View Details

A jamhuriyar Niger, majalisar dokokin kasar ta amince da bukatar gwamnati ta tsawaita dokar ta-baci a jihar Diffa ta tsawon wata uku. Ku saurari rahoton Tchima Illa Issoufou daga Maradi.

View Details

Rundunar sojan Nigeria ta ce yawan sojojin da aka sallama daga aikin soja a yan kwanakin nan, ba su kai dubban da ake shaci fadi a kansu ba. Ga tattaunawar Ahmad Abba Abdullahi, da Kakakin rundunar sojan Nigeria Kanar Sani Usman Kukasheka.

View Details

Shugaban majalisar dokokin Nigeria Aminu Waziri Tambuwal ya bar kujerarsa ta Kakakin majalisar gabanin karewar wa'adinsa a farkon watan gobe. Ku saurari hirar Kakakin Majalisar dokokin kasar Hon. Aminu Waziri Tambuwal da wakilin BBC Haruna Shehu Tangaza.

View Details

Muhimman alkawuran da shugaban Najeriya mai jiran gado Muhammadu Buhari ya yi a lokacin yakin neman zabe, su ne cewa zai mayar da hankalinsa kan magance rashin tsaro, da rashin aikin-yi da kuma cin-hanci da rashawa. Ku saurari rahoton da Haruna Shehu Tangaza ya hada mana.

View Details

Wasu kananan sojoji a Najeriya sun yi ikirarin cewa ana sallamar su daga aikinsu, kuma mai yiwuwa a sallami karin wasu a nan gaba. Ku saurari karin bayanin Yusuf Tijjani.

View Details

Shugaban kasa mai barin gado Goodluck Jonathan ya sanya hannu a kan wata dokar cin zarafin mutane. Ga tattaunawar Aisha Shariff Baffa da babbar Sakatariyar kungiyar kare hakkokin mata da tabbatar da yi musu adalci watau WRAPA Hajiya Saudatu Mahdi kan wannan batu. Ku saurara a nan.

View Details

Mahukunta a birnin Shiyan na kasar Sin wato China sun kai jami`an gwamnati da matansu da ke yankin gidan yari domin yi masu gargadi. Ku saurari fassarar rahoton wakilin BBC Michael Bristow.

View Details

Ali Nuhu ya shaida wa BBC cewa matsalar satar fasaha ita ce babbar matsalar da ke addabar sana'ar tasu. Ku saurara hirarsu da Naziru Mikai'il.

View Details

APC a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Nigeria, na zargin jam'iyyar PDP da yi wa magoya bayan jam'iyyarta bita-da-kullin siyasa. Ku saurari karin bayanin da Alhaji Hassan Jika Ardo, shugaban jam'iyyar APC a jihar Taraba ya yi wa Yusuf Tijjani.

View Details

A ranar Litinin ne kwamitin da gwamnatin kasar ta kafa karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasar Muhammad Namadi Sambo ya mika rahoton sa ga kwamitin shugaba mai jiran gado na Muhammadu Buhari. Ku saurari hirar Raliyah Zubairu da Ambasada Bashir Yuguda, Ministan ma'aikatar kudi ta Nigeria kuma mamba a kwamitin mika mulki na gwamnati mai barin gado

View Details

Ministan kudin kasar Nepal, Ram Sharan Mahat ya kare matakan da gwamnatin kasar ta dauka wajen kyautata rayuwar al`ummar da masifar ta ritsa da su, bayan wata guda da aukuwar mummunar girgizar kasa a kasar. Ku saurari rahoton da Badariyya Tijjani Kalarawi ta hada mana.

View Details

'Yan sanda a kasar Malaysia sun ce sun samu kimanin kaburbura 140 a wani daji mai iyaka da kasar Thailand. Ku saurari fassarar rahoton Jonathan Head daga Bangkok.

View Details

Masu ruwa da tsaki a harkar man fetur a Najeriya sun cimma wata yarjejeniya domin kawo karshen matsalar mai da ake fama da ita a kasar. Alhaji Danladi Fasali shi ne sakataren kungiyar dillan man fetur na Najeriya kuma ya yi wa Nasidi Adamu Yahya karin bayani bayan fitowarsu daga taron. Ku saurara a nan.

View Details

Cristiano Ronaldo ya ci wa Real Madrid kwallaye 61 a kakar wasan bana, yayin da ya ci uku a lokacin da suka doke Getafe 7-3 a La Liga ranar Asabar. Ga Mamman Skipper da sauran labaran.

View Details

Yusuf Tijjani ya tattauna da Dr Nazifi Darma wani masanin tattalin arziki a Abuja Nigeria a kan irin manyan kalubalen tattalin arziki da sabuwar gwamnatin Muhammadu Buhari za ta fuskanta da zarar ta karbi iko. Ku saurara a nan.

View Details

A wata sanarwa da ta fitar, jam'iyyar APC ta zargi gwamnatin PDP mai barin gado da yi wa shugaban kasa mai jiran-gado Muhammadu Buhari zagon-kasa. Ku saurari rahoton da wakilinmu Haruna Shehu Marabar Jos, ya hado mana.

View Details

A Najeriya, rahotanni daga wasu jihohi na cewa jama'a na ci gaba da fuskantar matsalar karancin ruwan sha, Ku saurari rahoton da wakilinmu Is'haq Khalid ya aiko mana.

View Details

Ana ci gaba da samun karin bayanai dangane da inda ake ajjiye da wasu mata da kananan yaran nan da sojin Najeriya ta ceto daga dajin Sambisa ranar Talata daga sansanin 'yan gudun hijira na Malkohi dake Adamawa. Haruna Shehu Marabar Jos ya aiko mana da karin bayani.

View Details

A Najeriya cece-kuce game da batun wanda zai zama kakakin majalisar dokokin kasar na cigaba da jan hankalin yan siyasa. Ku saurari hirar Hon Kawu Sumaila dan majalisar wakilai na Kano, da Abdullahi Tanko Bala.

View Details

Shugaban kasar mai jiran gado Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin Jonathan mai barin gado, ba ta bai wa kwamitin da ya kafa, cikakkun bayanai ba game da halin da gwamnatin tarayya ke ciki. Ku saurari rahoton da Raliya Zubairu ta hado mana.

View Details

Rundunar 'yan sanda a Jihar Kebbi na bincike kan yadda wasu gungun mutane a garin Argungu suka kona wata dattijuwa har lahira bisa zarginta da maita. Ku saurari hirara Abdullahi Tanko Bala da kwamishinan yan sanda na Jihar Kebbi, Mr Danladi Mshelbwala.

View Details

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta ce sojojin kasar sun kwashe mata da yara kusan 300 daga sansanin 'yan gudun hijira da ke jihar Adamawa. Ku saurari a rahoton da Yakubu Liman ya aiko mana.

View Details

Wasu kungiyoyin farar hula a jamhuriyar Nijar sun yi watsi da zargin da ministan cikin gida na kasar ya yi wa fitaccen dan kare hakkin dan adam din nan Malam Musa Cangari. Ku saurari rahoton da wakilinmu Baro Arzika ya aiko mana.

View Details

Kalaman da aka yi su a wajen wani Maulidin Shehu Ibrahim Inyass, sun tada hankulan jama'a da dama. Daya daga cikin manyan shehunnan Darikar Tijjaniyya Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya shaidawa wakilin mu Yusuf Ibrahim Yakasai cewa babu ruwan su da duk mai irin wadannan kalaman. Ku saurara a nan.

View Details

A yayin da ya rage 'yan kwanaki a rantsar da sabuwar gwamnati a Najeriya, wata kungiyar Kiristocin arewacin kasar na shirin fara wani azumi da gudanar da adduoi na musamman. Ga rahoton wakilin mu Nurah Mohammed Ringim.

View Details

Jam'iyyar PDP ta yi karin haske dangane da dalilan da suka sa shugaban ta na kasa Alhaji Ahmadu Adamu Mu'azu tare da shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar Chief Tony Anenih yin murabus daga mukamansu. Ku saurari hirar Yusuf Tijjani da Sanata Walid Jibrin wanda shi ne sakataren kwamitin amintattu na jam'iyyar, kuma a yanzu shi ne mukaddashin shugaban kwamitin amintattun.

View Details

Shugabannin kasashen Kungiyar bunkasa tattalin arzikin Afirka ta yamma, wato ECOWAS ko CEDAO sun yi fatali da wani kudiri da ya bukaci a kayyade adadin wa`adin mulki ga shugaban kasa. Ga fassarar rahoton Mary Harper.

View Details

A Najeriya, Ma'aikatan kamfanin man fetur na kasar wato NNPC sun shiga wani yajin aiki domin matsin-lamba ga Ministar mai ta kasar, Diezani Alison Madueke ta janye mika wasu rijiyoyin mai guda biyu ga wasu kamfanonin 'yan kasuwa. Ku saurari rahoton da Habiba Adamu ta hada mana.

View Details

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Alhaji Ahmed Adamu Mu'azu ya murabus a matsayin shugaban jam'iyyar nan take. Ku saurari karin bayanin da mataimakin kakakin jam'iyyar PDP na kasa, Barrister Abdullahi Jalo ya yi wa abokin aikimu Aliyu Abdullahi Tanko.

View Details

A jihar Kaduna, kwamitin karbar mulki da zababben gwamnan jihar mai jiran gado Malam Nasiru El Rufai ya kafa, ya kai karar gwamnatin jahar mai barin gado gaban hukumar yaki da cin hanci da karbar rashawa wato EFCC. Ku saurari rahoton wakilin mu Nurah Mohd Ringim.

View Details

Wani dan kasar Birtaniya da ake ganin dan kungiyar dake da'awar kafa kasar musulunci ta IS ya wallafa wani littafi dake bayyana ka'idojin zama a cikin kungiyar. Ku saurari fasarar rahoton wakilin BBC, Sebestian Usher.

View Details

Matasan karamar hukumar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi sun kwato muggan makamai da dama daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram inda kuma suka mika wa hukumomin tsaro. Ku saurari rahoton da wakilinmu Is'haq Khalid ya aiko mana.

View Details

Dubban Farar-hula na tserewa daga birnin Ramadi, birnin da mayakan IS ke ci gaba da bararrajewa bayan sun kwace iko da shi. Ku saurari rahoton Badariyya Tijjani Kalarawi.

View Details

Wani rahoton da wata Kungiyar kare hakkin Biladama da ke Masar ta fitar ya zargin cewa cin zarafin da ake yi na biladama ya kara muni , bayan da sojoji suka karbi mulkin kasar. Ga hirar Ibrahim Isa da Mallam Nasiru El Rufa`i Sokoto, dan jarida a kasar Masar a kan wannan batu.

View Details

Hukumar Lafiya ta duniya, WHO, ta ce za ta kafa wani Asusun ko-ta-kwana na dala miliyan dari don yaki da cutar Ebola. Babbar Daraktar Hukumar Margaret Chan, ta bayyana cewa annobar Ebola ta ci karfin Hukumar lokacin da ta barke a shiyyar Afirka ta yamma, kasancewar abin da aka bukata wajen yaki da ita ya ninka sauran bukatu da hukumar ta saba dawainiyarsu sau goma. Dr Nasiru Sani Gwarzo Mamba ne a kwamitin ayyukan gaggawa na yaki da cutar Ebola a Najeriya, ga hirarsu da Ibrahim Isa a kan wannan yunkuri na WHO.

View Details

Hukumomi a jihar Kano da ke arewacin Nigeria sun ce an samu raguwar masu ta'ammali da miyagun kwayoyi a jihar idan aka kwatanta da baya. Jihar dai ta jima a matsayin na daya cikin wadan da aka fi sani da shan miyagun kwayoyi a kasar. Yanzu alkaluman hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyin kasar sun nuna cewa ba Kanon ce kan gaba ba a yanzu. Ku saurari rahoton da waklinmu Yusuf Ibrahim Yakasai ya aiko mana.

View Details

A kasar Ghana, ana kukan targade sai ga karaya, yayin da talakawan kasar ke fama da karancin wutar lantariki, gwamnati ta kara farashin albarkatun man petur da kashi 9 (tara) bisa dari. Iddi Ali ya tattaro mana ra'ayoyin wasu 'yan kasar dangane da wannan batu. Ku saurara a nan.

View Details

Mazauna yankin karamar hukumar Faskari a jihar Katsina sun ce mutum shida ne aka halaka a wani hari da wasu masu satar shanu suka kai kan wasu kauyuka da yammacin jiya. Ku saurari karin bayanin da wakilin mu Yusuf Ibrahim Yakasai ya aiko mana.

View Details

Wani jerin motocin mayakan sojin sa kai na 'Yan Shi'a da gwamnatin Iraki ta tura ya isa wani sansanin a kusa da birnin Ramadi wanda ya fada hannun yan gwagwarmayar kasar Musulunci watau IS. Ahmad Abba Abdullahi ya tattauna da Malam Muhamad Kaddam Sidiq Isa, mai sharhi kan harkokin Gabas ta tsakiya dake Dubai. Ku saurari hirarsu a nan.

View Details

A Najeriya, yayin da ake ganin yankin arewa maso gabashin kasar ne yankin da ya fi kowane yanki galabaita a kasar, saboda matsalar rikicin Boko Haram da kuma koma bayan rayuwa, jama'ar yankin ciki har da 'yan siyasa na ci gaba da fafutikar ganin sabuwar gwamnati da za a rantsar a kasar a karshen wannan wata, ta mai da hankali sosai da sosai ga yankin. Ku saurari rahoton da wakilinmu, Is'haq Khalid, ya aiko mana daga Bauchi.

View Details

Sakataren kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP Sanata Walid Jibrin, ya ce jagororin jam'iyyar ne da kansu suka yi sanadiyyar kayen da ta sha a zabukan Najeriya da suka gabata. Ku saurari hirarsu da Yusuf Tijjani.

View Details

'Yan kasuwa manya da kanana dai sun dade suna kokawa game da haraji barkatai da akan aza masu karfi da yaji a matakan kananan hukumomi da jihohi da ma tarayya. Matsalar harajin da illolinta sun addabi harkokin kasuwanci a sassa daban-daban na Najeriya. Gwamnatin kasa mai barin gado ta tsara wasu matakai da ka'idoji don shawo kan matsalar.